‘Yadda barayin mutane suka hallaka mahaifinmu da abokinsa bayan karbar kudin fansa’

A yammacin ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna suka shiga cikin damuwa da tashin hankali sakamakon kashe wani dan unguwar mai suna Kabiru Abdullahi da abokinsa Alhaji Sanusi Iro Dabai da masu garkuwa da mutane suka yi bayan kuma sun karbi kudin fansa. […]

‘Yadda barayin mutane suka hallaka mahaifinmu da abokinsa bayan karbar kudin fansa’

‘Yadda barayin mutane suka hallaka mahaifinmu da abokinsa bayan karbar kudin fansa’

A yammacin ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna suka shiga cikin damuwa da tashin hankali sakamakon kashe wani dan unguwar mai suna Kabiru Abdullahi da abokinsa Alhaji Sanusi Iro Dabai da masu garkuwa da mutane suka yi bayan kuma sun karbi kudin fansa.

Masu garkuwa da mutanen sun karbi Naira miliyan biyu da dubu 100, sannan suka kashe mutanen biyu wadanda abokai ne.  Aminiya ta gano cewa masu garkuwan sun sace su ne lokacin da suke gona a kusa da garin Kangimi da ke hanyar zuwa Jos a Karamar Hukumar Igabi.

Bayanai sun ce an sace mutanen biyu ne kusan kwana 12 da suka wuce kafin a hallaka su.

Mohammed Dikko, wanda da ne ga marigayi Alhaji Kabiru  domin a hannunsa ya girma ya shaida wa wakilinmu da ya ziyarci gidansu da ke Hayin Banki cewa an gano gawar mahaifinsu da na abokinsa ne a cikin daji a ranar Litinin da gabata.

Ya ce lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kira waya sun bukaci a ba su Naira miliyan biyar a kan kowanensu. “Sai muka fada musu cewa babu wannan kudi, daga nan dai muka ci gaba da ciniki har aka amince za a ba su Naira miliyan biyu suka ce a kawo, amma suka nemi sai mun kara musu da katin waya na Naira dubu 100.

Muka ce za a bayar daga nan muka nemi wani mutum da zai kai musu kudin domin kowa na tsoron zuwa. Shi wanda aka amince zai kai kudin muka sasanta da shi a kan za a ba shi Naira dubu hamsin. Bayan an ba shi kudin ya tafi da babur dinsa sai suka karbi kudi suka kirga suka ce sun cika amma sai suka kira waya cewa wannan kudi sun karba amma na cin abinci aka ba su, sai an karo Naira miliyan biyar muka ce gaskiya babu wannan kudi,” inji shi.

Ya ce “Sai suka ce to ga su mu yi ban-kwana da su. Tun daga wannan rana ba su sake kiran waya ba, da muka ji shiru kwana biyu sai muka nemi taimakon ’yan banga da ’yan sanda aka shiga dajin nemansu. Su ’yan banga ne ma suka gano gawarwakin nasu. Bayan an dauko su sai aka kai su Asibitin Barau Dikko aka wanke su daga nan muka dauko namu gida su ma iyalan Sanusi Dabai suka dauki nasu zuwa gida domin yi musu jana’iza.”

Dikko ya ce ’yan sandan da suka shiga dajin a karkashin shugabansu wani Hassan Gimba sun yi nasarar kama mutum12 da suke zargin suna ne masu garkuwa da mutanen domin a tsakiyar dajin aka kama su a lokacin da aka shiga.

Game da shekarun mahaifinsu ya ce, “Baba zai kai kusan shekara 61 ko 62 kuma yana da iyali. Kuma aboki ne ga Sanusi Dabai da aka sace su tare. Muna kuma ganin duk yadda aka yi akwai sanayya wanda shi ya sa mutanen suka kashe su,”inji shi.

Ya bayyana cewa hatta wanda suka tura ya kai kudin sai da suka buge shi sannan suka kwace masa babur. Ya ce mutanen na rike da bindigogi lokacin da suka fito karbar kudin.

Kokarin jin ta bakin iyalan daya marigayi Sanusi Dabai ya ci tura domin lambar wayar da aka bayar na dan uwansa ba a dauka ba sai dai daya daga cikin kannensa wanda bai ambaci sunansa ba ya nuna abin da ya faru da dan uwansu a matsayin mukaddari daga Allah.

Ya ce dama ta wannan hanya Allah Ya yi zai rasu, don haka sun mika lamarinsu ga Allah domin shi ke bada rai Ya kuma karba a duk lokacin da ya ga dama. Sannan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa dan uwan nasu da Aljannar Firdausi.

Kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna,  DSP Yakubu Sabo ya ci tura domin bai amsa waya ba.