Yadda basarake ya harbi ‘yar aiki saboda kukan ’yarsa

A kwanakin baya ne mazauna Unguwar Barnawa suka wayi gari cikin alhini sakamakon labari da ya yadu cewa wani basarake da ake kira Jamilu Barden Kano ya harbi mai yi masa aiki da bindiga saboda ’yarsa tana kuka ba ta zo ta kula da ita a kan lokaci ba. Matar wacce aka harba mai shekara […]

Yadda basarake ya harbi ‘yar aiki saboda kukan ’yarsa
Yadda basarake ya harbi ‘yar aiki saboda kukan ’yarsa

A kwanakin baya ne mazauna Unguwar Barnawa suka wayi gari cikin alhini sakamakon labari da ya yadu cewa wani basarake da ake kira Jamilu Barden Kano ya harbi mai yi masa aiki da bindiga saboda ’yarsa tana kuka ba ta zo ta kula da ita a kan lokaci ba.
Matar wacce aka harba mai shekara 30 mai suna Ummukulsum ita ce ke yin girke-girke a gidan wanda ake zargin.
Aminiya ta samu labarin cewa Jamilu wanda aka ce dan marigayi Sarkin Tofa ne, ya harbi Malama Ummukulsum ce da misalin karfe 1:00 a ran 25 ga watan Yunin da ya gabata.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa Jamilu ya harbi Ummukulsum ne a lokacin da take  rainon ’yar tasa bayan uwargidansa ta fita unguwa ta bar ta tana barci a cikin dakinta. “Eh, to kamar yadda labari ya zo mana ita matar maigidan ta fito makwabta ne ta bar yarinyarta a cikin irin gadon jariran nan tana barci. Koda yarinyar ta farka daga barci sai ta soma kuka. Ita kuma Ummukulsum tana daya daga cikin masu aikin gidan. Shi kuma mijin sai aka ce ya nemi matarsa ta waya kan me ya sa yarinyar take kuka. Ita kuma sai ta kira masu yi mata aiki kan su shiga su duba mata yarinyar. Ummukulsum da abokiyar aikinta sai suka shiga cikin dakin inda yarinyar ke kwance domin lallashinta. Bayan ta dan daina kuka sai daya mai aikin ta fita daga dakin ta koma cikin gida. Shi kuma maigidan sai ya sauko a fusace daga saman bene rike da bindiga ba tare da bata lokaci ba sai ya yi harbi inda harsashin ya gogi wuyar Ummuklusum da koma gefen nononta nan take ta fadi kasa,” inji Kwamrade Bala Muhammad wanda shi ne ke taimaka mata wajen neman hakkinta. Bayan Malama Ummukulsum ta fadi kasa sai Barden na Kano ya yi maza ya dauke ta zuwa asibitin Fada da ke Kakuri ba tare da iyayenta sun sani ba har tsawon kwana biyu.
A halin da ake ciki,  Malama Ummukulsum, tana  jinya ne a gidansu da ke Layin Shagari a karshen Kwalta a Hayin Rigasa bayan an sallame ta daga asibiti a ranar Litinin din makon jiya.
Aminiya ta ziyarce ta a gida domin jin yadda abin ya faru amma ba ta iya magana sosai kuma ’yan uwanta sun nuna cewa likitanta ya nuna a daina damunta da surutu saboda yanayin jikinta.
Sai dai ’yan uwan sun nuna cewa kuskure ta da harsashin ya yi ne ya sa ta rayuwa da sai dai wata ba a ita ba. ’Yan uwan sun ce Barden Kanon Jamilu ya amince shi ya yi harbin, inda ya nuna cewa harsashi ya fita ne cikin kuskure, kuma ya amince zai ci gaba da kulawa da ita tare da ’ya’yanta har zuwa lokacin da za ta warke.
Wata majiya ta ce ’yan sanda sun kama wanda ake zargin daga bisani aka ba da belinsa. “Gaskiya da-na-sanin da ya yi tare da alkawarin kulawa da ita da dawainiyar ’ya’yanta da ya dauka ne suka sa ya samu sassauci. A yanzu haka kusan a kullum sai ya kashe mata kudin magunguna kusan Naira dubu 27. Wannan ya sa ’yan uwan Umukulsum suka gamsu da matakin da ya dauka,” inji Saudatu Mohammad Inuwa, yayar wacce aka harba shakikiya. “Shi yake daukar dawainiyarta a yanzu kuma dama shi ya ja abin ya yi tsawo, amma tunda ya yi nadamar abin da ya aikata mun gamsu, muna kuma fatan Allah Ya ba ta lafiya,” inji ta.
kokarin jin ta bakin wanda ake zargin ya ci tura domin an ce ba ya gari yana zuwa ne daga Kano.