Yadda batun canjin kudi ya kada hantar ’yan Najeriya
Batun ya kada hantar ’yan Najeriya, musamman wadanda suka san abin da ya faru a lokacin canjin kudi da gwamnatin mulkin soja ta Janar Muhammadu Buhari ta yi a 1984.
Ga dukkan alamu, hantar ’yan Najeriya ta kada saboda shirin sauya takardun kudade, musamman wadanda suka san abin da ya faru a lokacin canjin kudi da gwamnatin mulkin soja ta Janar Muhammadu Buhari ta yi a 1984.
A makon jiya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana kudirinsa na sauya fasalin wasu takardun kudi da suka hada da Naira 200 da 500 da 1,000.
- Canjin Naira: EFCC ta dana wa gwamnoni tarko —Bawa
- Kotu ta ba da umarnin kwace kadarorin Sanata Ekweremadu
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka, inda ya ce Babban Bankin ya samu sahalewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, don fara amfani da sababbin takardun kudin a ranar 15 ga Disamban bana, inda ya ce matakin zai taimaka wajen kara daga darajar Naira.
Dakaddamar canjin takardun kudi
Wannan sanarwa ga dukkan alamu ta kada hantar ’yan Najeriya da dama, musamman wadanda suka san abin da ya faru a 1984.
A wancan lokaci mutane da dama sun tafka asara sakamakon shiga hannun dillalan zaune da suka rika cutarsu a lokacin canjin da kuma yadda karancin lokaci da bankuna suka sa mutane asarar miliyoyin Naira.
Bayan sanarwar dai Ministar Kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta nesanta ma’aikatarta da shirin lokacin da take amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa.
Ta ce, “Bankin CBN bai tuntube mu ba a Ma’aikatar Kudi ba kafin yanke shawarar sauya wasu takardun kudin.
“Kuma a matsayina na babbar jami’a a harkar tsare-tsaren kudi a Najeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa na da matukar hadari ga darajar Naira.”
Amma a ranar Litinin da ta gabata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da amincewarsa za a sauya takardun kudin, inda ya ce ’yan Najeriya za su ga amfaninsa.
Shugaba Buhari ya ce ya gamsu da bayanan da Gwamnan Babban Bankin ya gabatar masa cewa hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan, wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da rage yawan kudaden da suke hannun mutane.
“Mutanen da suke da kudaden haramun da suke boye a karkashin kasa ne za su fuskanci matsala, amma ma’aikata da ’yan kasuwa da suke da kudaden halalinsu ba za su samu wata matsala ba,” kamar yadda Shugaban Kasar ya bayyana a wani tsakuren tattaunawa da fitaccen dan jaridar nan Alhaji Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai na Gidan Talabijin din Tambari suka yi da shi.
Kada a maimaita abin da ya faru a 1984 – Talakawa
Wasu ’yan kasuwa talakawa da Aminiya ta tattauna da su, sun nuna tsoro da rashin jin dadinsu ne kan lamarin.
Sabi’u Ali ya ce ba su goyon bayan shirin lura da cewa wanda aka yi a baya ya janyo wa mutane fadawa cikin talauci.
Ya ce, “A lokacin mulkin Buhari na soja haka ya canza kudi lamarin da ya janyo wa mutane da dama suka shiga kangin talauci.
“Gaskiya ba mu so a sake maimaitawa; Ga shi har yanzu wasu ba su farfado ba.”
Malam Hassan Ado, da ke Kasuwar Abubakar Rimi ya ce bai dace gwamanti ta fitar da wannan magana a wannan lokaci na matsin tattalin arziki ba.
“Ya ce canjin kudin zai iya zame wa mutane wahala lura da cewa mutane dama na tsoron daukar kudade masu yawa zuwa wani wuri saboda barayi.”
Hantar ’yan Najeriya ta kada
Wata ’yar kasuwa Hassana Ado ta ce ba su yi farin ciki da jin labarin ba, saboda lamarin zai iya zama nakasu ga harkokin kasuwancinsu.
Wani dan kasuwa Ibarahim Saleh ya ce suna fata gwamnati za ta kara wa’adin da ta sa na ranar 31 ga Janairun badi don daina amfani da tsofafffin takardun kudin, inda ya nemi a kara tsawon wa’adin domin mutane su samu canjawa kada su yi asara.
Wani dan kasuwa shawartar gwamanti ya yi cewa ta yi amfani da kudin da za ta kashe wajen canjin kudi ga ayyukan da za su amfani al’umma.
Abbakar Hassan Gusau kuwa cewa ya yi canjin karya darajar kudin kawai zai yi, amma zai tona asirin wadanda suka saci kudi suka ajiye don rabawa a lokacin zabe.
“Su ma ’yan fashin daji da suka karbi kudin fansa suka ajiye sun fada wannan rukuni.
“Don haka in dai a kan wannan ne muna goyon bayan. Allah Ya sa hakan shi ne alheri”, in ji Abbakar.
Ansar Abdulwasi’u Andarai ya ce, “Duk masu sukar sauyawar na gudun a san abin da suka boye ne, shi ya sa suke haka.”
Wani matashi, Sulaiman Kabir ya ce ba komai ya sa aka kirkiro sauya kudin ba, sai don a cire rubutun ajamin da ke jiki.
Momcyn Anas Ma’een kuwa, cewa ta yi kamata ya yi gwamnati ta mai da hankali wajen sauko da farshin man fetur da gas da kananzir, kafin ta kama zancen sauya takardun kudin.
Wani dattijo mai suna Abubakar Sadik ya ce ko sauyin bai shafi kowa ba a Najeriya, to shi ya shafe shi, domin kuwa asusu ne da shi da yake tara kudin da zai aurar da jikarsa da mahaifiyarta ta rasu.
“Idan aka sauya kudin nan, sai fa an sa na fasa asusu, na je bin layin karbar sababbi.
“Kuma kowa zai je canjin don haka idan ba tsari wahala kawai za ka je ka sha a banki.
“Kuma kin ga a watan Disamba za a yi bikin, don haka gaskiya ba na farin ciki da wannan canjin, in dai ba a kara lokaci ba”, in ji shi.
Wata mai sayar da abinci mai suna Hajiya Amina da aka fi sani da Bola, ta ce, “An tsara yadda mutane za su je sauya kudin?
“Ko kawai kowa zai tashi ya shiga banki ne da kudinsa ya canja?
“Sannan wa’adin da aka bayar a sauya kudin ya yi kadan, idan ba ka samu sauyawa ba a tsakani saboda cinkoson mutane a banki, yaya za a yi?
“Kin ga wannan ai kawai ta da zaune-tsaye ne gwamnati ke son yi wa mutane ba gaira ba dalili,” in ji ta.
Shirin zai farfado da tattalin arziki —Masana
Sai dai masana tatatlin arziki sun nuna cewa shirin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasa.
Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata malami a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ya ce dukkan dalilan da Babban Bankin ya bayar a kokarinsa na canjin kudin dalilai ne karafafa wadanda ya kamata a yi la’akari da su.
“Idan aka yi la’akari da dalilan da Babban Bankin ya kawo na canjin kudin abu ne da ya kamata a ce an dade da yin sa.
“Mutane da yawa sun boye kudade a wurinsu, kusan a yanzu kashi 85 na kudin Najeriya ba sa cikin bankuna.
“Kudaden suna ajiye sun daina shiga bankuna. Lamarin da ya saba da wasu tsare-tsare na Babban Bankin Kasa,” in ji shi.
Haka ya ce kudaden sun tsufa wanda idan kudi suka tsufa ba su da kima kuma hakkinsu ne su ga an sabunta.
Kuma ya ce saboda dadewar da kudaden, masu buga kudin jabu suna ci gaba da buga irinsu.
Dokta Kofar Mata ya ce suna fata idan aka sake kudin ba za a sake maimaita abin da ya faru a baya ba, inda mutane suka rika daukar kudinsu suna kwana a kan layi a bankuna don neman canjin kudin.
Ya ce, “Idan har gwamnati ba ta so a maimaita abin da ya faru a baya inda mutane suka rika kwana a layin bankuna, to ya kamata ta samar da kyakkyawan yanayi da wadatatun kudi a bankuna ta yadda za a gudanar da aikin cikin nasara.”
Darajar Naira na ci gaba da faduwa
Tuni dai darajar Naira take ci gaba da faduwa yayin da farashin Dala a kasuwar bayan fage ya kai Naira 822 a ranar Juma’a.
Binciken Aminiya ya gano cewa faduwar darajar Nairar ba ta rasa nasaba da sanarwar da CBN ya fitar na sauya fasalin kudin.
Ba da wannan sanarwa ke da wuya, sai darajar Naira ta soma faduwa daga yadda ake canja Dala daya kan Naira 765 zuwa Naira 818 a ranar Litinin, kuma ga alama faduwar ba za ta tsaya a nan ba.
Da Aminiya ta ziyarci Kasuwar ’Yan Canji da ke yankin Zone 4 na Abuja, ta gane wa idonta yadda ake gogoriyon neman Dala.
Wakilin Aminiya ya nemi sayen Dala 10,000, amma bai samu ba.
Wani dan canji mai suna Isma’ila Yusuf ya ce Dala na matukar wahala, kuma ba da dadewa ba jami’an Hukumar EFCC suka zo kamen wadanda suka zo sayen Dala mai yawa.
Ya ce, ’yan canjin na taka-tsantsan wajen sayar da Dala mai yawa ga mutane a yanzu.
A wani bincike da Aminiya ta yi a kasuwar canji ta bayan fage a Legas a farkon makon nan, ta gano ana sayen Dala daya a kan Naira 790 zuwa Naira 800, sannan a sayar da ita a tsakanin Naira 795 zuwa Naira 805.
EFCC na hakon masu canjar daloli don boyewa
Aminiya ta samu labarin cewa a ranar Talata da gabata jami’an Hukumar EFCC sun kai samame a wajen da ake zargi ana hada-hadar Dala ta bayan fage domin dakile hauhawar farashinta.
Aminiya ta gano cewa Dalar tana hauhawa ce saboda mutane da dama sun ki zuwa banki don ajiye kudadensu, inda suke da kokarin canja su zuwa Dala don ajiyewa.
Haka binciken Aminiya ya gano wasu masu kudin suna kiran masu canjin ne har gida, inda suke canja musu kudadensu ba tare da an gan su ba.
Hada-hadar bayan fage ta sa farashin Dalar ta yi sama, wanda hakan ya sa jami’an EFCC suka kai samame tare da kama wasu da ake zargin da harkallar.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Yulin bara, Bankin CBN ya hana sayar wa kamfanonin canji kudaden waje a duk fadin kasar nan.
Da yake bayani kan dalilin faduwar darajar Naira, masanin tattalin arziki, Dokta Muda Yusuf ya ce hakan bai rasa nasaba da yadda masu makudan kudade a gida suke ta gogoriyon sauya su zuwa daloli domin ci gaba da ajiye su a gida.
“Wasu na da makudan kudade a gida da ba za su so zuwa banki ba domin EFCC na bibiyar lamarin,” in ji shi.
Daga: Isiyaku Muhammed da s I. Garba, da Rahima Shehu Dokaji, Kano