Yadda batun sulhu kan makomar siyasar Bauchi ya ja hankalin al’umma
Tun bayan zaben 2015 ne aka fara samun takaddama tsakanin jiga-jigan APC a Jihar Bauchi musamman ‘Yan Majalisar Wakilai ta Tarayya da wadansu kusoshin jamiyyar da kuma Gwamnatin Jihar Bauchi, bisa zargin da ‘yan majalisar ke yi cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ta gaza tabuka abin a gani a jihar, zargin […]

Tun bayan zaben 2015 ne aka fara samun takaddama tsakanin jiga-jigan APC a Jihar Bauchi musamman ‘Yan Majalisar Wakilai ta Tarayya da wadansu kusoshin jamiyyar da kuma Gwamnatin Jihar Bauchi, bisa zargin da ‘yan majalisar ke yi cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ta gaza tabuka abin a gani a jihar, zargin da Gwamnan ya sha karyatawa, kuma tun lokacin ake ta takun saka a tsakaninsu.
To amma sai dai zuwan da gwamnan ya yi wajen bikin murnar cikar shekaru 50 na Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara a Abuja ya sanya wadansu ganin kamar an yi sulhu, lamari da ya janyo zantuka daban-daban a farfajiyar siyasar jihar, inda shugaban majalisar ya fito ya fayyace matsayinsa.
Tun da farko bayan da Gwamna Muhammadu Abubakar ya halarci wajen bikin na Dogara, dan majalisar dake wakiltar mazabar Misau da Dambam a majalisar wakilai ta tarayya Ahmed Yerima ya bayyana cewa zuwan da gwamna ya yi ba na sulhu ba ne, don da ace sun yi sulhu da Yakubu Dogara da ya sani, domin Dogara zai fada masa, sai ya ce wanene a cikinsu ko Dogara zai je mazabarsa ya ce jama’a ku sake zaban Gwamna Abubakar saboda ya muku aiki kaza da kaza a mazabarsa, ya kawo muku alheri kaza da kaza? Ya ce da wuya ka samu wanda zai iya yin hakan, tun da ba mazabar da ta samu wani aiki daga gwamnatin jihar.
Koda magoya bayan Jamiyyar APC da kuma ita kanta uwar jam’iyyar APC sun halarci bikin da aka yi a Bogoro don murnan cikar shuagaban majalisar shekaru 50. Koda yake wasu na ganin cewa ’yan siyasa da shugabannin addini ne suka tado da batun sulhun a wajen liyafar, kafin dan majalisar mazabar Lere da Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa, Hon. Aminu Tukur ya ce kada Dogara ya amince da a sa shi a daki a yi sulhu ba su sani ba, don ba za su amince da haka ba.
Hon. Tukur ya ce tun lokacin marigayi Ajiyan Bauchi, Alhaji Adamu Tafawa Balewa kullum yana shugabantar su ne su na ba shi shawara, su na fada masa gaskiya, kuma yana dauka saboda haka yake shawartar Dogara da cewa kada wadansu su ce sun yi sulhu da shi alhali su magoya bayansa ba su sani ba. A jawabinsa, Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar wanda mataimakinsa Injiniya Nuhu Gidado ya wakilta, ya bayyana cewa wakilcin shugaban majalisar wakilci ne da ya daga darajar jihar Bauchi a matakin Tarayya, ya kuma gode masa saboda kyakykyawan jagoranci da yake yi.
Gidado ya ce “kafin na karbi abin magana sai da na tambayi Dogara cewa in yi magana ne a matsayina na wakilin Gwamna ko a matsayina na Nuhu Gidado, shi kuma da ya ke mutum ne mai karamci ya ce in yi abin da nake so ba komai.”
A jawabin Shugaban Majalisar Wakilan, Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa ba zai sa igiya a wuyan kowa yasa shi ya yi abin da baya kauna ba, illa iyaka zai yi abin da mafi yawan al’ummar jihar Bauchi suke so ne, kafin a yanke wata shawara kan makomar siyasar jihar kafin zaben 2019.
Dogara ya ce “dangane da batun sulhu a jihar duk abin da mafi yawan jama’armu suka yarda da shi ni ma shi ne zabina, inda mafi yawan jama’a suke, a nan za a same ni cikin ikon Allah” sai ya kawar da tsoron da al’umma suke ji kamar yadda dan majalisa mai wakiltar Lere da Bula a majalisar Dokoki na jihar, Hon. Aminu Tukur ya nuna kan cewa akwai jita-jitar da ake yadawa cewa sun yi sulhu kan harkokin siyasa a jihar, Dogara ya ce ba zai ci amanar jama’a ba, inda mafi yawan jama’a suke shi ma anan yake”
Dogara ya kuma baiwa magoya bayansa tabbacin cewa kafin a yanke wata shawara ko a dauki wani matsayi sai an tuntubi kowa da kowa kuma kowa ya fayyace ra’ayinsa, abin da mafi yawan jama’a suka fi so shi zamu yi in ji shi.
“A matsayinmu na shugabanni tilas ne mu yi amfani da abin da mafi yawan jama’armu suke so ba abin da mu muke so ba, zamu zauna akan teburi a matsayinmu na yan’uwa maza da mata mu tattauna koda zamu daidaita mu kasa cimma daidaito, to mu daidaita mu kasa cimma daidaiton. Wannan shi ne matakin da zamu dauka.