Yadda Benzema yake kwatar Real Madrid a bana

Ba don Benzema ba da an cire Real Madrid a Gasar Zakarun Turai, kuma ba a tunanin za a lashe La Liga

Yadda Benzema yake kwatar Real Madrid a bana

Benzema

A wasa na farko na wasanni dab da na Kwata Fainal na Gasar Zakarun Turai, Real Madrid ta doke Chelsea da ci uku da daya.

Da aka dawo wasa na biyu, sai Chelsea ta yi Madrid din shigar wuri, cikin dan lokaci ta jefa magoya bayan kungiyar cikin fargaba da tsoro.

Ana cikin hakan ne Karim Benzema ya yi ta maza ya jefa kwallo a minti 96, wanda hakan ya yi waje da Chelsea, ita kuma Madrid ta tsallaka zuwa wasan dab da na karshe.

Haka a wasan Gasar Laliga na makon nan, Sevilla ta fara zura kwallo biyu a ragar Madrid a cikin minti 25 na farko.

Daga baya Madrid ta farke kwallayen, sannan minti 92 Benzema ya zura kwallo na uku, wanda hakan ya sa Madrid ta doke Sevilla da ci uku da biyu.

Shin Benzema ke dauke da Madrid a bana?

Dan wasan na Faransa mai shekara 34, a yanzu za a iya cewa kakar bana ce kakar da ya fi tashe tun zuwansa kungiyar Real Madrid a kakar 2009/2010.

Zuwa yanzu ya zura kwallo 39 a kakar bana, wanda shi ne addadi mafi yawa na kwallaye da ya ci a kakar wasanni daya a tarihinsa.

Saboda hazakarsa, yanzu Real Madrid ce ke saman teburi da tazarar maki 12, ta lashe Kofin Spanish Super Cup, sannan yanzu haka ta kai matakin daf da na karshe a Gasar Zakarun Turai.

A Gasar Laliga, Benzema ya zura kallo 25, inda yake kan gaba wajen zura kwallaye da tazarar kwallo.

Kafin kakar bana, bai taba zura sama da kwallo 24 a gasar ta Laliga a kakar wasanni daya ba.

El-Classico na karshe

A ranar 20 ga watan Maris ce aka fafata wasan El-Classico na karshe na Gasar Laliga ta bana, inda Barcelona ta ragargaji Real Madrid ta ci hudu da nema.

Sai dai kusan duk magoya bayan Real Madrid da na Barcelona din sun yi amanna cewa rashin Benzema ya taimaka wajen ba Barcelona nasara a wasan.

Tun kafin wasan aka samu labarin Benzema ya ji rauni ba zai samu damar buga wasan ba saboda jinya.

Wannan labarin ya sanya magoya bayan Barcelona murna, su kuma magoya bayan Real Madrid suka shiga zullumi, wanda hakan ya nuna muhimmancin Benzema.

Baya ga kwallayen da ya zura, dan wasan na Faransa shi ne wanda ya fi taimakawa a zura kwallaye a kakar ta bana.

A bana, ba don kwallayen da ya ci wa Real Madrid da kuma wadanda ya taimaka ta ci ba, da yanzu an cire kungiyar a Gasar Zakarun Turai, ballanta a fara tunanin za ta lashe Gasar Laliga ta bana.

‘Dole mu gode wa Benzema’

Da yake bayani kan yadda dan wasan yake daukar nauyin Real Madrid, wani mai goyon bayan Real Madrid, Abubakar Abdullahi, ya ce lallai a kakar bana Benzema ne yake dawainiya da su, kuma dole duk masoyin kungiyar ya mishi godiya ta musamman.

A cewarsa, “Ko a wasan El-Classico da Barcelona ta jigge mu da ci 4-0, rashin Benzema ya nuna, wanda shi aka fi gani, amma kuma ba don golanmu ya yi kokari ba, da cin sai ya fi hudu,” inji shi.

Abubakar ya kara da cewa, “Benzema da ma tun da can yana kokari, kawai dai ba a cika ba shi goyon baya ba ne.

“Mutum ne da yake daura bukatar kungiyar sama da tasa, irinsu a duniyar kwallo ba su da yawa.

“Ya dade ana damawa da shi, amma ba a cika maganarsa, watakila saboda ya zo a zamaninsu Messi da Ronaldo ne.

“Yanzu a kakar badi da muke sa ran samun Mbappe a kungiyar, tun yanzu Benzema ya fara maganar yadda zai taimaka masa wajen zura kwallaye.

“Ka ga yanayinsa ke nan, shi dai kawai a samu nasara a kungiyar.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara