Yadda bikin aure ya koma na makoki a Gombe

A ranar Asabar da ta gabata ce wata amarya da ’yan biki da kuma ’ya uwan ango da amaryar suka hadu da tashin hankali bayan da suka samu labarin rasuwar angon a hadarin mota a hanyar Gombe zuwa Yola lokacin da suke dawowa daga daurin aurensa a garin Kumo fadar karamar Hukumar Akko a Jihar […]

Yadda bikin aure ya koma na makoki a Gombe
Yadda bikin aure ya koma na makoki a Gombe

A ranar Asabar da ta gabata ce wata amarya da ’yan biki da kuma ’ya uwan ango da amaryar suka hadu da tashin hankali bayan da suka samu labarin rasuwar angon a hadarin mota a hanyar Gombe zuwa Yola lokacin da suke dawowa daga daurin aurensa a garin Kumo fadar karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe.
Aminiya ta ziyarci Unguwar Barunde inda gidan su angon yake inda ta samu zantawa da yayan angon mai suna Isa Malam Usman mai shekara 27, wanda ya ce hankalinsu ya tashi lokacin da suka jin labarin rasuwar kanensa Sa’idu.
Isa Malam Usman ya ce Sa’idu wato angon shekararsa 25 kuma wannan ne aurensa na fari, kuma an daura ke nan ana dawowa sai motar da angon yake tukawa dauke da mutum bakwai ta yi hadari dukkansu suka rasu nan take ciki har da wata jaririya mai shan nono.
Ya bayyana marigayin kanensa da mutumin kirki mai son shiga jama’a da bai da wata matsala da kowa a gidan malaminsu da suke zaune fiye da shekara 18 da aka kawo su almajiranci. Ya ce sun dauki malaminsu Malam Usman a matsayin uba saboda mahaifinsu ya rasu.
Isa Malam Usman ya ce su ’yan asalin garin Potiskum ne a Jihar Yobe, amma tun da suka zo almajiranci sai suka zauna a Gombe a wurin malaminsu wanda yanzu shi ne kamar mahaifinsu.
An kai marigayi Sa’idu karatu wurin Malam Usman bayan shekara daya da fara mulkin Gwamnan farar hula na farko na Jihar Gombe Alhaji Abubakar Habu Hashidu, inji yayansa.
Malamin marigayin, Alaramma Malam Usman Muhammad, ya ce marigayi Sa’idu mutum ne mai biyayya da hakuri sannan komai zai yi sai ya nemi shawara idan kuma aka ce masa kada ya yi abu ko da bai ji dadin hakan ba zai bari kuma ba zai nuna a fuskarsa ba.
Alaramma Malam Usman, ya yi kira ga sauran almajirai cewa su zama mutanen kawarai masu yin koyi da irin halayen marigayin, wanda da wuya mutum ya ga bacin ransa.
daya daga cikin abokan angon mai suna Salisu Muhammad, da ya samu karaya a cinyoyinsa biyu da kuma hannu tare da yin raunuka yanzu haka yana kwance a dakin kofar gidan malamin yana jinya.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ASP Ahmed Usman ya tabbatar da aukuwar hadarin inda ya ce da shi aka yi sallar jana’izar mutanen a kofar fadar Mai martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Atiku.
Ya ce hadarin ya auku ne sakamakon mummunan gudu inda kuma tayar motar kirar Jepp mai lamba kA 360 GME ta fashe kuma dukkan mutane ciki su bakwai suka rasu nan take.
Ya ce sauran wadanda suka rasu tare da angon sun hada da A’ishatu Musa da Jamila Adamu da A’ishatu Hassan da Fatsuma Muhammad da Hauwa Musa da kuma Muhammad Babangida.
Kawun amaryar Umar Babuga ya shaida wa wakilinmu ta wayar cewa angon da mutanen da ke cikin motar sun samu mummunan hadari ne a lokacin da angon ya dauko ’yan bikin zai dawo da su Gombe bayan daurin auren.
Umar Babuga, ya ce gawarwaki bakwai aka samu nan take, sannan wasu bakwai sun ji munanan raunuka inda aka kai su asibitin Kumo don yi musu jinya, daga baya aka tura uku daga cikinsu zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Gombe a cikinsu daya ya cika daga baya.