Yadda bikin cika shekara 40 na Sarkin Ningi ya gudana
Aranar Asabar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Ningi da ke Jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Mohammed danyaya ya cika shekara 40 a gadon sarauta, wanda hakan ya sa ya fi dukan sarakunan masarautar 15 dadewa a kujerar sarauta. A baya Sarki Zakari wanda ya shekara 32 yana sarauta ne ya fi kowane Sarki a […]
Aranar Asabar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Ningi da ke Jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Mohammed danyaya ya cika shekara 40 a gadon sarauta, wanda hakan ya sa ya fi dukan sarakunan masarautar 15 dadewa a kujerar sarauta. A baya Sarki Zakari wanda ya shekara 32 yana sarauta ne ya fi kowane Sarki a masarautar dadewa.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin da aka shirya don taya Sarkin murna akwai Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na Biyu da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, da Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi da Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da Mai martaba Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo da sauran sarakuna da hakimai da dagatai da dubban masu rike da sarautun gargajiya daga ciki da wajen jihar.
’Yan siyasar da suka halarci bikin domin taya Sarkin murna har da wakilin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki da ya samu rakiyar sanatocin da suka hada da Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Isa Hamma Misau da na Bauchi ta Arewa Sanata Suleiman Nazif Gamawa.
Shugaba Buhari wanda Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya wakita ya taya Sarkin murnar kawowa wannan lokaci a matsayin Sarkin da ke jagorantar babbar masarauta irin wannan, sannan ya yaba masa game da yadda yake gudanar da shugabancinsa cikin gaskiya da amana da adalci. Sai ya roki Allah Ya kara wa Sarkin lafiya da tsawon rai.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya taya Sarkin murna duk da dimbin matsalolin da suke jibge a hidimar shugabanci, ya yi fatan Allah Ya bai wa Sarkin ikon sauke dukan nauyin da ke kansa ya ci gaba da jagorancin alu’mmarsa cikin adalci da zama lafiya.
Babban Bako Mai jawabi a wurin bikin, Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya ce masarautu da sarakuna jakadu ne na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Sarkin ya ce saboda addinin Musulunci ne ya kafa gidajen sarautar ya sa suka kasance fage na tarbiyyar al’umma da kyautata rayuwa kuma sarakuna suna samun martaba a idon jama’a da girmamawa wanda haka ke kara nuni da karbuwar masarautun a wajen al’umma duk da shudewar zamani.
Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar wanda Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Kawuwa Shehu Damina ya wakilta ya bayyana Sarkin a matsayin daya daga cikin manyan sarakuna masu fada-a-ji da suke kokarin wanzar da zaman lafiya da ci gaban jihar da Arewa da kasa baki daya.
Da yake jawabin godiya, Alhaji Yunusa Muhammad danyaya ya ce ikon Allah ne dalilin da ya sa ya kawo wannan lokaci yana gadon sarauta.
Ya ce shi ya sa suka tara jama’a domin bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma yin addu’o’in samun zama lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a masarautar da Najeriya baki daya.
Sarkin ya roki Gwamnatin Tarayya ta waiwayi batun gina madatsar ruwa ta Kafin Zaki, don bunkasa ayyukan noma a yankin musamman a wannan lokaci da gwamnati ta ba da fifiko kan harkokin noma. Sannan ya roki ’yan siyasa su rika tafiyar da harkokinsu na siyasa kamar yadda dokoki suka tanada domin dorewar dimokuradiyya.
An haifi Sarkin Ningi na 15 Alhaji Yunusa danyaya a 1935 a garin Ningi. Kuma shi ne Sarki na biyu daga gidan Malam Muhammadu Ciroman Ningi dan fitaccen mayakin nan Usman danyaya.
Ya yi firamare a garin Ningi daga nan ya halarci makarantar Midil ta Bauchi, sai Makarantar Koyon Aikin Tsabta (School of Hygiene) da ke Kano kafin ya je Jami’ar Ahmadu Bello inda ya yi diploma kan harkokin mulki.
Ya zama wakili a Majalisar Masarautar Ningi daga 1956 zuwa 1960, kuma ya zama Hakimin cikin Ningi kuma Chiroman Ningi daga 1959 zuwa 1960, kuma ya yi aiki a En’e ta Ningi da sauran hukumomin tsohuwar Jihar Arewa.
A zamanin Sarki Yunusa danyaya, masarautar ta samu ci gaba ta kowace fuska a fannin rayuwa da kuma ci gaban masarautar. A lokacin da aka nada shi, masarautar na da matsayin mai daraja ta uku ne, daga bisani aka daga darajar masarautar zuwa mai daraja ta biyu, sannan kuma ya zama Sarki Mai daraja na daya a zamanin mulkin soja na Janar Sani Abacha.