Yadda Bikin Cikar Sarkin Zazzau Shekara 40 ya gudana
Dubban jama’a daga sassan Najeriya da kuma wasu kasashen waje ne suka halarci bakin murnar cika shekara 40 a gadaon sarauta na Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Bikin wanda ya gudana ne a kofar fadar Sarkin da ke cikin garin Zariya, inda ya samu […]
Dubban jama’a daga sassan Najeriya da kuma wasu kasashen waje ne suka halarci bakin murnar cika shekara 40 a gadaon sarauta na Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Bikin wanda ya gudana ne a kofar fadar Sarkin da ke cikin garin Zariya, inda ya samu halartar manyan sarakuna da suka hada da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi da Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da sauran sarakuna daga jihohi daban-daban.
Wakilin Aminiya ya ce sauran mahalarta taron sun hada da manyan malaman addinin Musulunci da shugabannin addinin Kiristan da manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati masu aiki da wadanda suka yi ritaya da shugabannin al’umma da na ’yan kasuwa da jami’an tsaro da jakadun kasashen waje tare da makada da mawaka da makada da suka fito daga kasar Hausa da makwabtanta.
Daga cikin manyan bakin har da tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Birgediya Janar Abba Kyari wanda shi ne Gwanman da ya mika wa Sarkin sandar girma shekara 40 da suka gabata.
A wajen wannan bikin an shirya hawan dawaki na musamman wato hawan Daba, kuma makada da mawaka sun baje kolinsu a a fadar ta Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
Da yake gabatar da jawabi Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaj Sa’ad Abubakar ya shawarci sarakunan kasar nan su yi taka-tsantasn wajen sauke nauyin da ke kansu na jagorancin jama’arsu.
Ya ce, ya zama wajibi su fada wa jama’arsu gaskiya tare jawo hankalinsu a kan muhimmancin zaman lafiya domin kauce wa irin tashin hankalin da ya auku bayan zaben shekarar 2011.
Sarkin Musulmi ya kuma ce dole a fada wa ’yan siyasa gaskiya ta hanyar kin munanan manufofin da suka bullo da su.
Ya ce addinin Musulunci yana koyar da zaman lafiya da kuma nuna gaskiya da adalci ga kowa ba wai sai Musulmi kawai ba.
A sakon tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon wanda Janar Yakubu danjuma ya wakilta ya bayyana Sarkin Zazzau da cewa jagora ne da ke yin biyayya ga tsare-tsare da manufofin gwanmati tare da inganta al’adu a masarautar Zazzau da kasa baki daya.
Janar Gowon ya ce watsi da harkar ilimi musamman na firamare a yankin Arewa ya yi matukar illa ga rayuwa da zamantakewa. Ya tunatar cewa Shehu Usman dan Fodiyo ya yi bayani cewa mulki ba ya tabbata a hannun azzalumi koda yana da imani, yayin da yake tabbata a hannun mai adalci ko da ba mumini ba ne.
A jawabin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi godiya ga Allah bisa yadda Ya ba shi ikon jagoracin masarautar Zazzau har na tsawon shekara 40 wanda kuma take zaune lafiya da taimakon Allah.
Alhaji Shehu Idris Ya mika godiya ga gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna musamman na masarautar Zazzau bisa goyon baya da hadin kai da suke ba shi a tsawon wannan lokaci. Ya yi addu’ar Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya ganin lokacin zabe ya zo kuma ’yan siyasa su gudanar da harkokinsu ba tare wani tashin hankali ba.
An haifi Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ne a ranar 20/2/1936 a cikin birnin Zariya, kuma ya fara karatunsa ne da na addini yana da shekara biyar a duniya. Daga nan ya shiga makarantar firamare ta Zariya, a shekarar 1949 ya je Makarantar Midil sai Katsina Training College da kuma Makarantar Koyon Harkokin Mulki ta Jami’ar Ahmdu Bello da ke Zariya da kuma Makarantar Horar da Ma’aikata da ke Kaduna da Makarantar Koyon Harkokin Mulki da ke kasar Austireliya duk daga 1947 zuwa 1968.
Sarkin ya yi aikin koyarwa a firamare kafin ya koma aiki da Hukumar Lardi ta Arewa da Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar Arewa, kafin ya zama Magatarkadar Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu da sauransu.
Alhaji Shehu Idris ya zama Sarkin Zazzau ne a ranar 8/2/1975 bayan da masu zaben Sarkin su biyar marigayi Limanin Juma’a Malam Muhammadu Yero da Wazirin Zazzau Alhaji Nuhu Yahaya da Fagacin Zazzau Marigayi Muhammad Umar da marigayi Limamin Kona Malam Ahmad Balarabe Ibrahim da marigayi Makaman Zazzau Alhaji Halliru suka zabe shi.
Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris yana da mata hudu da ’ya’ya maza da mata da dama, kuma shi mutum ne mai sha’awar motsa jiki tare da nishadantuwa da wakoki na gargajiya.