Yadda bikin Goron Sallar Gizagawan Kano ya gudana
A ranar Asabar da ta gabata ce Gizagawan Jihar Kano suka shirya bikin Goron Sallah a dakin taro na Hasiya Bayero da ke daura da gidan Sarkin Kano. Taron wanda aka bude da addu’a da misalin karfe 11:05 na safe, an fara shi ne da jawabin maraba daga bakin Shugaban Gizago na Jihar Kano, Malam […]
A ranar Asabar da ta gabata ce Gizagawan Jihar Kano suka shirya bikin Goron Sallah a dakin taro na Hasiya Bayero da ke daura da gidan Sarkin Kano.
Taron wanda aka bude da addu’a da misalin karfe 11:05 na safe, an fara shi ne da jawabin maraba daga bakin Shugaban Gizago na Jihar Kano, Malam Kabir Halliru Gogel, tare da bayyana makasudin taron kamar yadda ya samo asali.
Bayan nan sai Babban Ma’ajin Gizago na kasa, Malam Kabir Ghali Ibrahim ya gabatar da makala mai taken ‘Jirwaye Mai Kamar Wanka’ inda ya tabo batutuwa da dama a kan kungiyar Gizago da mabiyanta, dangane da fadakarwa, tunatarwa, da kuma zabuwarwa wajen aikin alheri da kungiyar take gabatarwa.
Shi ma a nasa tsokacin, tsohon Shugaban Riko na kasa kuma tsohon Shugaban kungiyar ta Jihar Kano, Nura Adamu Ahmed ya jawo hankalin Gizagawa ne, tare da nuna musu irin fadi-tashin da shugabanin uwar kungiyar na kasa suke yi a kullum domin ganin an samu ingantaccen hadin kai da kawo sauyi mai ma’ana. A karshe, ya yi kira cewa ya kamata a samar wa kungiya hanyoyin dogaro da kanta.
Ita ma a nata jawabin, Shugabar Mata ta kasa, Hajiya A’isha Lawan Tarauni, ta nuna fushinta ne kan yadda ta ga abubuwa ke kokarin lalacewa, inda ta dora alhakin hakan ga mambobi. Ta ce lallai sai an samar wa kungiyar mafita.
Nan take Shugaban Gizago na kasa, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe ya ba ta hakuri tare da tabbatar da samun mafita.
A sakon godiya, Hajiya Hauwa J. Ahmad, Shugabar Mata Gizagawa na Jihar Kano, nuna farin ciki ta yi da ganin tsofaffin fuskoki da ta jima ba ta gani ba. Daga karshe ta yi addu’ar fatan alheri ga mahalarta taron.
A yayin taron, an mika takardun karramawa da yabo ga Madugun Zumunci, Malam Bashir Yahuza Malumfashi da tsohon Shugaban kungiyar Gizago na farko, Alhaji Muntaka Abdul-Hadi Dabo da Shugaban Gizago na kasa da ke kan kujera yanzu, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe tare da wadansu Gizagawan.
Sakon jajantawa ga Gizagawa
Bagizage Naziru Tamburawa Jihar Kano, 0703 878 5658 (Mahaifinsa ya rasu).
Bagizagiya Rukayya Zubairu Jihar Filato, 08167067187 (Mahaifinta ya rasu).
Bagizage Adamu Yahaya, Jihar Gombe, 0806 225 3727 (Matarsa ta rasu).
Bagizage Ibrahim Gani dan Sarki Jihar Gombe, 0706 610 5594 (Mahaifinsa ya rasu).
Muna addu’a a gare su, Allah Ya jikansu da Rahama, Ya gafarta musu kura-kuransu, amin.