Yadda Bikin Makon Adabi na Marubutan Jihar Kano ya gudana a bana
Kungiyar Marubuta ta Kasa (ANA), Reshen Jihar Kano ta gudanar da gagarumin taronta na rubutu da marubuta na bana a Kano. Taron wanda aka gudanar na tsawon kwana hudu, an fara shi ne daga ranar Alhamis, 6 ga Disamba aka kammala ranar Lahadin da ta gabata, a karkashin jagorancin shugabanta, Malam Zaharaddin Ibrahim Kallah. An […]
Kungiyar Marubuta ta Kasa (ANA), Reshen Jihar Kano ta gudanar da gagarumin taronta na rubutu da marubuta na bana a Kano.
Taron wanda aka gudanar na tsawon kwana hudu, an fara shi ne daga ranar Alhamis, 6 ga Disamba aka kammala ranar Lahadin da ta gabata, a karkashin jagorancin shugabanta, Malam Zaharaddin Ibrahim Kallah.
An bude taron na bana mai taken ‘Makon Adabin Jihar Kano,’ domin bunkasa adabi ta hanyar farfado da dabi’ar karance-karancen littattafai da suka shafi adabi da baje kolin sauran dukkan wasu dabi’u da ke da alaka da karatu da rubutu. Sannan an gabatar da laccoci da tarukan kara wa juna sani da koyon rubuce-rubucen adabi da nazarinsu da kacici-kacici a tsakanin daliban sakandare da tattaunawa a tsakanin marubuta da baje kolin littafan adabi da gabatar da karatu ga dalibai da bayar da lambobin girmamawa da sauransu.
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ne uban taro a yayin bude makon. Kuma kamar yadda aka san shi da dabi’ar girmama lokaci, Mai martaban ya bayyana a dakin taron da safiya tun kafin sauran mahalarta taron su kammala halarta. Ya halarci babban taron tare da manyan hakimansa goma.
Bayan Mai martaba Sarki, taron ya samu halartar manyan farfesoshi da malamai da marubuta da manazarta da dalibai da ’yan jarida. Daga cikinsu sun hada da kwararren marubuci kuma hamshakin dan siyasa, Alhaji Bashir Othman Tofa da Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Farfesa Mustapha Ahmad Isa wanda ya kasance Shugaban Taron da Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Adamu Idris Tanko da kuma Farfesa Habu Muhammad Fagge, wanda zamo mai gabatar da jawabi.
Sauran masanan sun hada da Farfesa Aliyu Kamal da Farfesa Isma’ila Zango da Farfesa A’isha Isma’il da Dokta Nu’uman Habib da Dokta Musa Auyo da Dokta Ibrahim G. Satatima da Dokta Saka Aliyu da Dokta Isma’ila Bala da Maude Rabi’u Gwadabe da Tijjani Muhammad Musa da Khalid Imam da sauran mutane da dama.
Bayan Farfesa Habu Muhammad Fagge ya gabatar da takarda kan rawar da rubutun littattafan adabi ke takawa a cikin tafiyar siyasa da kuma gudunmawar da marubuci zai iya bayarwa wurin tsarkakewa tare da bunkasa siyasa, an kuma gayyaci wadansu shahararrun mutane, ciki har da Alhaji Bashir Othman Tofa domin su gabatar da karatu ga daliban makaranta.
A jawabin, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana mai zurfi kan muhimmancin neman ilimi da yadda ilimin zai zamo wani sinadari na bunkasa rubuce-rubucen adabi. Ya yi kira kan a bai wa harshen Hausa muhimmanci da kuma amfani da shi a matsayin harshen da za a rika amfani da shi wurin karatu a makarantunmu. Ya nanata muhimmancin amfani da harshen Hausa wurin koyar da darussan kimiyya da fasaha da kiwon lafiya a makarantunmu.
Kuma ya yi kira ga marubuta su fafada rubuce-rubucensu wurin bayyana matsalolinmu na yau da kullum kamar matsalolin zamantakewar aure da shaye-shaye, tarbiyar yara da sauransu a cikin rubutunsu domin fadakarwa da wayar da kan al’umma.
Taron ya samu masu gabatarwa biyu; na Ingilishi da Hausa. Tsohon Shugaban Hukumar ‘A Daidaita Sahu’ ta Jihar Kano kuma babban malamin jami’a, Dokta Bala Muhammad ne ya zamo mai gabatarwa na daya cikin harshen Ingilishi sai Malam Nasiru Wada Khalil, babban ma’aikaci a Ma’aikatar Shari’a kuma manazarci ya zamo mai gabatarwa na biyu cikin harshen Hausa.
A yammacin ranar ne kuma kungiyar marubutan ta gabatar da taron jawabi daga bakin marubuta na Ingilishi a Dakin Karatu na Murtala Muhammad da ke Kano. Manyan marubutan da suka gabatar da jawabi a taron sun hada da Dokta Bala Muhammad da Shugaban Cibiyar Fasahar Sadarwa (CITAD), Injiniya Y. Z Ya’u da Malama Maryam Ali Ali da kuma Malam Kabiru Musa Jammaje, wanda Usama Jilani Dayyab ya wakilta.
A yammacin ranar Lahadi da aka rufe bikin Makon Adabin, an karrama wadansu fitattun marubuta da suka taka rawar gani a duniyar rubutu. Wadanda aka karrama a rukunin farko sun hada da Alhaji Bashir Othman Tofa da Farfesa Abdallah Uba Adamu da Farfesa Mustapha Ahmad Isah da Farfesa Adamu Idris Tanko da Farfesa Aliyu Kamal da Dokta Bukar Usman da Zaharaddeen Ibrahim Kallah da sauransu.
A rukuni na biyu, an karrama Abdulkadir Badsha Mukhtar da Aliyu Abubakar da A’isha Zakari da Abba Shehu Musa da Aminudden Ladan Abubakar (ALA) da Aminu Salisu Giginyu da Danladi Z. Haruna da Faruk Lawan Da’u da Kabiru Musa Jammaje da Khalid Imam da sauransu.
Haka an karrama wadansu marubuta da suka riga mu gidan gaskiya, domin tunawa da su, wadanda suka hada da Malam Hadi Alkanci da Muhammad Balarabe Sango da Malama Rukayya Umar Maikarfi da Malam Sulaiman Sani da Abdullahi Mukhtar Yaron Malam da Malam Bashari Farouk Roukba, Allah Ya jikansu.