Yadda bikin yaye dalibai da karrama mashahuran mutane karo na 37 ya gudana a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya
A ranakun Juma’a da Asabar na makon jiya ne Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta gudanar da bikin yaye dalibanta, karo na 37 tare da karrama mashahuran mutane uku da digirin girmamawa.A bikin na bana, jimillar dalibai 1,4067 ne jami’ar ta yaye a matakan digiri daban-daban, inda a cikinsu dalibai 33 me suka samu kyakkyawan sakamakon […]
A ranakun Juma’a da Asabar na makon jiya ne Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta gudanar da bikin yaye dalibanta, karo na 37 tare da karrama mashahuran mutane uku da digirin girmamawa.
A bikin na bana, jimillar dalibai 1,4067 ne jami’ar ta yaye a matakan digiri daban-daban, inda a cikinsu dalibai 33 me suka samu kyakkyawan sakamakon Digiri Mai Babbar Daraja (First Class). Haka kuma, an karrama mashahuran mutane uku da digirin girmamawa. Mutanen sun hada da fitaccen marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a fadar Shugaban kasa, Dokta Bukar Usman da tsohon Ministan Man Fetur Da Makamashi, Alhaji Shettima Ali Munguno da kuma Yarima Talal Abdul’azeez Bin al-Saud, dan kasar Saudi Arebiya.
Bikin wanda ya gudana a harabar jami’ar na dindindin da ke Samaru Zariya, ya faro ne a maraicen Juma’a, inda aka gabatar da kwarya-kwaryan taron lacca. A yayin laccar, wacce aka gabatar a babban dakin taro na jami’ar, bisa shugabancin farfesa Mahmood Yakubu ta samu halartar Babban Shugaban Jami’ar, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar (III) da Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Mustapha da hamshakan malaman jami’a, dalibai da sauran mutane da dama da suka fito daga bangarorin rayuwa daban-daban.
Laccar mai taken: ‘Yadda Za A Samar Da Tsarin Ilimi Mai Tasirin Samar Da Aikin Yi Da Biyan Bukatar Al’umma A Najeriya’ tsohon Sakataren Hukumar Kula Da Jami’o’in Najeriya, Farfesa Peter A. Okebukola ne ya gabatar da ita. Ya yi bayani dalla-dalla na matsalolin da ke addabar tsarin ilimi a Najeriya, inda ya bayyana cewa mafi yawan dinbin daliban da jami’o’in ke yayewa ba su samun isasshen ilimin da zai sama musu aikin yi ko kuma su dogara da kansu wajen tafiyar da wata sana’a ta kashin kansu.
Shehin malamin, ya nuna cewa wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da matsaloli a harkar ilimi da ilimantarwa a Najeriya sun hada da rashin kwararru kuma ingantattun malamai da rashin isassun kayan aiki da kuma hanci da rashawa da suka yi katutu a tsakanin malamai da dalibai. Haka kuma ya nuna cewa mafi yawa daga daliban suna nuna halin ko-in-kula wajen neman ilimi, inda ba su mayar da hankali ga karatu da sauransu.
A rana ta biyu, wato Asabar, an fara gudanar da bikin yaye daliban da misalin karfe tara na safe, a babban filin wasanni na jami’ar. A jawabinsa, Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Mustapha, ya taya murna ga daukacin daliban da aka yaye sannan ya yi kira na musamman a gare su da su zama jakadu na kwarai wajen tafiyar da rayuwarsu cikin al’umma.
“A daidai wannan lokacin, bari in tunatar da daliban da ake yayewa a yau cewa ku sani, daga lokacin da aka mika maku takardar shaidar kammala digiri ko diploma, wannan na nufin kun shiga cikin kungiyar daliban jami’ar nan guda sama da dubu 500 da aka yaye a shekaru hamsin da suka gabata. Za a rika jaraba ku a duk inda kuka shiga sannan a rika yi maku alkalanci, a ga irin yadda kuke tafiyar da al’amuranku, domnin a ga za ku kamo ko ku yi daidai da zakakuran dalibanmu na baya da suka ciri tutu a fannoninsu a kowane sako na Najeriya?” Inji Farfesa Abdullahi.
Da ya juya wajen mashahuran mutanen da jami’ar ta karrama da digirin girmamawa, kuwa shugaban jami’ar ya bayyana cewa: “Ya dace a wannan lokacin, in tabbatar da alfaharin Jami’ar Ahmadu Bello wajen karrama Alhaji Shettima Ali Mungono, Dokta Bukar Usman da Yarima Talal Abdul’azeez Bin al-Saud. Jami’ar ABU ta karrama wadannan mutane ne saboda sun ba da gagarumar gudunmowa wajen bunkasa al’umma.”
Shi ma babban malami a jami’ar kuma daya daga cikin wadanda suka tantance da amincewa da zaben wadanda aka karrama, Dokta Bashir Kurfi ya bayyana cewa cancanta ce ta sanya suka amince da mutanen da aka karrama. Ya kara da cewa ba a kula da matsayi ko mukami ko dukiya wajen karrama mutum a ABU, suna duba cancanta ne kawai. “Wannan shi ya sanya har zuwa yanzu da ABU ta haura shekara hamsin da kafawa amma har yanzu wadanda aka karrama ba su kai mutum hamsin ba, domin cancanta muke dubawa ba mukami ko dukiya ba.” Inji Dokta Kurfi.
An kammala bikin lami lafiya.