Yadda birnin Makkah ya yi cikar kwari da alhazai bayan kammala Aikin Hajji

Alhazai sun kammala Aikin Hajji, sun koma Makkah

Yadda birnin Makkah ya yi cikar kwari da alhazai bayan kammala Aikin Hajji

Birnin Makkah ya cika ya batse bayan alhazan bana sama da miliyan 2.5 daga fadin duniya sun yi masa cikar kwari bayan sun kammala Tsayuwar Arfa da Zaman Muzdalifa da kuma Mina.

A ranar Asabar rukunin karshe na alhazan da suka fito daga kasashe kimanin 160 suka baro tantunansu da ke Mina zuwa cikin birnin Makkah.

A yanzu haka babu masaka tsinke a harabar tsakiyar Masallacin Harami, saboda wanan masu dawafi, haka ma lamarin yake a daukacin wurin yin Sa’ayi da kuma wurin dawafi da ke a hawa na farko da na biyu, har ma da na saman rufin masallacin na Harami.

Sayayyar tsaraba

A shugunan da ke zagayen masallacin da cikin gari kuwa da sauran wurare kuwa, alhzai sun dukufa yin sayayyar tsaraba da za su kai gida, a yayin da suke jiran sanarwar lokacin da za a fara mayar da su kasashensu.

Ga alhazan Najeriya, abubuwan da suke jira daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) bayan sanarwar, sun hada da karbar manyan jakunkuna da za su sa kayansu da kuma fara aikin cibiyoyin awon kaya da kuma jigilarsu zuwa inda za a kwaso musu su zuwa Najeriya.

Wasu alhazai dai tun ranar da suka sauka a ƙasar Saudiyya suka fara yin sayayyar tsaraba a Madina, musamman ma na dabinon Ajwa, wanda shi ne nau’in dabino mafi daraja.

Wasu alhazai har gidan gona suka je domin su sayo Ajwa, wanda ya samo asali daga birnin, kuma ake dangantawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Da suka koma Makkah kuma suka dora daga inda aka tsaya, a manyan shagunan zamani da na cikin unguwanni, da ma suk inda suka yi arba da abin da suke son saye.

Baje-kolin Mina

Haka ma a Mina inda tukari da ’yan Bangladesh suka baje-kolin kayan yari, da na shafe-shafe da takalma da huluna da rawunna da makawuya da turaruka da jallabiyoyi da abayoyi da sauransu manya da kanana — sabbi da na gwanjo — har ma da abincin gargajiya irinsu fura da sauransu.

Rububin sayen fura

Aminiya ta yi kicibus da wani cincirindon jama’a gab da magariba a kusa da masaukin alhazan jihohin Kano da Kebbi, ana rububin sayen fura a wurin wata tukari.

“Ba Saudiyya ka zo ba, ko Legas ka je haka za ka iske mutane suna layin sayen fura,” in ji wani alhaji, wanda ya je sayen fura a wajen, amma ya ki bayyana mana sunansa.

Shi kuma wani cewa ya yi, “Ai dole sai mutum ya samu ya haɗa da fura ko wani abincin gida tunda dai ana samu nan, ai wannan ba abun kunya ba ne.”

Ana dama furar ce a kan Riyal 5 (Kimanin N1,000) zuwa sama

Akwai kuma wata wadda muka gani tana sayarwa a gaba masaukin alhazan Jihar Kogi alhzai masu saye sun baibaye ta, amma ba su yi mana magana ba.

Hada-hada a Makkah

Yanzu da alhazai suke zaman jiran lokacin komawa gida daga Makkah kuma, hadahadar kasuwanci ta kara kankama.

Hasali ma, lokacin da tukari suke baza hajojinsu a gefen tituna da dare ya fadada zuwa cikin yini, a unguwanni irinsu Shara’-Mansur.

’Yan tuwo-tuwo

Masu abincin gargajiya da kayan kwalama irin na Najeriya kuma kakarsu ta yanke saka.

Wakilinmu ya zaga wani wuri da tukari suke sayar da abinci, inda alhazan Najeriya suke in-ba-ka-yi-ba-ni-wuri.

Wani alhaji daga Jihar Kebbi, ya ce, “Abin mamaki wai ga shi tuwo za ka saya, sai ka yi kokawa. Shi ma ba lallai ka samu ba

“Yo ni a gida me zai hada ni da tuwo; da daidai shinkafa da wake ne, wannan kuma lafiya lau,” in ji Alhaji Bashir.

Wani dattijo, Alhaji Musa daga Jihar Jigawa ya shaida mana cewa ya je sayen tuwo da miya a wajen tukari bayan dawowarsa Makkah daga Mina, amma ya samu “Abincin ya kare, dayar kuma ba ta fito ba, saboda haka na hakura, zan je in sayi shinkafa da wake a wurin wata wacce na wuce a baya.”

Alhaji Muhammad daga Jihar Kaduna ya ce, “Da ma kafin mu tafi Mina na bar madara a cikin firinji shi ne na sha a matsayin abincin rana da muka dawo.

“Da ma da safe da za mu dawo na yi guzurin kwai da aka ba mu a Mina, Shi ne na ci da farar shinkafa da miyar wake da muka saya a wajen wata ’yar kasar Saliyo, a matsayin abincin rana da na dare.”

Ana ciyar da alhzai da safe da kuma dare, amma wasunsu sukan gwammace sayen yaka-malam a wurin tukari da rana.

A bangaren kayan kwalama na ’yan Najeriya kuma, mun ji wani malami da ya je sayen soyen kayan ciki a wurin wani tukari yana cewa, “Riyal biyar fa”, cikin mamaki, saboda tsadar da ya ga ya yi.

Shi kuma tukarin ya mayar ajiya, wata mai son na daidai kudin tana tambaya ya mika mata ya karbi kudin.

Daga baya malamin ya nemi ya sa masa, sai ya ce, “Baba ka ce na Riyal biyar za a ba ka, na sa kuma ka ce ya yi tsada,” nan take malamin “to, na fasa saye.”

A wurin ne Aminiya ta ga yadda alhazai suke rububin sayen farfesun ganda da soyayyen naman kaza, baya ga wurin masu sayar da tuwo da miyar yauki.

Rububin zuwa Jidda

Hakazalika, motocin haya masu daukar alhzai zuwa birnin Jidda kuma sun zama ruwan dare.

Jidda birnin kasuwanci ne da ke da tashar jirgin ruwa a kasar Saudiyya, don haka alhzai sukan je birnin da tunanin samun saukin farashi da kuma yawan kaya a can fiye da Makkah da Madina.

Duk da cewa akwai alhazai da ke ganin zuwa Jidda a matsayin wani abu ne na ba wa ido abinci, wasu na ganin za su samu duk abin da suke so na tsaraba, ko suka rasa ko ya yi tsada sosai a Makkah, za su iya samu a Jidda kuma cikin sauki.

Yawanci alhazai kan shafe tsawon yini ko ma su yi dare kafin su dawo Makkah idan suka je Jidda yin sayayya, kasancewar galibi ’yan kasuwa a can sun fi fitowa ne bayan azahar.

Yadda alhazai suka yi Babbar Sallah a Masallacin Harami

Tun a safiyar a ranar Babbar Sallah dubban daruruwan alhazai suka yi cikar kwari a Masallacin Harami domin yin ‘Dawaful Ifada’ bayan sun baro Muzdalifa, inda wadanda suka yi sammako daga cikinsu suka samu halartar Sallar Idi a masallacin na Harami.

“Mun gama jifan Jamra da misalin karfe 3.30 na dare, muka wuce Makkah a mota, muka yi Sallar Asuba, a nan muka yi Dawaful Ifada, muka yi Sallar Idi.

“Bayan mun gama Dawadi da Sa’ayi muka wuce masaukinmu a Masfala, muka cire Ihrami, muka yi wanka muka sa kayan sallah muka huta, bayan La’asar muka dawo Mina,” in ji Alhaji Usman daga Jihar Taraba.

Ya ce kafin sannan kafin faduwar rana suka koma Mina domin karashen zaman kwana biyu ko uku da kuma yin Jifan Shaidan.

Yadda muka bace bayan Jifan Shaidan —Alhazai

Aminiya ta gano yadda alhazai da dama da suka bata hanyar komawa masaukansu da ke Mina bayan sun yi jifa a ranar farko (ranar Sallah) inda wasu daga cikinsu suka shafe tsawon yinin suna bilimbituwa kafin su gane masaukinsu ko suka samu aka kai su.

Haka lamarin ya kasance da wasu daga cikin wadanda suka je yin Dawafi a Makkah bayan sun dawo Mina.

Wani alhaji daga Abuja ya ce, “Ba zan iya kwatanta iya nisan tafiyar da na yi kafin na iya dawowa tantinmu ba.

“Tun safe nake yawo bayan na yi jifa, sai kusan magariba iya na gane wurinmu da kyar.

“Na yi yawo har na rasa ina zan yi — in koma baya ko in yi gaba, amma na ce bari in yi gaba kawai — amma duk da haka sai da ta kai jan kafafuna kawai nake yi saboda tsabar wahala.

“Ai da na dawo, tun na kwanta ban farka ba sai da aka tashe ni da asuba.”

Shi kuma wani alhaji, wanda dan jarida ne daga Kano, ya ce su ma sun yi batar hanyar dawowa daga wurin jifa.

“Mun zo har kusa da tantinmu, muka ga wannan alamar, amma ba mu gane ba, sai muka kara komawa baya, da kyar muka iya dawowa bayan an tura mana taswirar wajen ta GoogleMap.

“Washegari da muka fita za mu koma jifa ne muka gane ashe wurin da muka fara zuwa jiya kusa yake da tantinmu.”

Dalilin bacewar alhazai a Mina

Yawancin alhazan da muka zanta da su sun danganta bacewar tasu da bakunta musamman yadda yanayin tantuna da da titunan da ke sansanin Mina suke kamanceceniya da juna da kuma yadda jami’an tsaro sukan tare hanya domin guje wa cunkoso ko turereniya.

Akwai matsalar bambancin harshe inda alhazai ba sa iya tambayar takwarorinsu daga wasu ƙasashe ko yadda jami’an Saudiyya, su iya musu kwatance.

Akwai kuma wadanda suka ki bin kwatance da aka yi musu, wasu kuma ba su yi tambaya ba, gaban kansu suka yi, suna lalube a cikin duhu.

Wani alhaji daga Jihar Legas, Abdulwahab Wasiu, cewa ya yi, “Tun da muka baro wurin jifa, hanyar da muka bi daidai ce, saboda muna ta tambayar jami’an tsaro su nuna mana.

“Amma sai aka kai wata gaba da muka yi kokwanton hanyar da suka nuna mana, muka bi wata, daga nan komai ya lalace mana, sai da muka wahala kafin mu gane wurin nan.”

Wasu dai su yi gamon Katar inda suka samu wadanda suka nuna musu masaukinsu ko kusa da shi ko aka hada su da jami’an hukumar aikin Hajji da suka sada su da masaukan nasu.