Yadda ’yan ta’adda suka kashe sojoji da ’yan sanda 967 a shekara 2

Abubuwan da binciken Aminiya ya gano kan yadda aka kashe ’yan sanda 581 da sojoji 384 a Najeriya daga 2021 zuwa 2023

Yadda ’yan ta’adda suka kashe sojoji da ’yan sanda 967 a shekara 2

Kimamin sojoji da ’yan sanda 965 ne suka rasa rayukansu a bakin aiki a sanadiyyar ta’addancin Kungiyar Boko Haram da ’yan fashin daji da masu rajin kafa kasar Biyafara (IPOB) da wasu tsirarun mutane suka kashe a cikin shekara biyu.

Aminiya ta bi diddigi tare da binciko yadda aka kashe wadannan jami’ai a tsakanin watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Afrilun 2023, inda sakamakon binciken ya gano cewa jami’an tsaron Najeriya sun hadu da dimbin asarar rayuka sakamakon kisansu da wasu ba suka yi.

A binciken da ta yi ta hanyar tattara rahotannin jaridu daban-daban a kan kisan jami’an tsaro da aka bayar da rahoto, ta gano cewa ’yan sanda 581 da sojoji 384 ne aka kashe a bakin aiki a tsakanin wannan lokaci.

Sai dai hakan, kamar yadda wasu manyan tsofaffin jami’an tsaro suka bayyana ba zai sa jami’an su karaya ba wajen tabbatar da doka da oda a Najeriya.

Aminiya ta yi kokarin samun tabbataccen bayanai daga masu magana da yawun hukumomin biyu, Onyema Nwachuku na Rundunar Soji da Muyiwa Adejobi na Rundunar ’Yan sanda, amma hakarta bai cim ma ruwa ba.

Sai dai wasu bayanai daga Rundunar ’Yan sandan Najeriya sun bayyana cewa rundunar tana da jami’ai 371,800 a fadin kasar nan, wanda ke nuna duk dan sanda daya na lura da mutum 540.

Wannan ya haura yawan mutanen da ya kamata kowane dan sanda ya kula da su a kai’dar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na kowane dan sanda ya kula da mutum 450.

Haka su ma a bangaren sojoji, kundin bayanai na Bankin Duniya ya bayyana cewa a shekarar 2019, Najeriya na da sojoji 223,000.

Alkaluman kashe jami’an tsaro

Aminiya ta gano cewa cikin sojoji 384 da aka kashe, 192 ’yan ta’addar Boko Haram ne suka kashe su, sai 68 da ’yan IPOB suka kashe, sannan 62 ’yan bindiga da kuma 62 da kungiyoyin daban-daban da ke tada kayar baya suka kashe.

Rahotannin jaridu kuma sun bayyana cewa ’yan sanda 344, ’yan ta’addar IPOB ne suka kashe, 119 kuma ’yan bindiga da masu garkuwa ne, inda 53 ’yan fashi da sauran bata-gari suka kashe.

Har wa yau, alkaluman sun nuna cewa, ’yan sanda 32 ne suka rasu ta sanadiyyar hadari, 18 kuma abokan aikinsu ne suka kashe su. Sai kuma sauran 15 da Boko Haram da ISWAP suka kashe.

Yankin da aka fi kashe da sojoji

A binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa, sojoji 178 aka kashe a Arewa maso Gabas, sai 90 a Arewa maso Yamma, 49 kuma a Arewa ta Tsakiya.

Kudu maso Gabas kuma sojoji 41 aka kashe, yayin da Kudu maso Kudu aka kashe 24, Kudu maso Yamma kuma guda biyu kacal.

Wanda hakan ke nuna cewa kaso 82.6 na kisan duk a yankin Arewa yake sai kaso 17.4 a Kudu.

A jihohin da wannan lamari ya fi kamari kuma Jihar Borno ce kan gaba a yawan sojojin da aka kashe, inda sojoji 152 suka rasa rayukansu a wannan tsakani.

Daga nan sai Jihar Kaduna inda aka kashe sojoji 35, sai Jihar Neja sojoji 28, Jihar Kebbi 23, sai kuma Jihar Anambra an kashe sojoji 20.

Jihohin da aka fi kashe ’yan sanda

A bangaren ’yan sanda, a cikin 581 da aka kashe kaso 60 duka a yankin Kudu aka kashe su, sai sauran kaso 40 a Arewa.

Har wa yau, bayanan sun nuna cewa ’yan sanda 305 ne aka kashe sakamakon harin kwanton-bauna da ’yan bindiga suka kai; inda yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu suka dauki kashi 73.7 na alhakin wadannan kashe-kashe.

A shiyya-shiyya kuma, ’yan sanda 200 ne aka kashe a Kudu maso Gabas, 110 a Arewa maso Yamma, 106 a Kudu maso Kudu da 85 a Arewa ta Tsakiya.

Har wa yau, 43 a yankin Kudu maso Yamma da 37 a Arewa maso Gabas.

Jihohi biyar da aka fi kashe ’yan sanda sun hada da Jihar Anambra inda aka kashe ’yan sanda 63, sai Jihar Imo 52 sai Jihar Neja 42.

Sauran jihohin sun hada da Jihar Delta 37 da Jihar Ebonyi 35.

Kisan ba zai sa jami’an su karaya ba

A lokacin da Aminiya ta zanta da Manjo Muhammad Bashir Galma (mai ritaya) a kan lamarin, ya shaida mata cewa ba abin mamaki ba ne a iya samun asarar rayukan jami’an musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsalar tsaro a Najeriya.

Sai dai ya ce duk wani soja da aka kashe sakamakon hakan ba karamin rashi ba ne ga Najeriya.

Manjo Galma ya bayyana adadin sojojin da aka kashe a bakin aiki a matsayin abin tsoro, sai dai ya ce dangane da yadda aikin soja yake, abu ne sananne ana asarar irin wadannan rayuka, don haka wannan ba zai sa sojojin su karaya ba.

A bangaren Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda (AIG), Wilson Inalegwu (mai ritaya), ya ce harin kwanton-bauna da ake kai wa ’yan sanda musamman a Kudu maso Gabas ba zai yi tasiri ga kwarjinin ’yan sandan ba, domin duk wanda ya shiga wata hukumar tsaro ya san cewa ba abin da ba zai iya faruwa ba.

Musabbabin kai wa jami’an tsaro hari

AIG Inalagwu, ya alakanta yawaitar samun irin wadannan laifuffuka da rashin aikin yi, talauci da jahilci da sauransu, inda ya ce dole ne gwamnati ta magance duk wani abu da ke sa a aikata irin wadannan laifuffuka.

Ya ce, “Dole ne a magance tushen wannan matsala domin dakile wadannan hare-hare da kashe-kashe da ake yi wa ’yan sanda. Kuma dole ne a kara inganta alakar da ke tsakanin ’yan sanda da al’umma domin su rika ba su bayanan sirri.”

Ya kara da cewa, “Akwai bukatar a kara horo a cikin tsarin don taimaka wa ’yan sandan kan yadda za su tsira da rayukansu.”

Ya ce, ’yan sanda na iya kokarinsu wajen ganin sun yi aiki daidai da yadda doka ta tanada wajen ganin sun kawo dauki duk lokacin da aka bukaci haka, duk da sun san akwai hadari a irin wannan fita.

“Amma saboda sha’awar aikin da son taimaka wa mutane sai ka ga an yi musu kwanton-bauna an kashe su.

“Abu daya da zai iya karya masu gwiwa a wannan aiki nasu, shi ne halin da iyalansu za su shiga bayan tsautsayi ya fada musu kan irin hakkokin da ya kamata a biya su da kuma tuna za a kori iyalansu daga bariki da sauransu.

“Irin wadannan su ne abubuwan da kawai za su sa ’yan sanda su karaya ba yawan kashe-kashen ba,” in ji shi.

‘Samar da ingantattun kayan aiki da shugabanci na kwarai zai kawo dauki’

Wasu jami’an soji da ’yan sanda da ke filin daga sun shaida wa Aminiya cewa idan za a samu ingantaccen shugabanci a bataliyoyin soji da bangaren ’yan sanda da kuma ingantattun kayan aiki za su iya rage yawan kashe-kashen da ake yi wa jami’an tsaron.

Wani karamin soja da ke aiki a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ya ce irin harin kwanton-bauna da ake kai wa sojoji a wasu lokuta na karya wa wasu gwiwa. Sai dai ya ce “Amma mu sojoji ne, mun riga mun saba,” in ji shi.

“Sau tari irin wannan hari na kwanton bauna, abokan fada na samun nasara da kusan 99 cikin 100, domin duk wanda ya shirya yin kwanton-bauna ya san a shirye yake.

“Kawai abin da muke yi a yanzu don ganin mun tsira shi ne kasancewa cikin shiri a koyaushe,” in ji shi.

Ya kara da cewa da shugabanninsu za su rika aiki yadda ya kamata, ba za a rika samun yawan kashe-kashen ba.

Shi ko wani wani babban dan sanda da ke aiki a yankin Kudu maso Gabas ya ce, idan za a samar masu da kyawawan kayan aiki da kuma abubuwan da za su karfafi gwiwarsu, da ba za a rika kashe su haka nan barkatai ba.

“Duk wanda ya ce maka yadda ake kashe mu ba ya damun mu, ba gaskiya ya fada ba. Mu fa ake turawa wadannan wurare da ake fama da rikici domin samar da zaman lafiya,” in ji shi.

Jami’in ya kara da cewa in za a samar da abubuwan da za su kara wa jami’ansu karfin gwiwa irin karin albashi da karin horo da kuma kayan aiki na zamani da ’yan sanda za su iya dakile wadannan hare-hare da ake fama da su.

 

 

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya