Yadda Boko Haram ta ƙyanƙyashe sabbin mayaƙa 60,000 —Shugaban Sojoji
Ya ce yara 60,000 sun miƙa wuya a baya-bayan nan.
Shugaban Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce yara sama da 60,000 na daga cikin mayaƙan Boko Haram 120,000 da suka miƙa wuya a baya-bayan nan.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise, Janar Musa ya bayyana cewa yawancin mayaƙan Boko Haram ba su shiga ƙungiyar don son ransu ba, ciki har da yaran da aka tilasta musu ko kuma aka bautar da su.
- Abba ya ƙaddamar rabon kayan makaranta kyauta ga ɗalibai 789,000 a Kano
- Gwamnatin Kano ta fara shirin yaƙi da matsalar shara
“Ba duk wanda ke cikin Boko Haram ba ne ɗan ta’adda b6,” in ji Musa.
“Wasu an tilasta su shiga ƙungiyar, wasu an bautar da su ta dole.”
Ya bayyana cewa bayan Boko Haram ta rasa dabarunta, sai ta nemi wata sabuwar dabara.
“A baya, suna kama ƙauyuka suna tilasta wa maza shiga ƙungiyar, kuma suna kashe waɗanda suka ƙi amincewa,” in ji shi.
Ya ce sun koyi dabarar yi wa mata ciki da bautar da mata don haifar musu yara da za su taso a matsayin mayaƙa.
“Bayan wata huɗu da haihuwa, suna sake yi wa mata ciki,” in ji Musa.
“Wannan shi ne sabon salonsu na haifar sabbin mayaƙa.”
Ya jaddada cewa waɗannan yaran da aka haifa a cikin yanayin tashin hankali ba za su taso da tausayi ba.
“Wannan ne ya sa muke farin cikin cewa yara sama da 60,000 sun miƙa wuya,” a cewarsa.