‘Yadda Boko Haram suka yi awa 4 suna ta’asa a Garkida duk da sanar da sojoji’
A ranar Juma’ar da ta gabata ce da misalin karfe 6:00 zuwa 7:00 na yamma ’yan Boko Haram suka kai hari garin Garkida da ke Karamar Hukumar Gombi a Jihar Adamawa. Mazauna garin sun ce rashin kai dauki daga jami’an tsaro a kan lokaci ne ya sa Boko Haram din suka sheke ayarsu wajen yi […]
Wani waje da Boko Haram suka kona a Garkida
A ranar Juma’ar da ta gabata ce da misalin karfe 6:00 zuwa 7:00 na yamma ’yan Boko Haram suka kai hari garin Garkida da ke Karamar Hukumar Gombi a Jihar Adamawa.
Mazauna garin sun ce rashin kai dauki daga jami’an tsaro a kan lokaci ne ya sa Boko Haram din suka sheke ayarsu wajen yi musu barna da sace musu kayan abinci da magunguna, inda suka ce ’yan ta’addan sun dauki kusan awa biyar suna kone-kone ba tare da an kai wa garin dauki ba.
Aminiya ta samu labarin cewa sojoji biyu da ke aiki a garin sun rasa rayukansu a musayar wuta da ’yan Boko Haram din kasancewar ba su da yawa a lokacin da ’yan bindigar suka shiga Garkida.
Wadansu mutanen Garkida sun bayyana wa Aminiya yadda abubuwan suka auku
Mun samu labarin za su shigo tun karfe 4:00 na yamma
Wani mai suna Yusuf Gurunga wanda dan Garkida ne ya ce mutanen Garkida sun samu labarin ’yan Boko Haram za su kai hari tun karfe 4:00 na yamma.
Ya ce suna jin wannan jita-jitar ba su yi wata-wata ba suka sanar da jami’an tsaro. Ya ce a wannan lokacin matan zumunta suna coci suna harkokinsu kamar yadda suka saba.
Ya kara da cewa da jita-jitar shigowar ’yan Boko Haram din ta yi yawa, sai Fastonsu ya ce, su tafi gidajensu. “A wannan lokaci ne mutane suka shiga gudu da buya inda wadansu suka hau kan duwatsu domin tsira,” inji shi.
Yusuf ya ce tun karfe hudun aka sanar da jami’an tsaro game da shirin shigowarsu, amma ba su ga kowa ba illa wadansu sojoji hudu da suke zaune a inda suke aiki.
Ya kara da cewa da misalin karfe bakwai na yamma saura mintoci sai ga ’yan Boko Haram din sun shiga garinsu da motoci kirar Hilud guda bakwai.
“Suna shiga garin Garkida sai suka shiga harbe-harbe. A wannan lokaci ne wadannan sojoji hudu suka shiga harbe-harbe a tsakaninsu da ’yan Boko Haram har biyu suka rasa rayukansu,” inji shi.
Mun ga jiragen yaki na shawagi a sama a lokacin
Yusuf Gurunga ya ce a lokacin da ’yan Boko Haram ke cin karensu ba babbaka, sai suka ga jiragen sojojin sama suna ta shawagi a kansu. “Kamar yadda muka fahimta sojojin sama ne domin ina ta yin waya da su, sai suka ce min ana jira ne su fita a bi bayansu inda za a kone su da bam idan sun nufi hanyarsu ta zuwa Chibok.
“Can kawai sai muka ga garin ya kama da wuta. A wannan lokaci ba mu sani ba ko coci ne aka kona ko kuma Asibiti. Can sai muka ga kamar ’yan Boko Haram din za su yi hanyar Biu kuma sai suka sake shigowa,” inji shi.
Ya ce koda ya yi waya da sojijin Adamawa da misalin karfe7:00 sai suka ce masa cewa sun wuce Gombi a hanyarsu ta zuwa Garkida.
Yusuf ya ce ba zai iya tabbatar da cewa ko sojojin sun samu isowa Garkida ko ba su samu damar isowa ba, “Wannan sai Allah.Boko Haram kuma suka gama cin karensu babu babbaka har na tsawon awa biyar suka fara shirin fita daga Garkida sai na sake yin waya da sojojin wadanda suka ce min idan sun fita za a jefa musu bama-bamai da a cewarsu jirginsu na dauke da bama-baman.
“Sai na fahimci cewa motocin da suke fita Garkida sun fi wadanda ’yan Boko Haram suka shigo da su. Wannan ya nuna min cewa sun tafi da wasu motocin da ba na su ba,” inji shi.
Ya ce “Duk da haka ba mu ga abin da sojoji suka yi ba a wannan lokaci ban da jiragensu biyu da suke shawagi a sama.”
Yusuf ya kuma ce abin tashin hankali da ya ba su mamaki shi ne sojojin kansu ba su san cewa wadansunsu sun mutu ba, sai da Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya ziyarci Garkida, shi ne yaran unguwa suke nuna musu gawar ’yan uwansu da suka rasu.

“A wannan lokaci ne sojojin suka fahimci cewa akwai ’yan uwansu da suk mutu sakamakon harbe-harben,” inji shi.
Yusuf ya ce yana ganin kamar ana son a kori kabilun da ke cikin garin Garkida ne domin inda Boko Haram suka kona kamar sun zaba ne. “Domin sun kone gidajen manyanmu ciki har da gidan Janar Tarfa da Kanar Sawa da coci uku da wajen adanar abinci da wasu gidaje da kuma kayan aiki na makarantu da motocinmu na kai mutane asibiti da ofishin kamfanin lantarki da asibiti da ofishin waya da kuma turken wayar sadarwa.
“Ganin yadda suka kai hare-harensu wuraren ne ya sa muke ganin kamar sun zaba wurin Kiristoci ne kawai,” inji shi.
Ya ce ’yan Boko Haram ba su je da niyyar kashe mutane ba domin ban da sojoji biyun da suka rasa rayukansu, babu wanda aka kashe.
“Garkida gari ne da mutanensa ke son baki wannan shi ne karonsu na hudu da suke shiga garin Garkida amma ba su taba irin wannan ba. Abin takaici a nan shi ne muna zaune da kowa lafiya a garinmu babu wani bambanci har muna alfaharin cewa ’yan Boko Haram ba su taba yi mana barna ba a duk shigowarsu,” inji shi.
Garin Garkida mai nisan kimanin kilomita 167 daga Yola, Babban Birnin Jihar Adamawa, yana kan hanyar zuwa Chibok ne a Jihar Borno wanda daga garin za a iya shiga har cikin dajin Sambisa.
Sun sace magunguna a asibiti da shaguna
Yusuf ya ce yana ganin abinci da magunguna ne suka sa ’yan Boko Haram suka ziyarce su domin da suka zo asibitin, ba su taba inda marasa lafiya suke ba sai dai inda ake ajiye magunguna da kuma kayan gwaje-gwajen jini da sauransu.
Bayan nan duk wani shagon magani sun bi sun kwashe magungunan cikinsa sannan suka kona shagunan.
Ya bayyana cewa ’yan Boko Haram din sun tafi da wani malamin makaranta daya.
Babu hadin kai a tsakanin sojin sama da na kasa
Yusuf Gurunga ya ce a fahimtarsa babu hadin kaia tsakanin sojojin kasa da na sama wanda hakan ya sanya suka gagara cin galaba a kan ’yan Boko Haram din. Ya ce irin yadda shi da kansa ya rika magana da sojin sama amma har Boko Haram suka gama ta’asarsu suka fice daga garin ba tare da kai musu hari ba, yana nuna babu hadin kai a tsakanin sojin sama da na kasa.
Wani dan banga, Abdul Yusuf ya ce bindigodin da ’yan Boko Haram ke dauke da su sun fi na sojoji don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar da tarayya su samar da bindigogi masu inganci ga jami’an tsaro.
Dalilin da ba mu kai musu hari ta sama ba – Sojoji
Wani babban jami’in soji wanda ya sanar da jaridar The Cable aukuwar harin, ya ce sojojin sama sun kasa bambance ’yan ta’addar Boko Haram ne da mutanen gari shi ya sa ba su kai hari da jiragen sama ba. Ya ce sojojin kasa kuma da ke yankin ba su da kayan aiki. Ya ce motar yaki daya kacal suke da ita su kuma mayakan Boko Haram sun fi su yawa.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Birged na 23 da ke Yola da ke aiki a karkashin shirin “Operation Lafiya Dole” a Jihar Adamawa, Manjo Hamza Sani game da korafin da mutanen Garkida suka yi cewa har jami’ansu ma da aka kashe ba su da masaniya a kai, sai ya ce wannan ba gaskiya ba ce. Ya ce bayan harin sun fitar da sanarwa ga ’yan jarida inda suka nuna cewa jami’insu ya rasa ransa sannan daya ya samu rauni.
Ya kara da cewa sun iso a lokacin da ake harbe-harben inda suka yi luguden wuta a tsakaninsu da ’yan
Boko Haram, wanda hakan ne ma ya sa jami’insu daya ya rasu, sannan wanda ya ji rauni yana samun kula a asibiti.
Birgediya Janar Sani Gambo Mohammed wanda shi ne Kwamandan Birged na 23 da ke Yola ya jinjina wa sojoji game da kokarin da suka yi sannan ya kirayi jama’a su cigaba da sanar da su idan akwai kishin-kishin shigowar kowane dan ta’adda.
Za a kara tura jami’an tsaro – Fintiri
Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Fintiri wanda ya ziyarci Garkida tare da bada tallafin Naira miliyan hudu ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu, ya dauki alkawarin kara tura jami’an tsaro zuwa yankin.