Yadda Boko Haram ta kashe mutane 29 a Adamawa
Basaraken yankin, Aggrey Ali, ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun ɗauki awanni suna kashe-kashe da ƙone-ƙone, yana mai roƙon a turo ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin
Mutane 29 sun mutu bayan wani ƙazamin hari da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka kai a ƙauyen Sabon-Gari da ke Gundumar Guyaku a Ƙaramar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Wani mazaunin yankin mai suna Nimfas Bala, ya shaida wa wakilinmu cewa a ranar Lahadi ne maharan suka kutsa ƙauyen da misalin 5 na yamma a yayin da al’ummar Yankin suke tsaka da kallon gasar ƙwallon ƙafa da aka shirya a ƙauyen.
Nimfas Bala ya ce da zuwan maharan a kan babura ke da wuya, suka buɗe wuta, lamarin da ya tilasta wa ’yan wasa da ’yan kallon tserewa daga filin ƙwallon domin neman mafaka.
Ya bayyana cewa maharan sun raba kansu gida biyu, inda suka yi wa ƙauyen, suna harbun wanda suka yi arba da shi.
- Tuhumar da Malami yake fuskanta reshe ne ya juye da mujiya — Sowore
- NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji
“Ni da kaina na ƙirga gawarwakin mutane 29, baya ga wasu da dama da suka tsere waɗanda har yanzu ba a gan su ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa, ’yan ta’addan sun kuma coci, inda suka ƙone kayan kiɗa da kujerun roba da ke ciki.
Nimfas ya kara da cewa ’yan ta’addan sun kuma ƙona babura 42 da aka tsere aka bari a filin ƙwallon, sa’annan suka farga da shagunan jama’a suka kwashi kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi.
Ya ce daga bisani an hangi ’yan ta’addan suna shiga yankin Dajin Sambisa, da kayan da suka sace.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa wurin da abin ya faru a ranar Litinin, inda ya bayyana takaicinsa kan kisan gillan, wanda aya ce ba abin da za a lamunta ba ne.
Ya jaddada haɗin gwiwar gwamnatin jihar da hukumomin tsaro domin hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Basaraken yankin, Aggrey Ali, ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun ɗauki awanni suna kashe-kashe da ƙone-ƙone, yana mai roƙon a turo ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
Ƙaramar Hukumar Gombi da ke maƙwabtaka da Dajin Sambisa, na ga,a da barazanar ’yan ta’adda saboda yanayin yankin, wanda ’yan ta’adda suka amfani da shi.
Kafar yaɗa labarai ta Al-Jazeera ta ruwaito kungiyar ISIL, wadda Boko Haram ta yi wa mubaya’a ta yi iƙirarin kai harin, ta wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram.