Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa
Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa.
Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa.
Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa.
“Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe.
“Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi.
- Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa
Ya ce ’yan sanda tare da sauran jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kare yankin daga duk wata matsalar tsaro tare da yin kira ga jama’ar yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi.
Sai dai wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa al’ummar kauyukan biyu na fuskantar hare-haren ta’addanci ta hanyar bama-bamai da aka dasa da daddare a kan hanyoyin karkara.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kara tura jami’ansu da makamai a yankin, domin hare-haren ta’addanci a Damboa da Chibok da kuma gefen dajin Sambisa na zama abin damuwa.