Yadda bom ya halaka mutum 20 a tashar motar Dukku

Da safiyar ranar Litinin da ta gabata aka samu tashin wani bam a cikin wata mora kirar Sharon a tashar motar zuwa Dukku, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin ashirin, inda goma sha takwas suka samu munanan raunuka.Wani Direba a tashar da lamarin ya auku a kan idonsa, Ibrahim Manu, ya shaida wa wakilinmu […]

Yadda bom ya halaka mutum 20 a tashar motar Dukku
Yadda bom ya halaka mutum 20 a tashar motar Dukku

Da safiyar ranar Litinin da ta gabata aka samu tashin wani bam a cikin wata mora kirar Sharon a tashar motar zuwa Dukku, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin ashirin, inda goma sha takwas suka samu munanan raunuka.
Wani Direba a tashar da lamarin ya auku a kan idonsa, Ibrahim Manu, ya shaida wa wakilinmu cewa wata mota ce kirar Sharon da take lodin zuwa garin Bajoga bom din ya tashi a cikinta, a daidai lokacin da ta riga ta kusa cika suna zaune a tasha suna harkokinsu da suka saba sai kawai suka ji wata kara mai karfi a kusa da su cikin wannan motar, duk wadanda ke cikin motar sun mutu.
Ya ce bayan fashewar bom din ne sai suka fara tattara sassan jikin mutanen, aka gaggauta kai su asibiti.
Da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ’yan sanda, DSP Fwaji Attaji, ya tabbatar da hakan, inda ya ce daga lokacin da suka sami labarin sun kai daukin gaggawa, inda suka kai wadanda suka rasa rayukansu da masu rauni asibiti. Ya tabbatar da cewa mutane goma sha tara ne suka rasa rayukansu.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista