Yadda budurwa ta tunbuke wa matashi harshe

A ranar Talata 3 ga watan Agustan nan ne wata matashiya ta datse harshen wani matashi da suke zaune a gida daya a Legas, wakilinmu ya bi diddigin yadda lamarin ya faru, inda ya zanta da mahaifiyar matashin, ga yadda zantawar ta kasance:  Aminiya: Hajiya za mu so ki gabatar da kanki? Hassana Ali: Sunana […]

Yadda budurwa ta tunbuke wa matashi harshe

A ranar Talata 3 ga watan Agustan nan ne wata matashiya ta datse harshen wani matashi da suke zaune a gida daya a Legas, wakilinmu ya bi diddigin yadda lamarin ya faru, inda ya zanta da mahaifiyar matashin, ga yadda zantawar ta kasance: 

Aminiya: Hajiya za mu so ki gabatar da kanki?

Hassana Ali: Sunana Hajiya Hassana Ali, mu mutanen garin Gulu ne da ke ƙaramar hukumar Rimin Gado a jihar Kano, a nan Legas aka haife ni, wato a gidan da wannan ibtila’i ya abku, mahaifi na ne ya gina gidan bayan da ya aurar damu, ni mijina Bakatsine ne, wato ubban ’ya’yana, kuma a nan Legas muke zaune tare da shi, to da lokaci ya yi mahaifi na ya ga yana buƙatar  ya koma Arewa, wato asalin garinmu a Kano garin Gulu, sai ya nuna ba ya so ya sayar da gidan, don haka ya buƙaci ni da maigidana mu komo gidan domin mu kula masa da shi, haka kuwa aka yi, shi ya sa ka gani ina zaune a nan da ni da ’ya’yana, domin a yanzu mijina ya rasu.

Aminiya: Ko za ki yi mana ƙarin haske a kan yadda wata mace ta cire wa ɗanki harshe?

Hassana Ali: Ita dai  yarinyar da ta yi mana wannan aika-aikar mijin yayarta ne yake haya a gidanmu, a lokacin da suka zo gidan  ba ta tare da su, kimanin shekaru biyu ke nan da suka shuɗe, bayan da yayarta ta haihu sai ta zo ta zauna tare da su, to a wannan lokacin ne suka shaƙu da ɗana Babangida, domin mutum ne da ba shi da ƙyuya, tana aikensa wurare da dama kusa da nesa, a wasu lokutan ma sukan fita tare, to akwai lokacin da suka samu saɓani ta dinga zaginsa, da na lura da haka sai na ja kunnensa na ce ya fita daga harkarta, yau kimanin wata shida ke nan, to sai a ’yan kwanakin nan ne na ga kamar suna so su dawo da dagantakarsu ta baya, nan na kuma ja masa kunne na nuna masa ɓacin raina, sai ya kuma fita daga harkar ta, to a daren da lamarin zai faru da misalin ƙarfe 11:30 na dare ya fita ya yi fitsari, sai yarinyar mai suna Biyodun ta saɗaɗo ta bi shi banɗaki inda ta shaƙe masa wuya ta cire masa harshe ta kuma kulle ƙofar banɗakin, mijin yayarta ne ya farkar da mu daga barci bayan da ya ankara da lamarin, shi ma ya fita ya yi fitsari a daren ne sai ya ji alamar kamar mutum biyu ne a banɗakin, da ya yi magana sai ta amsa masa cewa ita ce, ya ce ke da waye? Ta ce ita kaɗai ce, da ya  ga alamar jini na kwaranyowa sai ya yi wuf ya ɓalle ƙofar, nan take ya tarar da Babngida a kwance cikin jinni, nan ya yi ƙururuwa ya tashe mu daga barci, ya ce mu zo mu ga abin da Biyodun ta aikata, nan yac e a riƙe ta kar ta gudu ta sanya shi cikin wahala, nan take ya kira jami’an ‘yan sanda suka tafi da ita. Kururuwarsa ta sanya maƙwabta suka taru, inda suka fara dukanta, nan take na hana a dake ta, aka miƙata ga hukuma.

Aminiya: Yaya aka yi da harshen da ta yanke masa?

Hassana Ali: Da farko ba mu san ma ta yanke masa harshe ba, domin a ɗimauce muka farka, sai da ya buɗe bakinsa ne muka lura da hakan, da wani ya haska wajen da fitila sai muka ga harshen a ƙasa tare da sarkar wuyarta wacce ke jiƙe a cikin jinni, mu ba mu san mai ya kai sarƙar wajen ba, don haka ne muke da tabbacin cewa ta cire masa harshen ne da zummar yin tsafi da shi, domin a lokacin da aka riske ta an ga tana zubar da jini daga bakinta, tana cewa sai ta kashe ɗan mutum a yau, kuma da mijin yayar nata bai ankara ba, ai ta kulle shi a banɗakin ne, da sai dai a wayi gari a ga gawarsa b atare da sanin wanda ya aikata masa ba.

Aminiya: Wane mataki kuka ɗauka bayan kun gano harshen nasa a ƙasa?

Hassana Ali: Mun yi hanzari muka garzaya da shi asibiti a cikin daren, inda har sau 3 ana ƙin karɓarsa saboda raunin da ta yi masa ya yi muni, domin harshen kacokan ta tunɓuƙe masa, tun daga  tushensa da ke baki, sai da muka kai shi asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas da ke Ikeja sannan ne aka ƙarɓe shi, bayan an je masu da harshen sai likitoci suka ce ba zai yiwu a yi dashen harshen ba domin ya riga ya yi tauri, suka ce a je a binne shi, ɗan uwansa ya yi niyyar binnewa sai ya ji tsoron kada yarinyar ta zagaya ta haƙe su yi tsafi da shi, sai ya jefa harshen a masai. Har zuwa yanzu Babangida  ba ya iya magana, ba kuma ya iya cin komai, sai dai likitocin sun shaida mana cewa za a c igaba da gasa bakinsa da ruwan gishiri mai ɗumi, kuma sun shaida mana cewa tun da yaron yana da ƙarancin shekaru, domin bai wuce shekara 23 ba, harshen zai iya tohowa, ko da kuwa ɗan kaɗan ne, a cikin shekaru 2, kuma zai iya yin magana, ko da kowa ba daidai da irin tamu maganar ba.

Aminiya: To yanzu mai kuke fatan ganin an yi a kan wannan lamari?

Hassanat Ali: Fatanmu shi ne a bi wa wannan  yaro haƙƙinsa, a hukunta Biyodun daidai da wannan laifi da ta aikata masa, domin a yanzu ta cuce shi, ta lahanta masa rayuwa, akwai wani ɗan uwansa da farko yake cewa wai mu yi irin tamu ta Hausawa, mu rungumi ƙaddara a sulhunta, niko na ce mu Hausawa mu ne masu tawakkali, amma ba zai yiwu wata ta zo ta lahanta rayuwar ɗana, ta tunɓuke masa harshe, ta nakasa shi, bayan na haife shi da ƙoshin lafiyarsa, sannan a ce a zo a yi sulhu, a gaskiya a wannan karon sai inda ƙarfina ya ƙare, zan yi iya yina, da Allah na dogara, Shi ne ƙarfinmu, domin mu talakawa ne, ba mu da wani ƙarfi, amma a haka za mu dage har Allah Ya ba mu sa’a mu bi masa haƙƙinsa.

 Kuma wani abin takaicin shi ne yadda jami’an ’yan sandan da aka kai maganar wajensu suke neman yin ƙafar-ungulu da maganar, domin ba don taimakon Allah ba, da yanzu sun ba da bailinta, sun sake ta. Domin na samu labarin jami’n ɗan sandan da ke binciken lamarin ya karɓi Naira dubu 30 a wajen ’yan uwar yarinyar, suna jiran a ba su cikon Naira dubu 20 ne su sake ta, nan na garzaya ofishin ’yan sandan da ke Ogudu, inda da kyar suka bari na shiga, bayan na tuɓure masu nace ɗana aka tunɓuke wa harshe, na shiga na ce a fito mani da yarinyar in ganta. Sai na ga har sun sauya mata kayan jikinta, a maimakon wanda ta yi aika-aikar da su, waɗanda suka yi caɓa-caɓa da jini, hakan ya san na ce masu ban yarda a sake ta ba, muddin kuwa za su sake ta ne sai dai su ba ni adda ni ma in datse mata nata harshen, kamar yadda ta yi wa ɗana. Da DPO ‘yan sandan ya ji hayaniyarmu ne, sai ya ƙaraso yake nuna alamun bai ma san da maganar ba, bayan an yi kwana biyu ana tsare da ita a ofishin da yake wa jagoranci, nan take yace ai wannan maganar babbar magana ce ta fi ƙarfin a ba da beli don haka za su tura su kotu. 

Sai dai abin ta kaicin shi ne, jami’in ɗan sandan da ke binciken lamarin ya sauya ainihin abin da ya faru, inda ya ce yaron ya je ya sunbace ta ne sai suka kaure da faɗa ta tunɓuke masa harshe, bayan kuwa lamarin ba haka yake ba, ɗan nawa a rubuce ya ba su bayaninsa, domin ba ya iya yin magana. Sai suka sauya kalmar da ya rubuta ta ‘fiss’ da yake nufin ya je ya yi fistari ne ta farmasa, suka canza kalmar zuwa ‘kiss,’ wato ya je ya sunbace ta. Don haka ina miƙa kukana ga hukuma da ƙungiyoyin kare haƙkin ɗan Adam da lauyoyi da su taimaka mana a karɓar wa wannan yaro ‘yancinsa, domin jami’an ‘yan sanda na neman yi mana sakiyar da ba ruwa, domin sunga mu talakawa ne ba mu da ƙarfi. Yaron ya gama sakandare, muna kan shirin tura shi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya  domin cigaba da karatunsa, wannan yarinya tayi masa aika-aika, a ranar litinin mai zuwa muka shirya zai je Zariya sai ga shi ta katse mana hanzari. Don haka muna miƙa ƙoƙon bararmu ga duk wanda zai iya taimakonmu a kan wannan lamari, a yanzu mutanen ungawarmu ne suka nema mana lauya, domin mu ba mu da ƙarfin yin haka.

Duk ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin zantawa da yayar yarinyar ko mijinta, lamarin ya ci tura, domin tuni suka ƙaurace wa gidan, tun bayan faruwar lamarin, don gudun kada ’yan unguwar da suka fusata su kai masu farmaki.

’Yan sanda na neman yi mana kafar-ungulu –  Ɗan uwan yaron

Wakilinmu ya ziyarci asibintin da Babangida yake jinya inda ya same shi ba ya iya magana, sai dai yayansa mai suna Yahaya Sulaiman, ya shida wa Aminiya cewa mijin yayar yarinyar mai suna Olumba  abokinsa ne, suna da kyakaywar alaƙa da shi, ya ce don haka da lamarin ya faru, duk da shi ba a gidan yake ba,nan take ya kira shi a waya ya shaida masa, domin shi ne farkon wanda ya shaida faruwar lamarin. Ya ce mijin yayar yarinyar  ya ba su haɗin kai da farko, har sai da ta kasance ’yan uwan yarinyar sun fara sa-in-sa da shi.  “Na kaɗu ƙwarai ganin yadda jami’n ɗan sandan da ke bincikar lamarin ya sauya haƙiƙanin yadda lamarin ya faru a takardar da suka shigar kotu, sun ɓatar da ainihin takardar ta Babangida ya rubuta jawabinsa, da kuma wanda mijin yayar yarinyar ya rubuta tun da farko, ni na riƙe ƙanin nawa muka je kotu a ranar alhamis ɗin da ta gabata, sai dai a irin yanayin da alkalin ta ga yaron ya sanya ba ta saurari ƙarar ba, inda ta ba da umarnin a mayar da shi asibiti a duba lafiyar sa, domin yana yawan tara yawu a bakinsa, nan take ta ba  da umarnin a kai yarin yar da tayi masa aika-aikar gidan kaso, har sai ranar da za a sake sauraron shari’ar,” inji shi.

Shi ma yayan yaron  ya haƙikance cewa yarinyar ta cire harshen ɗan uwansa ne da nufin yin tsafi da shi, ya ce likitocin da suke duba lafiyarsa su biyar, dukansu sun ce ba su taɓa cin karo da makamancin abin da ya faru da ƙaninsa ba, sannan babu yadda za a yi a ce da baki ta tunɓuƙe harshen, ganin yadda ta cire fiye da rabinsa tun daga tushensa. Ya ce  kafin faruwar lamarin, da kimanin kwanaki 3, an ji yarinyar tana yawan ambaton cewa za ta fara hawan babbar mota, za kuma ta kama hayar gida na alfarma.

A ’yan kwanakin nan dai ana yawan samun matasa a jihohin Legas da Ogun  da ke shiga ƙungiyoyin asiri domin neman abin duniya da yin kuɗi a dare ɗaya, ƙungiyar asiri da tafi fice a wannan yan ki ita ce ta Baddu, wace rundunar ‘yan sandan jihohin ta sanya ƙafar wando ɗaya da ita.