Yadda budurwa ta watsa wa saurayi guba saboda ya ki soyayyarta

Wata budurwa ta watsa wa wani saurayi guba a fuska saboda ya ki amincewa da ita a matsayin masoyiyarsa. Saurayin mai suna Mahmudul Hasan Maruf dan shekara 17, yanzu haka yana kwance a asibiti a birnin Dhaka na Bangladesh inda likitoci suke kokarin ceto rayuwarsa. Rahotanni sun ce budurwar wadda ta kai kimanin shekara 16 […]

Yadda budurwa ta watsa wa saurayi guba saboda ya ki soyayyarta

Wata budurwa ta watsa wa wani saurayi guba a fuska saboda ya ki amincewa da ita a matsayin masoyiyarsa.

Saurayin mai suna Mahmudul Hasan Maruf dan shekara 17, yanzu haka yana kwance a asibiti a birnin Dhaka na Bangladesh inda likitoci suke kokarin ceto rayuwarsa.

Rahotanni sun ce budurwar wadda ta kai kimanin shekara 16 ta watsa masa gubar ce saboda soyayya, inda ta watsa masa gubar a fuska, kuma ya samu raunuka a sannan jikinsa. Kuma rahotannin sun ce ta tare Mahmudul ne bayan ya dawo yawo da daddare.

Likitoci sun ce ya ji rauni da yawa da ba zai iya komawa yadda yake ba a da har abada domin dukanin fatar fuskarsa ta fita.