Yadda Budurwa ta yi karyar mutuwa a Facebook don ta guje wa danginta

Ana zargin wata  budurwa da shirya mutuwar  karya a kafar sada zumunta ta facebook domin ta kaucewa matsin da mahaifiyarta da ‘yan uwanta ke yi mata. Budurwar mai suna Margaret Adiya ‘yar shekara 19, tace tayi karyar mutuwa ne domin ta gujewa mahaifiyar ta da sauran ‘yan uwanta wadanda ke matsa mata da aike suna […]

Yadda Budurwa ta yi karyar mutuwa a Facebook don ta guje wa danginta

Margaret Adiya Ikumu, budurwar da ake zargi da karyar mutuwa a facebook

Ana zargin wata  budurwa da shirya mutuwar  karya a kafar sada zumunta ta facebook domin ta kaucewa matsin da mahaifiyarta da ‘yan uwanta ke yi mata.

Budurwar mai suna Margaret Adiya ‘yar shekara 19, tace tayi karyar mutuwa ne domin ta gujewa mahaifiyar ta da sauran ‘yan uwanta wadanda ke matsa mata da aike suna bukatar kudi daga gare ta.

Magret tace tayi hakan ne domin ta huta da yawan bukatar kudin da ‘yan uwan nata ke yi a wajen ta.

Mai magana da yawun Hukumar  ‘yan sandan jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan uwan budurwar ne suka aike wa Hukumar takardar koke daga karamar hukumar Oju a jihar Benue , takardar da Toni Iji ya sanya wa hannu.

Yace a takardar koken sun shaida cewa sun sami wani bayani da ke cewa yar su Magret Adiya ta rasu ba da jimawa ba,  kuma wasu kawayenta biyu, Marvelous  Mary da Nneka Buddy  sun binne ta a yankin Ajah a Legas.

‘Yan uwan budurwar sun kara da cewa  sun tuntubi kawayenta wadanda suka tabbatar masu ta mutu, kuma ita ta umarce su da su binne ta a boye ba tare da sun sanar wa ‘yan uwanta ba, inda suka tura masu hoton akwatin gawa suka ce a ciki suka birne ta, ‘yan uwan nata kuma sun yi magana da wani matashi ta wayar salula wanda shima  tabbatar masu ta mutu kuma yace shi ne saurayin ta.

‘Yan sanda sun gano ta

DSP Bala Elkana yace daga bisani jami’an ‘yan sanda sun gano budurwar  a gidan da take yin aikatau a unguwar Ajah a Legas, ” Uwar dakinta ne ta mika ta ga jami’anmu da ke aiki a yankin Ajah bayan da ta lura ta yi karyar mutuwa a facebook.

“A jawabin da ta yiwa jami’anmu, budurwar ta shaida cewa ta bude sabon shafi ne a facebook domin ta sanar da mutuwar ta.

‘Tace tayi haka ne domin ta guje wa mahaifiyarta da ‘yan uwanta da suke matsa mata da aike suna bukatar ta tura masu kudi.

“Ta kuma shaida cewa tana ciki da mahaifiyarta da kannan babanta wadanda suka gaza biya mata kudin makaranta tun bayan mutuwar mahaifinta, lamarin da ya sanya ta zuwa Legas domin ta yi aikatau ta tara kudi ta koma makaranta” in ji DSP Bala Elkana.

Ta bude Asusun facebook da hoton wata

Bala Elkana yace wacce ake zargin ta bude sabon asusun facebook ne da hoton ‘yar uwar dakinta, Dr Dr Nimechi Ugorji, ba tare da sanin uwar dakin ba, ” da kawunta ya ga sanarwar a facebook sai ya dauki  hoton da ta sanya a asusun ya bukaci duk wanda ya san mai hoton ya sanarwa ‘yan sanda, muna kuma cigaba da bincike akan lamarin” in ji shi.