Yadda Buhari da Sheikh dahiru Bauchi suka tsallake harin bam 1
Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran babbar jam’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya ce shi aka yi kokarin kashewa a harin bam din da aka kai a Kaduna a shekaranjiya Laraba, inda aka halaka fiye da mutum 50 a Kawo tare da raunata jami’an tsaronsa uku bayan lalata motar da yake ciki da kone […]

Tsohon Shugaban kasa kuma jagoran babbar jam’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya ce shi aka yi kokarin kashewa a harin bam din da aka kai a Kaduna a shekaranjiya Laraba, inda aka halaka fiye da mutum 50 a Kawo tare da raunata jami’an tsaronsa uku bayan lalata motar da yake ciki da kone sauran motoci uku da ke cikin tawagarsa.
Wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Janar Buhari ya ce: “Harin bam din Titin Ali Akilu da Kawo Kaduna da ya auku da misalin karfe 2:30 na rana ya rutsa da ni a kan hanyata ta zuwa Daura.”
Ya kara da cewa: “Wannan abin takaici a fili yake yunkurin halaka ne, ya zo ne a wata mota a guje da ta rika yunkurin shan gaban motar jami’an tsarona a lokuta da dama amma ’yan rakiyana suka hana su wucewa. Muna isa yankin kasuwar Kawo sai suka yi amfani da daga kafar da muka yi suka yi yunkurin kara motarsu a jikin motata kuma nan take suka tayar da bam din wanda ya lalata dukkan motoci uku da ke cikin tawagarmu.”
Janar Buhari ya ce “Abin takaici shi ne lokacin da na fito daga motata, nag a gawarwakin mutane warwatse. Mutane ne da ba su san hawa ko sauka ba da suke kasuwanci aka hallaka su. Na gode Allah kan rahamarSa, na fito ba tare da rauni ba, amma jami’an tsarina uku sun samu kananan raunuka – kuma an yi masu magani a asibiti an sallame su.”
Harin da aka kai kan Buhari shi ne na biyu a shekaranjiya Laraba bayan da aka kai irinsa ga fitattcen Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi a kan titin Alkali Road da ke Kaduna, inda aka halaka fiye da mutum 35.
Wani mukarrabin Buhari ya shaida wa Aminiya cewa, cikin motoci uku da ke cikin tawagar, wadda ke dauke da Buhari ce harin ya fi shafa.
Ya ce baya ga harin bam din, an bude wa motocin da ke cikin tawagar wuta da bindigogi musamman motar Buhari
“Wadda alama ce ta a tabbata an kashe Janar din koda ya kubuta daga harin bam din,” inji shi.
Ya ce, harin ya auku ne a lokacin da tawagar Buhari ke tafiya a kan hanyar Kawo a kan hanyarsa ta zuwa mahaifarsa Daura a Jihar Katsina.
Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross sun ce fiye da mutum 50 ne suka rasu a harin na Kawo
Shi ma Sheikh dahiru Bauchi ya tsallake harin bam din da ba a san ko su wane ne suka kai masa ba.
Aminiya ta samu labarin cewa harin farko wani matashi ne dauke da bam a jikinsa ya tunkari motar Sheikh dahiru Bauchi a daidai lokacin da yake barin Dandalin Multala Skuare inda ya je rufe Tafsirin watan Ramadan na bana.
Akalla mutum 32 ne suka rasu a harin na titin Alkali a daidai lokacin da motocin Shehin ke tafiya gida. Sai dai ’yan sanda sun ce mutum 25 suka rasu yayin da14 suka samu munanan raunuka.
Shi ma Shehin ya shaida wa kafar labarai ta Sahara Repoters cewa tabbas shi aka nufa da harin bam din na titin Alkali, to amma sakamakon addu’a sai Allah Ya kare shi. Shehin ya ce, “Ga Allah muka dogara, saboda haka babu abin da zai same mu. Yanzu haka da nake magana da kai ina kan hanyata ce ta zuwa Umara”
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna wanda ya tabbatar da aukuwar hare-haren biyu ya ki ya fadin sunan Janar Buhari a matsayin wanda aka kai wa harin Kawo sai dai ya ce wani babban mutum ne.
“Bam din farko Sheikh dahiru Bauchi aka kai wa hari amma dai bai samu rauni ba. Sai dai akalla mutum 25 sun rasu kuma 14 sun samu munanan raunuka,” inji shi.
Ana cikin kokarin kwashe gawarwakin mutanen da bam din titin Alkali ya rutsa da su ne sai ga labarin cewa wani bam din ya tashi a Kawo.
“Wani babban mutum ne aka kai wa harin kuma mutum uku ne muka samu labarin sun kai masa hari. Amma dai ya tsira babu ko rauni,” inji shi.
Sai dai sakamakon boren da matasa suka yi na jifar jami’an tsaro da duwatsu an tarwatsa su da borkonon tsohuwa.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafar dokar hana fita daga gida na awa 24 domin maido da doka da oda.
Wata sanar dauke da sa kakakin Gwamnan Ahmed Maiyaki ta bayyana harin a matsayin halin miyagu.