Yadda Buhari ya gana da Daliban Kankara a cikin hotuna
Hotunan ganawar Buhari da dalibai 344 na makarantar GSSS Kankara da aka ceto
Shugaba Buhari yana yi wa Daliban Kankara jawabi a Katsina
Ga hotunan ganawar Shugaban Kasa Buhari da daliban Makarantar GSSS Kankara da ‘yan bindiga suka sako.
Buhari ya gana da su ne Katsina, ‘yan sa’o’i bayan an dawo da su Katsina daga Jihar Zamfara inda ‘yan bindiga suka damka su ga wakilan gwamnati.
Dalibai 344 da aka sako suna sauraron jawabin Shugaba Buhari ranar Juma’a, 18 ga Disamba, 2020Shugaba Buhari a lokacinda yake yi wa daliban jawabi a Katsina, ranar Juma’a, 18 ga Disamba, 2020Buhari yana jinjinya wa jami’an tsaro da hukumomin da suka sanya baki aka sako daliban na GSSS Kankara da aka yi garkuwa da suBuhari na jawabi a lokacin taron tarbar daliban da aka cetoDaliban da ake ceto da jami’an tsaro da manyan jami’an gwamnati suna sauraron jawabin Shugaba Buhari