Yadda Buhari ya zakulo sabon Sufeto Janar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Kpotun Idris a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya.Wata majiya ta shaida wa Aminiya a ranar Talata da daddare cewa an zabo sabon Sufeto Janar na ’Yan sandan ne daga cikin manyan jami’an ’yan sandan da suka cancanci rike […]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Kpotun Idris a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya a ranar Talata da daddare cewa an zabo sabon Sufeto Janar na ’Yan sandan ne daga cikin manyan jami’an ’yan sandan da suka cancanci rike kujerar saboda shi ne ya tsallake binciken da Fadar Shugaban kasa ta yi a asirce a kan gaskiya da rikon amanarsa.
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa an yi bincike sosai kan gaskiya da rikon amana da kuma tarihin manyan ’yan sandan kuma aka nazarci irin dukiyar da suka mallaka.
“Bayan an gama binciken a asirce, an gano yawancin manyan ‘yan sandan suna da makudan kudi a asusun ajiyarsu na bankuna. Amma shi, baya ga gidan da ya saya a jiharsa ta Neja lokacin da yake Babban Sufurtandan ’Yan sanda (CSP)da kuma na bayan nan da ya mallaka ta hanyar mazauni-ya-saya a Abuja, ba ya da komai,” inji majiyar.
Idris, shi ne na uku a can kasa a jerin sunayen Mataimakan Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, karamin cikinsu shi ne Musa Katsina, sai na sama da shi Shu’aibu Lawal sai kuma shi Idris. Dukkan sauran Mataimakan Sufeto Janar din suna sama da sabon Mukaddashin Sufeto Janar din.
“Wannan bai hada da sababbin Mataimakan Sufeto Janar da tsohon Sufeto Janar Solomon Arase ya yi wa karin girma a makon jiya kafin ya yi murabus ba. Idris ya kafa tarihi mai kyau a aikin dan sanda wanda hakan ne ya sa aka nada shi Mataimakin sufeto janar na ’Yan sandan shiyyar Kano a watan Fabrairun bara, duk da cewa shi ne karamin mataimakan a wancan lokaci.”
Idris Kpotun ya maye gurbin Solomon Arase ne wanda ya yi ritaya a ranar Litinin bayan ya shafe shekara 35 yana aiki kuma ya cika shekara 60 a duniya.
Zabo Idris Ibrahim a matsayin sabon Sufeto Janar ya ba mutane da yawa mamaki ciki har da masu nazarin harkokin da masu sharhi mamaki, domin a tunaninsu sabon Sufeto Janar din zai fito ne daga cikin Na’iban Sufeto (DIG) wadanda su ne manyan mahukunta masu gudanar da aikin dan sanda.