Yadda canjin shekar ’yan siyasar Bauchi za ta iya sauya akalar siyasar jihar
Tun kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya je kaddamar da yakin neman zabe a Jihar Bauchi, ’yan siyasa da masu fashin bakin siyasa suke a ta bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da yanayin da ’yan siyasa suka samu kansu, musamman ma yadda suke ta canja sheka a jihar. Fitattun wadanda aka bayar da sanarwar sun canja […]
Shugaba Buhari da jiga-jigan Jam’iyyar APC a yayin qaddamar da kamfe xinsa a Jihar Bauchi a Asabar da ta gabata
Tun kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya je kaddamar da yakin neman zabe a Jihar Bauchi, ’yan siyasa da masu fashin bakin siyasa suke a ta bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da yanayin da ’yan siyasa suka samu kansu, musamman ma yadda suke ta canja sheka a jihar.
Fitattun wadanda aka bayar da sanarwar sun canja sheka zuwa Jam’iyyar APC su 18, da ba dukansu suka halarci filin wasa na Sa Abubakar Tafawa Balewa ba, inda aka kaddamar da yakin neman zaben, sun hada da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Mu’azu da tsohon Gwamnan Jihar, Malam Isa Yuguda da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa shiyyar Arewa kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Babayo Garba Gamawa da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Abdulmalik Mahmud da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed da sauran gogaggun ’yan siyasar da aka ambaci sunayensu cewa sun koma Jam’iyyar APC.
Sai dai yayin da wadansu ke ganin sauya shekar za ta sauya tafiyar siyasar jihar, wadansu na ganin shigarsu Jam’iyyar APC ba za ta sauya komai ba illa dai za ta nuna kamar an farfado da zumunci kuma an samu hadin kan al’ummar jihar ce.
Masanin Kimiyyar Siyasa kuma malami a Kwalejin Koyon Sana’o’i ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi, Malam Yusuf Abdullahi ya ce a gaskiya komawar da jiga-jigan ’yan siyasa suka yi ya sanyaya gwiwar ’yan takarar Gwamna a Jihar Bauchi, domin da suna watse ne, amma yanzu sun taru a waje guda za su hada karfinsu, kuma daga hannun dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC kumwa Gwamnan Jihar Mohammed Abubakar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi bisa la’akari da yadda irin wannan salo ya yi tasiri a baya, hakan na iya sa wadansu daga cikin masu zabe su karkata su bi abin da Shugaban Kasa ya ce.
Sai dai Malam Yusuf ya ce a kashin gaskiya sauya alkiblar siyasar Jihar Bauchi abu ne da ke hannun mafiya yawan wadanda za su jefa kuri’a.
Shi kuwa mai fashin baki kan siyasa El-Faruk Adamu Gado ya ce shigarsu cikin Jam’iyyar ba zai sauya komai ba, domin wadannan shugabanni ba su tare da mafi yawan jama’arsu kuma dukansu ’yan takara ne da suka sha kaye a baya, don haka kimar da suke da ita lokacin da suke gwamnati ba su da irin wannan kima a yanzu.
El-Faruk ya ce “A ganina haka da Gwamnan Bauchi ya yi ya farfado da tsohon zumunci, ya dinke Jihar Bauchi domin komawarsu na nuna cewa ya dauko kowane gefe a cikin siyasar Jihar Bauchi kuma zai iya tafiya da jama’ar jihar baki daya.
Wani mai goyon bayan Gwamna Muhammad Abubakar, Alhaji Danladi Osi-kwano ya ce komawarsu za ta iya sake fasalin siyasar jihar, domin dukansu shugabanni ne kuma masu jama’a da suka yi wa al’ummar jiha ayyukan alheri.
Ya ce in ka dauki Sanata Babayo Garba Gamawa, ya yi Mataimakin Gwamna, ya yi Sanata kuma ya taba zama Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar, yana da dangantaka da mutane da dama da kuma masoya da yawa a Arewacin Jihar.
Alhaji Danladi ya ce tsofaffin gwamnoni jihar Malam Isa Yuguda da Alhaji Ahmadu Mu’azu mutane ne masu hali nagari da kima a idon jama’a, don haka mutane za su ji maganarsu kuma wannan karin karfi ne ga tafiyar Gwamna Abdullahi Abubakar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Don haka shigarsu alheri ne, don za su yi yakin neman zabe ga Gwamna da Shugaba Buhari. “Ka ga yanzu koda a ce Gwamna zai zauna bai yi wani yakin neman zabe ba, wadannan mutane biyu, Mu’azu da Yuguda su za su kawo wa Jam’iyyar APC Jihar Bauchi,” inji shi.
Dan takarar Sanata a Bauchi ta Kudu, a Jam’iyyar NNPP, Alhaji Abubakar Billy Tafawa Balewa ya ce “Komawar wadannan shugabanni da daga hannun Gwamna da Shugaban Kasa Buhari ya yi, tamkar ya yi amai ne ya lashe, domin a baya suna neman ta kansu ne da wadanda suke kira barayi, kuma Shugaban Kasa na shelar a zabi cancanta ne, sai ga shi ya daga hannun wanda bai yi wa al’ummarsa komai ba,” inji shi.
Abubakar Billy ya ce komawarsu ba wani abu da zai sauya, jama’ar Jihar Bauchi kusan shekara hudu ke nan ake gasa musu aya a hannu.
Ya ce hukuncin baki daya yana hannun masu zabe ne da ke Jihar Bauchi kuma haka ba zai raunata tasirin jam’iyyarsu ba, ba zai kuma hana ’yan takararsu na Jam’iyyar NNPP yin nasara ba, don al’ummar Jihar Bauchi cancanta suke da niyyar zaba, ba daga hannu ko hudubar wadansu mutane ba. “Muna da kwarin gwiwa a bana za a yi adalci wajen ba jama’a damar su zabi wanda suke so, wannan shi ne dimokuradiyya,” inji shi.
Kakakin dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Maigari Muhammad Khanna ya ce “Komawar tsofaffin gwamnonin da mataimakansu da kuma wadansu ’yan siyasa ba za ta girgiza tafiyar dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP ba, kuma ba za ta cutar da Jam’iyyar PDP ba.”
Maigari ya ce “In ka lura, an yi wata irin shela ce amma daga cikin mutanen da aka ambaci sunansu su 18 cewa sun koma cikin APC daga PDP, ba gaskiya ba ne domin a cikinsu mutum biyu ne kawai za a ce suna kusa da Jam’iyyar PDP, sauran ba ’ya’yan PDP ba ne. Kuma da mamaki a ce dan siyasa ya bar jam’iyya; ai shi ne zai fada da bakinsa amma ba ya wajen kuma har Shugaban Kasa da kansa ya zo wajen, abin da mamaki.”
“Bari in yi maka dalla-dalla, ka ga Malam Isa Yuguda ba dan Jam’iyyar PDP ba ne, don ya dade da ficewa daga PDP har ma ya yi takara a Jamiyyar GPN. Don haka ba daga PDP ya koma APC ba, sai a bincika. Haka shi ma tsohon Gwamna Mu’azu, tunda suka fadi zabe ya sauka daga shugabancin Jam’iyyar PDP kuma ya ce ya fice daga cikinta, kuma ya bar kasar, yanzu haka ba ya kasar nan kuma bai halarci taron ba. Don haka sai mun ji daga bakinsa tukuna. Haka tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Yayale Ahmad, shi ma ba dan PDP ba ne, ba mu taba ganinsa cikin hidimar jam’iyyar ba kuma shi ma ba ya wajen sunansa kawai aka ambata,” inji shi.
Maigari ya ce, Sanata Babayo Gawama da Abdulmalik Mahmud su ne suke kusa da Jam’iyyar PDP. “Amma ka ga Babayo Gamawa, 24 kafin ya fice daga PDP, uwar jam’iyyar ta kasa ta dakatar da shi, ta ce ba ya halartar al’amuranta tsawon wata shida saboda abin da ta hango. Ka ga ya yi nesa da PDP tsawon wata shida. Shi kuwa Abdulmalik da yake ba wani mukami yake da shi ba, shi za mu iya cewa dan PDP ne ya koma kuma komawarsu ba za ta girgiza tafiyar PDP ba, ko tafiyar dan takararmu na Gwamna. Domin yanzu al’umma kansu ya waye, muna kuma kara wayar musu da kai a siyasa,” inji shi.
Ya ce “In da komawarsu za ta yi wani tasiri da lokacin da aka ambaci sunayensu an ji an cewa sun fita da magoya bayansu mutum dubu kaza, duk babu wannan illa dai sunayen mutum 18 din kawai aka kira iyaka.”
Koma yaya lamarin zai kasance, wadanda za su kada kuri’arsu ga ’yan takarar Gwamna, wanda ya samu kuri’u mafi yawa ne zai sauya akalar siyasar jihar.
Yanzu haka dai ’yan takara da suka fito daga jam’iyyu 24 ne hukumar zabe ta bayyana sunayensu a matsayin wadanda suke takarar Gwamna a Jihar Bauchi, cikinsu har da Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar na APC da Sanata Bala Muhammad na PDP, Dokta Muhammad Ali Pate na PRP da Ambasada Shu’aibu Adamu na NNPP da Hajiya Baheejah Mahmood ta ACD da Auwal Isa na APM da Alhaji Ahmed Iliyasu na PDM da Bello Sa’idu Abubakar na PPM. Sauran su ne Sanusi Balarabe na SNP da Usman Isma’ila Yalwa na Maja da Rabi’u Abubakar Ahmad na CA da Idris Ahmad na UPN da Kani Gidado Muhammad na MMN. Sai Kabiru Isiyaku na APP da Aliyu Mahmud na AD da sauransu.