Yadda cinikin fatar jaki ke jawo barazanar karewar jaki a duniya

Jaki dabba ne mai dadadden tarihi a Najeriya musamman ma a yankin Arewa, inda ake amfani da shi a mafi yawa a yankunan  karkara wani lokaci ma har cikin birane inda za a tarar  ana amfani da shi wajen ayyukan yau da kullum da suka hada da dibar kayan gona ko yin noman kansa ko […]

Yadda cinikin fatar jaki ke jawo barazanar karewar jaki a duniya

Wata kasuwar ana cinikin jakuna

Jaki dabba ne mai dadadden tarihi a Najeriya musamman ma a yankin Arewa, inda ake amfani da shi a mafi yawa a yankunan  karkara wani lokaci ma har cikin birane inda za a tarar  ana amfani da shi wajen ayyukan yau da kullum da suka hada da dibar kayan gona ko yin noman kansa ko dibar kasar gini ko amfani da shi a wajen sufuri tsakanin kasuwanni da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a.

Sai dai a ’yan shekarunan jukunan suna fuskantar barazanar karewa daga doron kasa sakamakon sayen fatun jakunan da ’yan kasar  China suke yi, inda ake zargin suna ba mutane kudi suna bi lungu da sako na Arewa domin saye jakunan a yanka su daga bisani a fede a cire fatar a tafi da ita kasarsu.

Wannan dalili ya sa wata kungiya ta kasar Birtaniya mai suna ‘The Donkey Sanctuary’ ta shirya taron wayar da kan  jama’a da mahukunta kan illar da ke tattare da bacewar jakunan a dorun kasa inda masana daga sassa daban-daban suka gabatar da makaloli a taron na yini guda da ya gudana a ranar Alhamis din makon jiya a Abuja.

Taron ya samu hallartar Ministan a Ma’aikatar Gona da Raya Karkara da wadansu daga cikin ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da malaman jami’o’i da sauran masu ruwa-da- tsaki.

Alhaji Garba Datti, dan majalisa ne mai wakiltar Karamar Hukumar Sabon Garin Jihar Kaduna yana daya daga cikin wadanda suka shirya wannan taro. Kuma shi ne ya shigar da dokar haramta fataucin fata da cin naman jaki inda dokar ta wuce karatu na biyu a zauran majalisar.

Da yake zantawa da Aminiya kan wannan kudirin dokar da ya shigar gaban majalisa  Alhaji Garba Datti ya ce “Wannan doka tana kunshe da hana safarar jakuna da cin namansu, lura da yadda mutanen kasar China suke kokarin kawar da wannan dabba daga doron kasa ta hanyar safararsu.  Kuma wannan kudiri namu ya jawo hankalin Majalisar Dinkin Duniya, sannan kasashe da dama sun yi doka a kan fataucin jakunan, kuma wannan doka da muka kai majalisa ita ta sa wannan kungiya ta Donkey Sanctuary ta kawo taron nata Najeriya.”

Da Aminiya ta tambaye shi game da abin da wannan doka ta kunsa Alhaji Datti ya ce “Wannan doka ta kunshi horo mai tsauri a kan duk wanda aka kama yana fataucin fata ko cin naman jaki a fadin Najeriya ko kuma shigowa da fatar ko naman jakin cikin kasar nan.

“Dokar ta tanadi daurin shekara 10 a gidan yari ga duk wanda aka same shi da wannan laifi sannan idan aka kama wanda ya dauko dakon jakunan a motarsa don sayarwa ga masu cin nama ko sarrafa fatarsu, to doka za ta kwace motar ta mallaka wa gwamnati ita. Wannan  doka za ta yi wa wandanda suke da jakuna gata domin a yanzu satar jakuna ta yi kamari a wurare da yawa a Arewacin kasar nan,” inji shi.

Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano Alhaji Manniru Babba Dan Agundi, shi ne Shugaban Kwamitin Jami’o’i da Kwalejojin Koyon Aikin Gona na Majalisar, lokacin da yake amsa tambayar Aminiya kan ko dokar za ta musguna wa masu jakuna, cewa ya yi “Ko a  Musulunci an haramta cin naman jaki don haka da wanda ya ci da wanda ya sara masa duk irin alhakinsu daya, kuma duk yawancin masu jakunan nan Musulmi ne sannan masu cin naman nan likitoci sun tabbatar yana da hadarin gaske don haka muna goyon bayan wannan doka kuma muna ba wa wadanda suka shirya wannan taro shawarar a shigo da malaman addini da sarakuna cikin wannan shiri domin  a wayar wa jama’a kai kan hadarin da ke tattare da bacewar wannan dabba da kuma hadarin mu’amala da naman jaki.”

Tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Alhaji Sani Zoro, wanda ke cikin wadanda suka shirya taron ya yi karin haske a kan barazanar da ke tattare da bacewar jaki, inda ya ce “Jaki yana da matukar muhimmanci a cikin al’umma ana amfani da jakuna wajen daukar kasar gini da daukar amfanin gona. Idan aka duba har yanzu babura da Keke NAPEP ba za su iya shiga kowane lungu da sako ba, ka ga ashe har yanzu jakuna suna da matukar tasiri a cikin rayuwar mutane don haka dole mu dauki matakin kare wannan barazana,” inji Zoro

A lokacin da Aminiya ta tambaye shi ko dokar ta shafi hana cinikin jakuna domin amfanin yau da kullum, Alhaji Sani Zoro ya ce “Wannan doka ba za ta shafi cinikin jakuna da aka saba da shi ba a ayyukan yau da kullum. Dokar za ta haramta cinikin jakunan ne ga masu safararsa zuwa kasashen waje ko kuma masu cin namansa a gida.”

Farfesa Sule Bello na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, cewa ya yi bacewar dabbobi irin jaki daga doron kasa  ba karamar asara ba ce ga dan Adam. Ya ce hatta karnuka suna da tasu baiwar da Allah Ya yi musu. Farfesa Sani ya ce “Abin da Allah ya yi maka baiwa da shi lallai abin a kula da shi ne, kuma jakuna suna da tasiri a cikin rayuwarmu dole mu kula da wannan barazana domin mu dakile ta. Za ka ga ko su turawan wasu dabbobi suke kalla su kirkri wasu abubuwa na amfanin yau da kullum, bai kamata a ce mun wulakanta wannan kyauta da Allah Ya yi mana ba.”

Shugaban Kungiyar Donkey Sanctuary Mista Mike Baker cewa ya yi “Tuni bincikensu ya nuna cewa akwai alamun yiywuwar karewar jakuna a Nahiyar Afirka musamman nan Arewacin Najeriya, don haka dole hukumomi sun samar da dokokin da za su shawo kan wannan barazana, sannan ga mutanen da suke cin naman jaki likitoci sun tabbatar yana da hadarin gaske ta hanyar kamuwa da cututtuka da kuma yada ta a tsakanin al’umma, dole sai mun tashi mun yi aiki tare domin kawar da wannan babbar barazana.”