Yadda cizon macizai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Neja

Manoman Ƙaramar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun koka kan ƙaruwar kisan da maciji ke yi a gonakinsu a lokacin da suke girbe amfanin gona. Ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Mokwa a majalisar dokokin jihar, Ndagi Zakari ne ya bayyana haka a madadin manoman da ke mazaɓarsa a zauren majalisar, inda ya […]

Yadda cizon macizai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Neja

Maciji

Manoman Ƙaramar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun koka kan ƙaruwar kisan da maciji ke yi a gonakinsu a lokacin da suke girbe amfanin gona.

Ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Mokwa a majalisar dokokin jihar, Ndagi Zakari ne ya bayyana haka a madadin manoman da ke mazaɓarsa a zauren majalisar, inda ya ce abin mamaki ne yadda ake yawan samun mace-macen jama’a sanadiyyar cizon maciji.

Ya ce, waɗanda lamarin ke rutsawa da su macizan na kai masu farmaki ne a kan hanyarsu ta zuwa gona.

Ɗan majalisar ya ce, duk da yawan saran maciji da ke haddasa asarar rayuka, ba a samun allurar riga-kafin dafin maciji a asibitocin ba saboda tsadar allurar, inda ya ce ta kai kimanin Naira 200,000, wanda manoman ba su da kuɗin da za su saya.

Ya yi nuni da cewa, lokacin girbi a kan sami yawaitar matsalar saran maciji, inda ya bayyana cewa macizan kai farmaki ga manoman da suke girbin amfanin gona.

Ya nuna takaicinsa a kan yadda waɗanda abin ya shafa kan yi amfani da hanyoyin gargajiya, wanda a ganinsa ba ta da aminci kuma ba abin dogaro ba ce sakamakon rashin samun magani.

A cikin ƙudurinta, majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta shiga tsakani ta hanyar samar da alluran riga­kafin dafin kyauta ga cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a a faɗin jihar domin rage yawan mace-mace.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Na kusa zama ɗan ƙwaya a baya — Obasanjo

Cibiyar Athena ta horar da malamai 100 hanyoyin bunƙasa koyarwa a Katsina