Yadda cutar kansa ke hallaka mutane a Najeriya
A daidai lokacin da aka yi bikin Ranar Yaki da Cutar Kansa (Ciwon Daji) ta Duniya, ranar Talatar da ta gabata, Aminiya ta gano cewa na’urar gasa kashi da ake amfani da ita wajen magance cutar guda 8 ne kacal ake da su a duk fadin Najeriya. Asibitocin da ke da na’urorin, su ne, Asibitin Koyarwa […]
Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire
A daidai lokacin da aka yi bikin Ranar Yaki da Cutar Kansa (Ciwon Daji) ta Duniya, ranar Talatar da ta gabata, Aminiya ta gano cewa na’urar gasa kashi da ake amfani da ita wajen magance cutar guda 8 ne kacal ake da su a duk fadin Najeriya.
Asibitocin da ke da na’urorin, su ne, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas da ke Idi-Araba da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkawto da Babban Asibitin Kasa da ke Abuja da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya da ke Nssuku da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Gombe da kuma Jami’ar Unibersity College da ke Ibadan.
Kuma bincike ya nuna wasu daga cikin na’urorin ba sa aiki, wanda hakan ya kara jefa masu fama da cutar cikin matsala.
Wata kididdiga ta nuna cewa Najeriya ta rasa akalla mutum dubu 281 da 308 dalilin cutar ta daji kansa a shekara hudu da suka gabata, hakan ba a hada da mutanen da suke mutuwa dalilin cutar ba da ba su je asibiti ba.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun rasu a gida a sanadiyar cutar saboda ba sa iya biyan kudin magani.
Malama Bilkisu Abubakar, mai shekar 47 ta kwashe tsawon shekara biyu zuwa uku tana fama da kansar mama a Kaduna, ta ce da farko ta fara ganin jijiyar mamanta ne ta dan kumbura, “Daga baya ta yi dan kullutu kuma da farko babu wani ciwo ko zafi. Amma bayan na fara shan magunguna sai kullutun ya koma ya kwanta daga baya ya fashe bayan ya yi ruwa sannan ya tsiyaye kuma a yanzu haka yana bushewa kadan da kadan,” inji ta.
Bilkisu, wacce ta ce da an fara tunanin yi mata aiki ne amma yanzu tana karbar allura kafin daga baya a san matakin da za a dauka.Ta ce ita ba ta san tsadar komai na magunguna ko alluran da ake mata ba domin wata gidauniya ta Fauziyya D. Sulaiman ce ta dauki nauyinta.
Batun kyama ko wariya da take fuskanta, Bilkisu ta ce saboda ita kadai ce a gidanta ya rage mata fuskantar tsangwama ko kyama daga abokan zama.
Shi kuwa Rabi’u Magaji Dambatta, wanda ya shafe shekara daya da rabi da kamuwa da ciwon dajin, ya ce bai taba fuskantar wariya daga jama’ar da ke tare da su ba. Ya ce duk da yakan samu tallafi daga wata kungiya, amma a wasu lokuta yakan sayi magunguna da kudinsu ke kamawa daga Naira dubu 10 zuwa dubu 50 wadanda duka-duka cikin mako uku suke karewa.
A Jigawa, wakilinmu zanta da Malam Ibrahim Isma’il mutumin Albasu da ke Jihar Kano, inda ya ce asalin ciwon mahaifinsa ne ya tura shi gona aiki da shanu, bayan ya dawo ya kwanta rashin lafiya, inda yake jin kamar ana soka masa wani abu a cikin jikinsa, shi ne daga nan sai kuma suka dukufa neman maganin gargajiya da na zamani.
Da lamarin ya gagara shi ne aka kai shi Asibitin Wudil, a can ya yi kwanaki daga can aka kai shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, saboda nisa da tsadar kayan aiki sai suka dawo Babban Asibitin Dutse.
Ya ce kafin a kawo shi asibitin, ya sha wahala saboda yawan karewar jininsa ba ya iya takawa da kafarsa, amma ko yanzu likitoci suka sallame shi zai iya komawa gida ya zauna.
Daga nan ya ba masu wannan ciwon shawarar su tafi asibiti likitoci su duba su kada su bata lokacinsu neman maganin gargajiya.
Malama Fatima Ibrahim da ke Unguwar Rijiyar Lemo a Kano, wadda ta yi jinyar mijinta wanda ya yi fama da cutar kansa tsawon shekara hudu a kafin ya rasu, ta shaida wa Aminiya cewa “Lokacin mun dauka basir ne an yi ta yi masa maganin gargajiya, wani lokacin mararsa ta kulle ya kasa yin fisari ana nan har muka tafi da shi Asibitin Malam Aminu Kano a nan ne aka gano cewa kansa ce, a haka su ma suka ci gaba da ba shi kula ana sayen magani har aka ce mafitsararsa ta tabu ta daina aiki dole a cire ta, bayan an cire aka sanya masa roba ya komo gida kullum sai dai a yi masa kunzugu. Sai da muka shekara a haka ana cikin hakan sai inda aka yi masa aikin ya kumbura ya fashe yana fitar da wani irin abu baki mai wari, haka nake sanya masa fanfas a daya bangaren kuma ina sanya masa auduga in share wajen. Kullum aikin ke nan haka muka yi ta fama.”
Ta ce a waccan lokacin likitocin Asibitin Malam Aminu Kano sun yi ta ja musu rai su ce a yi aiki na biyu yau a yi gobe amma shiru babu alama. “Wani lokaci da ya gaji da zama sai ya ce shi kasuwa zai koma haka ya fara fita wani lokacin in ya fita sai dai a dawo da shi, daga nan muka sake komawa Asibitin Malam Aminu Kano bayan wani lokaci likitocin suka ce sun sallame mu, sai ya ce musu yaya za su sallame shi bai warke ba? Yaya za su sallame shi bayan ciwo na cinsa? Sai ya nemi su ba shi shawara sai suka rubuta mana takarda suka ce mu tafi Zariya Asibitin Shika. Da muka isa can sai aka ce babu abin da za a yi sai dai a rika sanya shi a cikin na’urar gasa jiki (Radiotherapy) nan suka ba mu takarda babban dansa ya sa hannu, suka ce dole sai mun sanya hannu mun yarda domin za a iya samun matsala idan an saka shi cikin na’urar cutar ta yadu, zuwa sassan jikinsa kamar zuciyarsa da kwakwalwarsa. Haka muka sa hannu domin sun nuna mana babu wani abu da za su iya yi sai wannan, lokacin an yi wata uku ana saka shi cikin na’urar kwana dai-dai kawai ake fashi kuma duk sakawa daya Naira dubu 30 ne, haka muka yi ta fama ida mun tura shi a keken guragu mun kai saka shi sai kowa ya ruga a guje ya bar wajen har da ma’aikatansu domin tsoron kada cutar ta harbi mutum, don sun fada mana tana harbawa in an saka mutum. Haka muka yi ta fama har bayan wata uku lokacin da sa’a ta yi, Allah Ya karbi ransa a asibitin,” inji ta.
Dokta Imam Muhammad Ibrahim, likita ne a sashen kula da cututtukan kumburi da cutar daji a Asibitin Malam Aminu Kano ya shaida wa Aminiya cewa har zuwa yanzu bincike ilimi bai gano takamaimam abin da ke kawo cutar daji, ba sai dai akwai wasu abubuwa da ke da alkala kuma suke taimakawa wajen samun cutar da suka hada da gado da sauransu.
“Ana kamuwa da cutar daji ta hanyar gado, akan samu cutar tana yawo a cikin kwayar halitta. Idan iyaye ko kakkanin mutum sun taba yin cutar to akwai yiwuwar shi ma ya kamu da ita saboda kwayoyin cutar da ya gada daga iyayensa. Sannan akwai mu’amala ta yanayin aiki, misali mutanen da ke aiki a wajen da ake sarrafa wasu sinadarai da abubuwa, to idan mutum yana shakar su yakan zama a karshe sun yi masa illa har ya kamu da cutar daji. Kuma mutanen da ke mu’amala da barasa da taba sigari sukan iya kamuwa da ita. Haka nau’in abincin da mutane ke ci musamman na Turawa da suke kunshe cikin gwangwani ma na taimakawa wajen kamuwa da cutar. Kuma ana iya kamuwa da cutar ta hanyar karin jini idan a cikin jinin akwai wasu sinadarai,” inji shi.
Da yake bayani game da nau’o’in cutar kansa Dokta Imam ya ce sun hada da ta mama da ta bakin mahaifa da ta hanji da ta hanta da mafitsara da sauransu.
“Dukkansu ana iya gane su kafin su girma, misali ta mama, za a ga alamun kullutu a jikin maman amma ba kowane kullutu ke zama na cutar kansa ba, gwaji ne kadai zai tabbatar da haka. Kuma idan mace ta kamu da cutar a mahaifa za ta rika jin zafi yayin yin jima’i ko ta rika zubar da jini. Kuma idan ta huhu ce mutum yakan fara da tari wani lokaci har ya rika kakin jini. Idan ta hanji ce kuma akan samu bahayan mutum ya canja da sauransu,” inji shi.
Kan yadda ake kula da masu cutar, Dokta Imam ya ce cutar kansa cuta ce da ke daukar tsawon lokaci ba ta warke ba, kuma cuta ce da ke cin kudi wajen kula da ita. Ya ce hanyoyin da za a bi wajen guje wa cutar dajin sun hada da yin wata allura ga yara da kula da lafiyar mama ga mata da guje wa shan barasa da guje wa cin abincin gwangwani da sauransu.
Dokta Joseph Dikka likita a fannin kula da masu cutar daji a Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Yola, ya yi kira ga gwamnati ta gina fannin kula da masu dauke da cutar daji. Ya ce cutar daji ta kasu da yawa; akwai ta yara da mata da ta maza kuma alamomin cutar sun bambanta a jinsin mutum.
Ya bayyana alamomin cutar da za a gane a zahiri na da alaka da rashin sha’awar abinci da rashin jini da kuma rama. Ya ce in cutar ta gado ce ba za a iya magance ta ba, idan kuma ba ta gado ba ce kuma aka gano ta da sauri, za a iya magance ta.
Ya yi kira ga iyaye su dage wajen shayar da ’ya’yansu nono domin hakan na rage kamuwa da dajin nono kuma yana kara wa yaron kuzari da kare shi daga cututtuka da dama.