Yadda cutar mafitsara ke wa maza kisan mummuke
Cutar mafitsara cuta ce da take neman zame wa maza masu yawan shekaru ruwan dare.
Cutar mafitsara cuta ce da take neman zame wa maza masu yawan shekaru ruwan dare. Dakta Hassan Mukhtar Abubakar, babban likita a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ya ce, cutar Benign Prostatic Hyperplasia (BPH), wadda ake kira kumburin prostate na daga cikin manyan cututtukan da ke haddasa wahalar fitar fitsari ga maza masu shekaru 40 zuwa sama.
Dakta Hassan ya bayyana cewa, duk da ci-gaban da aka samu a fannin likitanci, har yanzu ba a gano takamaiman abin da ke haddasa cutar ba.
Sai dai ya ce, bincike ya nuna cewa, tsufa da kuma sauye-sauyen sinadaran halitta da ake kira hormone a jikin namiji na daga cikin manyan abubuwan da ke da alaka da kamuwa da ita.
A cewarsa, “prostate wata karamar jika ce (gland) ce da Allah Ya halitta ga maza, wadda take a karkashin mafitsara (bladder) kuma ta kewaye hanyar da fitsari ke bi (urethra). Idan wannan jikar ta kumbura fiye da yadda ya kamata, tana matse hanyar fitar fitsari, lamarin da ke hana fitsari fita yadda ya kamata.”
Rahoton Aminiya ya nuna cewa, wannan cuta ta mafitsara cuta ce da akasari ta fi yawaita ga mutanen da shekarunsu suka kai tsakanin 50 zuwa 70 ko ma fiye da hakan.
Na shafe shekara hudu ina fama da cutar-Malam Isa Zubairu
Aminiya ta samu tattaunawa da wani mai suna Malam Isa Zubairu wanda ya ce, shi ma ya yi fama da irin wannan cuta ta mafitsara shekaru biyar da suka gabata, yadda ala tilas sai da aka yi masa aiki a Babban Asibitin garin Damaturu .
A cewarsa kafin a yi masa aikin, akalla ya shafe sama da shekara hudu, yana fama da cutar mafitsara, inda ya rika amfani da magungunan gargajiya, yana jikawa, yana sha don neman sauki. Amma sai da ta kai ga ya gagara yin fitsari, sannan ne tilas ya kai kansa asibiti, don neman mafita.
Ya ce, lokacin da ya je asibitin, likita ya gwada shi, ya tabbatar masa da cewa, ciwon ya dade a jikinsa kuma dole sai an yi masa aiki, don samar masa mafita, wanda kuwa hakan aka yi. Bayan kammala gwaje-gwaje aka fada masa kudin aiki, ya biya, aka yi ya samu lafiya.
Malamin ya ce, “ciwon mafitsara ciwon ne mai wahalarwa, domin sai da ta kai ga in na je fitsari sai na kai mintuna kamar biyar ko ma sama da hakan kafin in kammala, kasancewar fitsarin ba ya fita da sauri ga kuma zafi da nake ji sosai.”
Don haka ne malamain yake ba wa maza shawara, musamman ma wadanda ke da yawan shekaru da cewa, da sun fara ganin alamar kamuwa da wannan cuta, to kar su bata wani lokaci, su tafi asibiti kawai don a duba su tun ma lokaci bai kure ba.
Shekara uku ina shan maganin gargajiya, amma ban warke ba-Majinyaci
Shi kuwa wani malami da Aminiya ta tattauna da shi, amma ya nemi a boye sunansa, wanda yake fama da wannan cuta ta mafitsara, ya bayyana cewa, akalla ya kai shekaru uku yana fama da cutar, kuma a yanzu haka yana fama da matsala sosai wajen yin fitsari, domin wani lokacin in ya je yin fitsari, bayan radadin da yake ji da bata lokacin da yake kafin ya gama da bayan ya gama kuma yakan ga jini ya biyo baya.
Ya kara da cewa, “wani lokacin ko da na gama, na tashi ma daga bisani nakan ji wani guntun fitsari na fita, inda yake bata mini wando. Hakan na sa sai na sake komawa makewayi, na sake wanke jikina da har ma inda fitsarin ya taba min a wandona,” in ji shi.
A cewarsa, a halin yanzu duk da yake ya san yana fama da cutar mafitsarar, har yanzu maganin gargajiya yake sha, domin ba ya da kudin zuwa asibiti.
Ya kara da cewa, amma yanzu yana nan yana tanadin kudi don zuwa asibiti ganin cewa, an sanar da shi cewa, cutar na bukatar kudi masu yawa kafin a samu waraka.
Don haka malamin ya roki gwamnati da ta taimaka, ta rika sa hannu wajen yin aiki ga masu irin wannan jinya ta cutar mafitsara a Jihar ta Yobe, in ma zai yiwu, a rika yin aikin kyauta, domin ko ba komai akasarin mutanen da ke fama da wannan cuta, dattawa masu karamin karfi ne.
Yadda na yi fama da cutar mafitsara-Dattijo mai shekara 70
Wani dattijo mai shekara 70 a Jihar Gombe da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana yadda ya shafe wata goma sha daya, yana fama da cutar mafitsara da ta wahalar da shi kafin a yi masa tiyaya.
Dattijon ya ce, ya samu wannan larurar ce bayan wani hatsari da ya faru da shi, inda ya karye a kafa, yayi jinya ta wata hudu, bayan ya fara takawa da sanduna wannan ciwon ya same shi.
Ya ce, a lokacin da larurar ta same shi, ya yi fama da matsanancin yanayi da har ta kai sai da aka yi sa masa robar fitsari (wato catheter) da take sauwake masa yadda yake fitsari.
Ya kara da cewa, “saboda yanayi, sai da na shafe wata goma da robar fitsari, ina fama da ita, yayin da ‘ya’yana ke jinya ta, a inda na kwanta a asibitin gwamnati na wani lokaci. Na yi ta fama yau a sallame ni gobe a dawo har aka ba ni shawarar zuwa wani asibiti na kudi da aka yi mini gwaje-gwaje, sannan aka yi mini tiyaya, aka cire ciwon.”
Ya kuma ce, bayan an yi masa tiyayar sai da ya kwana goma sha hudu, sannan aka sallame shi, inda ya je, ya karasa warkewa a gida.
A cewarsa, har ya yi wannan jinya, ya warke ba wani da ya ba shi taimako daga gwamnati ko wata kunkiya.
Sai dai ya ce, wannan ciwon ba karamin ciwon ba ne, domin kafin a yi sa masa robar fitsari sai da ya yi ta kara wajen yin fitsari, saboda azabar zafi.
Shi ma wani dattijo mai suna Malam Sa’idu da ya samu irin wannan matsala a kwana-kwanan nan, inda ya ce, sai da ya kashe kusan Naira dubu dari uku kafin a yi masa aikin tiyata, amma da Allah Ya taimaka, an yi masa kuma ya warke.
“Akwai azaba idan kana fama da irin wannan matsalar, amma kuma idan aka yi maka aiki, ana dacewa,” in ji shi.
Wakilinmu ya ziyarci wani asibiti mai zaman kansa a Gombe, don jin ta bakin wani likita Dakta Usman Musa kan yadda suke fama da masu wannan matsalar, inda ya ce, aikin tiyatar ciwon ba ta da wahala, idan kuma aka yi, ana rabuwa da shi har abada ba zai sake dawo wa ba.
Dakta Musa ya ce, “ana yawan samun irin wannan matsala a tsakanin dattawa da suke da shekaru sai dai har yanzu babu wata kunkiya ko gwamnati da take ba da kulawa ta musamman wajen yin tiyayar irin wannan aiki kyauta, kamar yadda ake daukar nauyin wasu cututtuka.”
Alamomin cutar
Ya kara da cewa, “mafi yawan masu fama da cutar kan fara lura da raunin karfin fitsari da jinkirin fara yin fitsari da yawaita tashi da dare, domin yin fitsari sau da dama da jin matsananciyar bukatar yin fitsari cikin gaggawa da kuma jin kamar ba a gama zubar da fitsarin gaba daya ba.”
A cewarsa, wasu marasa lafiya kan rika matsa karfi ko yin nishi kafin fitsarin ya fito, saboda toshewar hanyar fitsarin da kumburin prostate ke haifarwa.
Likitan ya kuma bayyana cewa, sauyin sinadarin Dihydrotestosterone (DHT) na daga cikin abubuwan da ake dangantawa da ci gaban kwayoyin prostate, wanda kan sa jikar ta ci gaba da girma har ta haifar da matsalar.
Ya ce, “cutar ta fi kama maza masu shekaru 40 zuwa sama, kuma yawan masu kamuwa da ita na karuwa ne yayin da shekaru ke karuwa.”
Ire iren cutar
Da yake bambance cutar kumburin prostate da kansar prostate, Dakta Hassan ya ce, BPH ba cutar daji ba ce, domin kumburin ba ya yaduwa zuwa sauran sassan jiki. Sai dai ya ce, kansar prostate na faruwa ne idan kwayoyin prostate suka fara hayayyafa ba tare da ka’ida ba, lamarin da kan sa cutar ta bazu zuwa sauran sassan jiki.
Ya ce, “baya ga wahalar yin fitsari, masu fama da kansar prostate na iya samun zubar jini ta fitsari da ciwon baya da ciwon kashin kugu da rage nauyi ba tare da wani dalili ba da kuma tsananin kasala.”
Hanyoyin kariya
Game da hanyoyin rage hadarin kamuwa da cutar, masanin ya ce, shan koren shayi (green tea) da cin kifi masu dauke da sinadarin Omega-3 irin su salmon da mackerel da motsa jiki a-kai-a-kai da kuma rayuwar aure mai kyau na daga cikin abubuwan da bincike ya nuna na iya taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da ita.
Maganin cutar
Dangane da magani, likitan ya ce, akwai magungunan da kwararrun likitoci suka amince da su wajen kula da cutar, yayin da ake yin tiyata, idan kumburin ya yi tsanani ko ya haifar da wasu matsaloli.
Shawara
Dakta Hassan ya shawarci maza da kada su yi watsi da alamomin wahalar yin fitsari ko kuma su dogara da shan maganin gargajiya ko shan magani kai-tsaye ba tare da ganin likita ba.
Ya ce, zuwa asibiti da wuri, domin yin gwaje-gwaje da samun kulawar kwararru na taimakawa wajen gano cutar da wuri da kuma samun saukin magani kan lokaci.
Ya kara da cewa, “har zuwa yanzu babu wani riga-kafi da aka tabbatar yana hana kamuwa da cutar Benign Prostatic Hyperplasia (BPH). Sai dai ya jaddada cewa, duba lafiya a-kai-a-kai, musamman ga maza masu shekaru 40 zuwa sama, na taimakawa wajen gano cutar tun da wuri da kuma kauce wa matsalolin da za ta iya haifarwa.