Yadda cutar Maleriya ke addabar yara kanana a Kamaru

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru ta bayyana cewa an samu asarar rayukan mutane fiye da dubu hudu sanadiyyar cutar zazzabin cizon sauro (Maleriya) a bara.  Wannan adadin ya sanya cutar a sahun gaba daga cikin cututtukan da suke lakume rayukan jama’a a Kamaru. Yankin arewacin kasar ne kuma ya fi fama da cutar. A dalilin […]

Yadda cutar Maleriya ke addabar yara kanana a Kamaru
Yadda cutar Maleriya ke addabar yara kanana a Kamaru

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru ta bayyana cewa an samu asarar rayukan mutane fiye da dubu hudu sanadiyyar cutar zazzabin cizon sauro (Maleriya) a bara. 

Wannan adadin ya sanya cutar a sahun gaba daga cikin cututtukan da suke lakume rayukan jama’a a Kamaru. Yankin arewacin kasar ne kuma ya fi fama da cutar. A dalilin hakane Ministan kiwon lafiya Andre Mama Fouda ya bayyana cewa za a sake raba wa jama’a gidajen sauro a kyauta wadanda aka yi feshin magani a ciki nan gaba zuwa watan Yuni.
Shekaru uku ke nan da suka gabata Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) take amfani da take daya, a duk sanda ake bikin tunawa da ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro. Taken da ako da yaushe manufarshi shine na ganin cewa an samu raguwar macewar marasa lafiya sanadiyar cutar. A dalilin haka ne domin kare jama’a da kamuwa da cutar Hukumomi suka fi mayar da hankali wurin raba wa jama’a gidajen sauro a kyauta wadanda kuma aka yi wa feshin magani.
A ci gaba da irin wannan yunkurin ne Ministan Mama Fouda ya ce za su tsara kamfe na biyu a wannan shekara na rabon gandun gidajen sauro a kyauta da adadinsu zai kama miliyan 12 wadanda za su bai wa ‘yan Kamaru sama da miliyan 20 damar rintsawa hankali kwance. Har ila yau, Ministan ya ce za su ci gaba da samar wa yara kanana miliyan daya da dubu 100 masu kasa da shekaru biyar a duniya kariya a iyyance zuwa lokaci-lokaci game da wannan cutar a lardunan arewa da kuma arewa mai nisa, inda cutar ta fi kamari.
Alkalumman Hukumar kasar Kamaru mai kula da yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta ce kasha 40 na daukacin masu kamuwa da cutar a zaune suke a lardunan na arewa da kuma arewa mai nisa. Hukumar ta ce, kodayake, idan aka danganta adadin mutanen bara wato dubu hudu da suka mutu a bara sanadiyyar cutar za a ga cewa ya ragu da na adadin shekarar 2013, inda kasha 70 na daukacin wadanda suka mutu daga arewacin kasa suka fito.
Hakan ya nuna kenan tasirin yin amfani da gidajen sauron da aka fara rabawa jama’a. Har ila yau, a yunkurin neman shawon kan kaifin cutar zazzabin cizon sauro Gwamnatin Kamaru ta bullo da wani shiri, mai suna “KO” Maleryia shirin da ya ba da dama a wancan karo raba gidajen sauron kusan miliyan tara. Hakan kuma ya sa an kashe kudi da suka haura CFA biliyan talatin da hudu.