Yadda TB ke Kashe Mutum 18 a duk Sa’a a Najeriya

Wata kungiyar farar hula mai suna BAN ta ce Najeriya na cikin kasashen da cutar ta yi katutu

Yadda TB ke Kashe Mutum 18 a duk Sa’a a Najeriya

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire

A duk sa’a daya mutum 18 na rasa rayukansu sanadiyyar cutar tarin fuka ko TB.

Wata kungiyar farar hula mai suna Breakthrough Action Nigeria (BAN) ce ta bayyana hakan.

Kungiyar ta BAN ta ce tarin fuka na cikin cututtuka 10 masu kisa a duniya kuma Najeriya na cikin kasashe 14 inda cutar ta yi katutu, kasancewar a duk mutum 1,000 ana samun mutum biyu da ke dauke da ita.

Jami’an kungiyar ta BAN sun bayyana hakan ne yayin wani taron kara wa juna sani da suka shirya wa ‘yan jarida a yankin Neja Delta da hadin gwiwar Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID).

“Manufarmu ita ce fahimtar da mutane girman matsalar da hanyoyin shawo kanta a Najeriya; muna kuma so mu kara wa mahalarta kwarewa wajen ba da labaran da suka shafi rayuwar al’umma”, inji Eze Eze, daya daga cikin manyan jami’an kungiyar ta BAN.

A lokacin taron na sa’a uku, kungiyar BAN ta ce tarin fuka na da kamanceceniya da COVID-19, hakan ne ya sanya aka wayar da kan mahalarta ta yadda za su iya gane bambancin ciwon tarin fuka da COVID-19 da  kamanceceniyar su.

A cewar Mista Eze, an shirya taron kara wa juna sanin ne domin bai wa ‘yan jarida damar bayar da ingantattun rahotanni game da cutar domin mahukunta su dauki mataki, tare da wayar wa al’umma kai da ba su damar daukar matakan da suka dace don gane cutar.

A cewar wadanda suka shirya taron, idan aka yi sake ba a yi wa mutum guda da ya harbu da cutar ta tarin fuka magani ba, zai iya harbar mutum 10 zuwa 15, don haka matsala ce da ya kamata a mai da hankali a kanta.