Yadda dalibai ke damfara ta yanar gizo – Hukumar EFCC

Aminiya ta samu ganawa da shugabar sashen wayar da kai ta hukumar Yaki da  da cin hanci da kuma ta’annutin kudi (EFCC), Hajiya Aisha Larai Musa, inda ta yi tsokaci kan ayyukan hukumar da kuma dalilan da suka sanya hukumar ta shirya taron wayar  da kan ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin tarayya da ke jihar Nassarawa a […]

Yadda dalibai ke damfara ta yanar gizo – Hukumar EFCC

Aminiya ta samu ganawa da shugabar sashen wayar da kai ta hukumar Yaki da  da cin hanci da kuma ta’annutin kudi (EFCC), Hajiya Aisha Larai Musa, inda ta yi tsokaci kan ayyukan hukumar da kuma dalilan da suka sanya hukumar ta shirya taron wayar  da kan ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin tarayya da ke jihar Nassarawa a karshen makon da ya gabata. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ki bayyana mana dalilan da suka sanya kuka shirya wannan taron a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke jihar Nasarawa?
Hajiya:  Mun shirya wannan taro ne don mu wayar wa jama’a da kai kan ayyukan hukumar EFCC da illar cin hanci da kuma yadda jama’a da ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Nasarawa za su ba mu hadin kai wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan. Ka san cewa matsalar cin hanci ba aiki ne na mutum guda ba, lamari ne da ya shafi kowa da kowa. Saboda haka muna kira ga jama’a su ba mu hadin kai kuma su goyi bayan abin da muke yi na yaki da cin hanci. Don shi cin hanci ya shafi kowa da kowa, sannan bai tsaya a kan ma’aikatan wannan makaranta ba kawai.
Aminiya: Kin bayyana cewa hukumar EFCC ta kafa kungiyoyin yaki da cin hanci a makarantu, me ye dalilin wannan yunkuri naku?
Hajiya:  Mun kafa wadannan kungiyoyi ne a makarantu don su karfafa gwiwar yara tun daga matakin firamare da sakandire har zuwa jami’a. Babban dalilin kafa wannan kungiya da a turance ake kira “Integrity Club” shi ne don idan yaran nan sun girma su nisanci cin hanci da rashawa. Muna koya musu yadda za su zama masu gaskiya a dukkan al’amuransu, su zama masu gaskiya da rikon amana, da yin biyayya ga na gaba. Sannan kuma muna nusar da su kada su dauki duk wani abu da ba nasu ba. Babban sakon da muke so mu isar ga yara shi ne su zama mutane masu gaskiya da rikon amana. A manyan makarantu kuwa kungiyar na fadakar da dalibai su kyamaci cin hanci da rashawa kwata-kwata. Su daliban jami’a ka san sun girma sun fara mallakar hankalansu, sun riga sun san illar cin hanci. To shi ya sa muke tunatar da su hadarin da ke tattare da aikata cin hanci da rashawa tare da kuma da fadakar da su yadda za su kauce wa fadawa tarkon cin hanci ta hanyar nuna musu misalai na ’yan’uwansu dalibai da suka fada cikin tarkon cin hanci da rashawa wadanda aka kama su kuma aka gurfanar da su a gaban kotu. Kuma muna fadakar da su abin da shari’a ta yi tanadi da hukuncin da za a yanke wa duk wanda aka samu da laifin cin hanci da satar kudin jama’a. Muna yin haka ne don ya zama darasi gare su.
Aminiya: Shin ko za ki gaya mana irin laifukan da kuka samu dalibai sun aikata wadanda a yanzu aka gurfanar da su a kotu?
Hajiya: Ga daliban makarantun firamare da na sakandire kananan laifuka ne, amma ga daliban jami’o’i  laifuka ne wadanda suka hada da mallakar takardun bogi da satar jarabawa, amma babban laifin da sukan aikata mafi girma shi ne damfara ta hanyar na’ura mai kwakwalwa da ake kira (Yahu-yahu). Mafi yawanci sun aikata lafuka masu yawa ta hanyar kafofin sadarwa ta yanar gizo. Misali akwai lokacin da muka kai samame wani shago da ke harkar yanar gizo. A nan muka kama wadansu yara a wurin suka kai mu maboyarsu. A nan muka ga motoci masu tsada da wayoyin hannu da suka karba daga mutanen da suka rika damfara ta hanyar  na’ura mai kwakwalwa. Kuma dukkansu matasa ne da ba su kammala karatun jami’a ba. Akwai wani labari na wani yaro da ya rika damfarar manyan mutane a kasar nan ta hanyar yanar gizo, ba mu san abin da yake amfani da shi ba, amma wadannan mutane sukan zuba makuden kudi a asusunsa na banki masu yawa.
Aminiya: Jama’a na zargin  wadansu daga cikin ma’aikatan hukumar EFCC da ke karbar kudi a wajen wadanda hukumar ke bincike da zimmar za su kawo karshen lamarinsu a hukumar, meye gaskiyar wannan zargi?
Hajiya: Ina kira ga jama’a  da su yi taka-tsantsan. Duk wanda ya ce maka ka ba shi kudi zai kawo karshen binciken da ake yi maka a hukumar EFCC to karya yake yi. Ba ma karbar kudi daga wurin jama’a don mu kawo karshe binciken da muke yi musu.Kuma ina sanar da jama da wadanda muke bincike da wadanda suka kawo mana korafi, duk wanda ya zo wurinsu ya ce shi ma’aikacin hukumar EFCC ne to su tambayi katin shaidarsa na aiki, su tabbatar da cewa shi ma’aikacin hukumar ne kuma kada su kuskura su ba shi ko sisi. Idan zarginka ake yi ka je hukumar EFCC ka rubuta takarda ka fadi gaskiya, idan kuma kai ne mai korafi kai ma ka je ka rubuta kokenka ka fadi gaskiya. Mu ba ma dakatar da binciken da muke yi. Komai daren dadewa muna sake taso da magana mu ci gaba da bincike.Ya kamata jama’a su guji bayar da rashawa da karbar hanci.
Aminiya: ,Akwai zargin da ake yi cewa wasu daga ckin jami’an hukumar EFCC sun sace tare da barnatar da dukiyoyin da suka kwato daga wurin jama’a meye gaskiyar wannan lamari?
Hajiya: Ba na so in yi magana a kan wannan lamari. Ba zan ce komai ba kan wannan batu.