Yadda dalibai mata ke satar jarabawa da ado a faratansu

An kama wadansu mata 35 kan zargin yunkurin satar jarrabawa a wata makaranta da ke Jihar Michoacán a kasar Mexico, inda suka rubuta a msar jarrabawar a jikin faratansu. Ana zargin wasu makarantu da magudin jarrabawa da kuma hanyoyin samun gurbin karatu ga dalibai, inda aka bankado cewa dalibai na sayen amsar jarrabawa a kasar […]

Yadda dalibai mata ke satar jarabawa da ado a faratansu

An kama wadansu mata 35 kan zargin yunkurin satar jarrabawa a wata makaranta da ke Jihar Michoacán a kasar Mexico, inda suka rubuta a msar jarrabawar a jikin faratansu.

Ana zargin wasu makarantu da magudin jarrabawa da kuma hanyoyin samun gurbin karatu ga dalibai, inda aka bankado cewa dalibai na sayen amsar jarrabawa a kasar Mexico a kan Naira dubu 266 da 745 zuwa Naira dubu 444 da 575.

Zuwa hada wannan rahoto hukumomi ba su tabbatar da zargin da ake yi a makarantun biranen Michoacán ba.

Amma kafafen labaran kasar sun yi zargin cewa dalibai 50 da suka rubuta jarrabawar duk sun amsa tambayoyi 100 daidai yadda ake bukata, yayin da wadansu dalibai 300 suka samu maki 99 cikin 100, sannan wasu dalibai 90 suka amsa tambayoyin daidai.

Wannan abin mamaki ne ganin cewa, a wasu biranen jihar sakamakon shi ne maki 71 ne mafi girma a makarantun.

Kan haka ne hukumomi a jihar suka yanke shawarar daliban su maimaita jarrabawar a ranar 21 ga Agustan da ya gabata, sannan an yi nasarar kama akalla mata 35 a manyan biranen Morelia da Arteaga da suke kokarin yin magudin jarrabawar.

Shafin Facebook na wani mai suna Primera Plana Michoacan ya wallafa wani bidiyo da ke nuna wadansu mata 35 da fenti a faratansu da ya yi zargin amsoshin jarrabawar ce da suka kai kusan tambayoyi 100 da suka yi fentin da launuka daban-daban.

An yin fentin cikin launuka 10 a kowane farce, don amsa tambayoyi 100.

Sai dai ba a dakatar da daliban ba, an bar su su rubuta sannan aka kebe su daga sauran daliban. Aka ba su wata roba da ta manne faratansu, don rufe fentin da suka yi.

Wanda ta shirya jarrabawar mai suna Gabriela Santillán Mora ta tabbatar da cewa, duk dalibai matan da aka kama sun yi fentin iri daya ne a faratansu da nufin satar amsar jarrabawar da za a iya zaba daga jerin amsoshin da suka dace da tambayar da aka yi.

NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar