Yadda daliban jami’a suka sace fiye da Naira biliyan biyu a banki
Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama wadansu daliban jami’ar Jos guda biyu, Isaiah Friday da Azzaior Samuel saboda zarginsu da yin zambar kudi har Naira biliyan biyu da rabi.Haka kuma an kama wadansu masu canjin kudi guda biyu Salihu Mahmud da dan Ibrahim game da zambar da daliban […]

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama wadansu daliban jami’ar Jos guda biyu, Isaiah Friday da Azzaior Samuel saboda zarginsu da yin zambar kudi har Naira biliyan biyu da rabi.
Haka kuma an kama wadansu masu canjin kudi guda biyu Salihu Mahmud da dan Ibrahim game da zambar da daliban suka yi.
Ana kuma zargin wadannan daliban da kasancewa cikin gungun wadansu mutane da suka kware wajen shiga cikin komfutocin bankuna suna taba tushen inda ake tura wa mutanen da ke hulda da bankunan kudade.
Shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Legas da kuma Jos.
Ya ce kama su da aka yi ya biyo bayan wata takardar korafi ce da bankin Union da ke Marina a Legas ya tura wa hukumar EFCC a watan Janairun 2013, inda bankin ya yi zargin cewa wadansu da ba a san ko su wane ne ba suna taba bayanen bankin nasu inda suke jirkita su, inda suke daukar kudi daga wadansu asusu suna komawa da shi wadansu asusun a wadansu bankunan.Wanda hakan ya kan sanya su kasa gane lissafinsu a rassan bankunansu.
korafin, wanda shugaban sashin binciken zamba na bankin Union A.F. Olufade ya sanya wa hannu, ta nuna cewa, a sakamakon haka an janye kudi ta wannan hanyar da adadinsu ya kai Naira biliyan biyu da rabi.
Hukumar EFCC ta gano cewa, Friday, wanda yake yi wa rassan bankin Union a Jos aikin gyaran na’urorin kwamfuta ana biyansa, shi ne ya nuna wa mazambatan yadda za su kutsa cikin bayanen bankin kuma suka yi cuta a rassan bankin.
Uwujaran ya ce an bi diddigin Friday kuma aka kamo shi, kama shi da aka yi ne ya yi sanadiyyar kama Azzaior Samuel.’’ Bincike ya nuna cewa Samuel ne ya gabatar daFriday ga Mahmud wanda shi ne kanwa uwar-gamin zambar da kuma wadansu da suka gudu. Mahmud da wadansu da ya hada baki da su sun bayyana wa Friday cewa suna bukatar sanin tushen bayanen bankin ne domin za su tura wadansu kudade, kuma suka yi alkawarin bai wa Friday Naira dubu 500 inda sun samu nasara.’’
Majiyarmu ta gano cewa Friday ya amince da haka, saboda haka a ranar da za a aikata laifin sai Friday ya fada wa ma’aikatan bankin cewa Samuel abokin aikinsa ne zai taimaka masa su yi aiki a ranar. Da suka samu damar shiga inda tushen bayanen bankin yake ne sai suka tura kudi zuwa asusun ajiyar kamfanoni guda shida da ke da asusu a reshen bankin Union da ke Marina a Legas.
Kamfanonin da ke da asusun, kamar yadda Uwujaren ya bayyana su ne, Gona Bureau De Change Limited da Jadmine Bureau De Change Limited da dan Kawu Bureau De Change Limited da Godswill Great Communications ZHG Serbices Limited da kuma A and B Console Limited. Da aka tura kudin sai nan da nan wadannan mutanen suka je suka kwashe, suka bai wa Friday kudin da suka yi masa alkawari, su kuma wadanda a halin yanzu suka gudu, suka raba sauran kudin a tsakaninsu.
Kakakin hukmar EFCC din ya ce hukumarsu ta samu nasarar kwato Naira biliyan biyu da dubu 129 da 900 da kuma wadansu Naira miliyan 134 da dubu 542.
Sauran kayayyakin da ya ce hukumarsu ta kwato sun hada da kujerun daki, da kudinsu ya kai Naira miliyan goma, a dakin Salihu Liman da ke Yaba Legas, da motoci guda hudu da filaye a Kano da Kaduna da kuma wani gida mai dakuna hudu da kudinsa ya kai Naira miliyan 45 a Legas.
Ana cigaba da bincike game da al’amarin.