Yadda daliban Najeriya a Sudan ke fuskantar tabarbarewar tarbiyya – Ibrahim Aldo

Wane hali ’yan Najeriya ke ciki a kasar Sudan? A matsayina na dan Najeriya mai kishin kasata kuma mai sonta da al’ummarta da kasancewata daya daga cikin masu jagorantar Musulmi a harkokin addini bai kamata in ga wani abu da zai cutar da su duniya da lahirarsu in yi shiru ba. Kuma ina fata in […]

Yadda daliban Najeriya a Sudan ke fuskantar tabarbarewar tarbiyya – Ibrahim Aldo

Wane hali ’yan Najeriya ke ciki a kasar Sudan?

A matsayina na dan Najeriya mai kishin kasata kuma mai sonta da al’ummarta da kasancewata daya daga cikin masu jagorantar Musulmi a harkokin addini bai kamata in ga wani abu da zai cutar da su duniya da lahirarsu in yi shiru ba. Kuma ina fata in amfanar ba in cutar ba. Ba zan fadi wani abu ba domin son rai, ko don cin mutuncin ’yan kasarmu Najeriya. 

Akwai wani labari mai dadi da faranta rai a kan dan Najeriya a baya kafin matsalolin da suke faruwa a yau. A shekarun baya, dan Najeriya a kasar Sudan dan gata ne, ana kallonsa kamar waliyi, mutanen kasar suna girmama shi, masu damararsu da farar hularsu, saboda halayen kwarai da haddar kur’ani da riko da addini da sauransu amma kash, a yau abubuwa sun canja! 

Wadanne matsaloli ne dalibanmu ke fuskanta a Sudan?  

Ana samun wadansu ’yan makaranta da suke bugewa a gidan wadansu lalatattun mata   a can Sudan maimakon karatun da ya kai su, ko kuma su rika sharholiya da ’yan matansu na Larabawa da suke bayyana tsiraici, ’ya’yan malamai ba su tsira ba, ballantana na almajiransu. An taba samun dan wani da ake kallonsa babban malami a Najariya, yana sharholiyarsa da ’yan mata, sai wadansu suka same shi cikin ’yan uwansa dalibai ’yan Najeriya ko zai tsagaita ya daina! Sai ya ce da su, shi fa ko a gida hakan ba komai ba ne a gidansu ya gani ana yi, saboda haka kada su sa masa ido! Idan haka ta faru da ’ya’yan malamai, to me za a ce da ’ya’yan masu hannu-da-shuni ko masu mulki?

Wadansu daga cikin maza masu bin mata sukan samu kansu a cikin kunci a yanayin wuraren da suke rayuwa a Najeriya, saboda ba kowane yaro matashi ne zai nemi ’yan mata da lalata a zuba masa ido ba, a wuraren masu mutunci, sai ta hanyar aure. Ita kuma hanyar aure da wahala ga marasa aikin yi, amma a can ya samu ’yanci babu mai tsangwamarsa, kuma ba mai kula da shi. Su kuma ’yan mata tarbiyyarsu tana lalacewa ne, saboda wadansu da suke fuskantar barazanar fyaden ’yan holewa ne, masu kai wa tsakar dare suna wajen biki da ake kira casu wato party, cikinsu akwai wadanda ake kira ’yan madara ko ’yan lagwada da sauransu.

Wadansu dalibai mata ’yan Najeriya na fuskantar fyade; misali wani dan uwa dalibi ya ce wadansu ’yan mata da wani dan kabu-kabu dan Sudan ya dauke su zai kai su masaukinsu da dare, sai ya yanke hanya da su, ya kira wadansu abokansa a waya suka yi musu fyade har daya daga cikinsu ta dauki juna biyu. Wadansu kuma daga cikinsu sukan bi wadansu ’yan uwansu dalibai ne har dakunan kwanansu da suka kama haya a cikin gari su yi ta kwana da su kamar matansu na aure.

Wadansu kuma talauci ke jefa su cikin mumunan hali, inda tun farko za a yaudaresu da iyayensu cewa karatun kyauta ne, sai sun je su ga ba haka ba ne. Wadansu ’yan siyasa ne ke jefa su cikin matsaloli domin cimma burinsu na siyasa suna cewa; sun dauki nauyin dalibai kaza domin yin karatu a Sudan, inda bayan kai su, to tallafa musu kan gagara, sai dalibai su shiga halin kaka-ni-ka-yi.

Sannan ga miyagun dillalan samar da guraben karatu a kasashen waje da suke jefa sababbin dalibai a cikin matsaloli, kamar yashe musu dan guzurinsu da sunan taimako, ko kuma idan suka samu mata ne, su jefa su a hanyar lalacewa.

Sai kuma matsawar da wadansu iyayen ’yan mata ’yan boko marasa addini da suke kai ’ya’yansu waje da sunan karatun likitanci ko na magunguna ba tare da kula da matsalarsu ba, wadansu ma sukan ce wa iyayensu suna bukatar aure, amma sai su ki, wadansu iyayen ma kan ce da ’ya’yansu su yi komai in ban da daukar ciki! 

Wadansu iyaye ne suke lalata ’ya’yansu ta hanyar shagwaba su da nuna musu wadata cewa su yi komai lokacinsu ne, na kuruciya za su daina nan gaba, sai abu ya fi karfinsu su koma suna neman mafita wadda ba ta bullewa. Saboda haka, ya fi sauki su jefar da su a duniya, ko sun samu hutawa.

Sannan ga shaye-shaye a tsakanin daliban Najeriya maza da mata da suke Sudan, saboda cakuduwa da masu wannan hali tun a nan Najeriya, wadanda ba su iya ba, su koya a wurin wadanda suke kwararru da suka kara samun ’yancin yin haka a waje. Akwai wani dan uwa da ke karatu a Sudan ya ba da labarin wani dalibi da babansa ya ce: “Don Allah kada a yarda a bar shi ya dawo Najeriya ko hutu ne, saboda yaron barazana ne ga rayuwarsa idan har ya dawo saboda shaye-shaye.”

 Yaya batun tsaron dalibai a Sudan?

A Sudan, idan wani abu ya hada dan Najeriya da wani dan kasar Sudan komai gaskiyar dan Najeriya, ba za su ba dan uwansu rashin gaskiya ba, sukan taru su taimaki nasu,   wannan ita ce al’adar Larabawa tun kafin zuwan Musulunci: “Taimaki dan uwanka ya yi zalunci ne, ko an zalunce shi.” Kuma sukan yi kokarin juyar da magana daga yadda take. Akwai wani dan uwa dalibi da wadansu ’yan Sudan ’yan daba da suka so fizge wayarsa ta fadi kasa, suka yi rigen daukarta. Da ba su samu sa’ar daukarta ba, ya dauke abinsa, sai suka ce masa: “Haram, haram! Suka yi masa kururuwa da harshen gargaliyar Larabci suna cewa barawo, barawo! Sai mutunensu suka kama shi da duka.

 Ta bangaren hukuma ma duk abin daya ne. Da aka kama wancan dalibin sai da ya zauna jarun na shekara guda. Wani lokaci ’yan sanda da sojojinsu sukan tsare dalibai ’yan Najeriya da sun gan su da wasu jakunkunan makaranta da suke zaton akwai kudi a cikinsu da sunan bincike. Akwai wani dan uwa da hakan ya faru da shi sau biyu a Khartum, babban birnin Sudan, sa’anan akwai wani abokinsa da ya ziyarce shi a masaukinsa zai koma cikin makaranta bayan Sallar Magariba duhu ya fara, wadansu mutane cikin Rakshah (Keke NAPEP) suka tare shi da bindiga suka karbe masa wayar hannu da yake sauraron karatun Alkur’ani da iya-fes da duk kudin da ke cikin aljihunsa. Cikin ikon Allah da suka so ta da Keke-NAPEP din, ya ki tashi, sai suka mai da masa abin da suka karba.

Shin kun taba kai kukan haka ga ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan?

Akwai tabarbarewar shugabanci a fannin Jakadanci tsakanin Najeriya da Sudan. Da yawa abubuwa suna faruwa na rashin aminci da yaudara daga ofishin Jakadancin Najeriya da ke Sudan wadanda suka yi dalilin zubewar kimar wakilcin da ya kamata a ce ana yi wa ’yan Najeriya da ke Sudan. Misali, idan dan Najeriya ya je Sudan ya kamata duk masu sa hannu da tambari na fasfo da sauran harkokin sadarwa tsakanin gwamnatocin biyu ya zama babu matsala. Amma gwamnatin Sudan ba ta yarda da hakan, sai a ce sai an ga tambarin ofishin Jakadancin Sudan a Najeriya, in ba haka ba sai dai mutum ya sake komawa gida Najeriya. Mukan kai wa ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan koke-koken abubuwan da suke faruwa da ’yan Najeriya musamman dalibai amma sai ofishin ya rika nuna halin ko-in-kula, akwai ma wani a baya da aka ce masa ga matsalolin dalibai sai ya ce, shi ba aikin dalibai ya kawo shi ba.

Kuma na zargin wadansu shugabannin da suka gabata da cewa su suke sa ana yi masu dillancin dalibai mata suna badala da su, saboda haka, ko an kai musu irin wadannan laifufuka sukan karfafa masu yi ta karkashin kasa su shashantar da maganar. Misali akwai wani mutum da aka ce ya shahara a harkar kawalanci ga irin wadancan miyagun shugabanni da yake safarar ’yan matan da ke karatu a jami’o’i don kara bude musu ido, a kasasshen Dubai da katar da sauransu. Wancan mutum (an sakaya sunansa) dan Najeriya ne da ke zaune a Sudan. 

To wace rawa shagabannin kungiyoyin dalibai suke takawa wajen magance wadannan matsaloli?

Akwai Hadaddiyar kungiyar dalibai ta Najeriya da kungiyar Tsofaffin dalibai a Sudan da kungiyoyin siyasa masu wakiltar manyan jam’iyyun siyasa biyu wadanda wadansu dalibai suke wakilta a cikin Sudan, wadanda ’yan siyasa sukan yi amfani da su don cimma burinsu na siyasa. Gaba daya wadancan kungiyoyi, ragamarsu na hannun wadansu daga cikin jami’an jakadanci da hadin hannu da gwamnatin Sudan, ba su da iko su tabo wata matsala da ta dami dalibai sai wadda ta yi daidai da abin da suke so, idan kuma ba haka ba, a murkushe su a kulle ko a daure ko a yi musu barazanar rasa karatu, ko kuma a kulla musu wani mugun abu, saboda haka, shugabanninsu suna jin tsoro. A gefe guda kuma ’yan siyasa da masu rike da sarauta da masu kudi suna taka tasu rawar don ganin sun sanya wadancan kungiyoyi a aljifansu. 

Akwai bayanan da ke cewa akwai tsadar kudin makaranta a Sudan, haka ne?

A shekarun baya, an samu saukin kudin makaranta a Sudan, don haka ake tururuwar zuwa can don karatun fannoni daban-daban. Amma yanzu abubuwan jami’o’insu na neman su fi karfin talaka, musamman a Jami’ar Africa International ta Sudan, wadda wasu kasashe suke tallafa mata, ake samun sauki, amma yanzu suna ta kara kudin makaranta a koyaushe.  Kuma akwai kudaden da gwamnatin Sudan take tatsa a hannun wadanda ba ’yan kasa ba, wadanda suke zaune cikin kunci da matsi, misali; akwai kudin ‘Mu’adalatu Wa Tausikush-Shahadah’ wato: ‘Daitaito da amintar takardun Makaranta,’ wanda kullum karawa ake, wasu ma ana biya ne da Dala. Sai ‘Tasjijul Ajanib,’wato ‘Yin Rajista ga wanda ba dan kasa ba,’ da ‘Ikamah’ wato ‘Izinin zama,’ da ‘Garamah’ wato ‘Haraji’ da sauransu. Wadannan su ne kadan daga cikin matsalolin da ’yan makaranta ’yan Najeriya da ke Sudan suke fuskanta a yanzu.

Kana ganin karancin jami’o’i a Najeriya na taimakawa wajen tura yara kasar Sudan da sauransu?

Idan an kula Najeriya ce kasa mafi yawan jama’a a Afirka, inda wasu masu kididdiga   suka ce, yawan jama’ar Najeriya zai karu daga mutum miliyan 170 ko 180 da aka sani zuwa miliyan 190 zuwa 200 nan da wasu shekaru. Kuma matasa masu son zuwa manyan makarantu su ne suka fi yawa. To idan aka kwatanta da yawan jami’o’in da muke da su a Najeriya na gwamnati da masu zaman kansu da kwalejojin ilimi da sauran manyan makarantu, gaba daya ba za su iya samar da gurbi ga wadannan dalibai ba. kasar Sudan da ba ta kai rabin Najeriya ba, amma jami’o’inta sun ninka na Najeriya, ban da kwalejoji na cikin gida da kasashen waje, akwai cibiyoyin ilimi masu yawa.    

A bangare guda, hukumomi kamar NUC da JAMB da makamantansu suna jawo tarnaki wajen kayyade wasu fannoni da muke da kishin ruwarsu a Najeriya kamar kiwon lafiya, a ce dalibai kaza kawai aka ware wa jami’a kaza. Sannan wata matsalar da ke kawo kwararar ’yan Najeriya zuwa Sudan da wasu kasashe ita ce muguntar wadansu lakcarori marasa kishin kaasa, musamman a matakin Digiri na farko da na biyu da na uku, inda suke gana wa masu karatu ukuba da tozartawa har ana yi wa wasu jami’o’in lakabi da cibiyoyin tsofarwa. Wato idan mutum yana son tsufa da wuri to, ya yi karatu a wadancan jami’o’in, inda zai kwashe shekara 10 ko sama, ba karamar sa’a ba ce ya gama a kasa da shekara goma ga mai Digiri na biyu ko uku.

Abu mafi muni a jami’o’inmu shi ne siyasar ubangida, inda ake samun wadansu malamai sun kasu kamar jam’iyyun siyasa, idan aka gane dalibi yana tare da wani bangare, ko aka sa shi a tsakiya, aka hada masu kula da shi masu mabambantan ra’ayi, an yi ta gara shi ke nan a tsakaninsu!

Ke nan rashin kishin kasa ke janyo wadannan matsaloli?

Mafi rinjayen matsalolinmu suna da dangantaka da rashin kishin kasarmu. Duk dan kasa na kwarai da ya san ya kamata ba zai yi abin da zai jawo kaskanci ga kasarsa ba. Idan mutum ya ga yadda ’ya’yan wasu kasashe suke ba da rayukansu da jininsu da duk abin da suka mallaka don kare mutuncin kasarsu da jama’arsu zai iya haduwa da bakin ciki da hawan jini da wasu cututtuka. Domin wadansu lalatattun ’yan Najeriya babu abin da suke yi ga kasarsu sai jafa’i, sun yarda su watsar da kimarta su gina kansu kawai, sun yarda su kashe ta su raya wata daban, su kwashi dukiyarta sukai wata kaskantacciya! A dauki misali ga kasar Sudan da ’yan Najeriya ke fuskantar tasku da walakanci, wani dan kasar waje bai isa ya ce zai zage ta ba, ko ya zagi dan kasar ko wani abu na mulkin kasar. Yanzu za a yi masa kururuwa, mutane su yi masa taron dangi su yi maganinsa. Sudan a wajen dan Sudan ita ce gaba da komai, ita ce ta daya, in akwai ta biyu, to ita ce Saudiyya sa’annan Amurka. Amma lalattatun ’yan Najeriya ba su damu ba, da yawa masu kudinmu kan kwashe dukiyarsu su kai Sudan da wasu kasashe don nuna kafafa da alfahari! Wannan dukiya ta isa su gina jami’o’i da manyan makarantu da masana’atu da miliyoyin ’yan Najeriya za su amfana.