Yadda dan cirani ya kayar da dan kasa a zaben PDP a Kalaba
Matsalar dan kasa da dan cirani ta taka muhimmiyar rawa a taron jam’iyyar PDP da zaben wakilan ’yan takara a gundumar mazaba ta daya da jam’iyyar ta gudanar ranar asabar din da tagabata. daukacin fadin Jihar Kuros Riba, musamman a layin Bagobiri, wato unguwar Hausawa, sakamakon rashin abin da za a iya bayyana shi da […]
Matsalar dan kasa da dan cirani ta taka muhimmiyar rawa a taron jam’iyyar PDP da zaben wakilan ’yan takara a gundumar mazaba ta daya da jam’iyyar ta gudanar ranar asabar din da tagabata. daukacin fadin Jihar Kuros Riba, musamman a layin Bagobiri, wato unguwar Hausawa, sakamakon rashin abin da za a iya bayyana shi da cewa “rashin hadin kan ’yan Arewa su tsayar da mutum daya tilo da zai wakilci akwatun mazabar a karamar Hukumar Kalaba ta Kudu,inda aka fafata tsakanin Alhaji Garba sarki Lawal da Adamu Muhammad Baba (Adamun master) .
An zargi bangaren Sarkin Hausawan Kalaba da fitowa karar wajen kamfe din su, suna cewa a zo a mara musu baya, dan kasa ya kayar da dan cirani; sannan sun kankane komai, illa dai su da gidansu na sarautar Hausawan Kalaba, lamarin da bai yi musu tasiri ba. Bugu da kari an ce har alfahari suka yi, na cewa yaushe dan cirani zai zo Kalaba ya ja da su. Tun farko ma sai da aka nuna wa ‘yan Arewa cewa idan matukar ba su hada kansu su zabi dan uwansu a wannan kujera ba, to fa nan gaba babu sauran wani dan Arewa mazaunin Kalaba da zai sake neman wani mukamin siyasa: yau ga shi yana neman ya yi tasiri a kan Hausawan.
Mazaba ta daya, wadda ta hada har da unguwar da layin Bagobiri.A mazabar gunduma ta daya. ’Yan takara shida ne suka fito, domin fafatawa, wato uku maza, uku mata. A unguwar Hausawa akwai Alhaji Garba Sarki Lawal, wanda da ne ga marigayi Sarkin Hausawa Alhaji Sarki Lawal, sai kuma Adamu Muhammad Baba (Adamun master). Mazauna unguwar Hausawa sun yi wa cibiyar zaben da ke cibiyar raya al’adu ta tarayya wato cultural centre tsinke, domin zabar wanda ran su ke so.
Tun kafin a gudanar da zaben Aminiya ta tattauna da ’yan takarar biyu, wato Adamu Muhammad Baba da kuma Alhaji Garba Sarki Lawal.
“Shi ba a saye shi da kudi ba, domin ya janye wa abokin takara. Na fi so a shiga fagen fama a fafata, kuri’a ta yi halinta; ni ba zan janye wa kowa ba,” inji shi. Shi kuwa Adamu Muhammad Baba da aka tambaye shi wane kwarin gwiwa yake da shi na kayar da abokin takararsa lura da cewa su ke rike da sarautar layin Bagobiri, wato unguwar Hausawa sai ya ce: “Dogara ga Allah da kuma yawan jama’a da suka tsaya kai da fata su ga cewa na lashe zabe ya sanya nake da kwarin gwiwa in Allah ya yarda zan ba mara da kunya, tunda suna kiran mu da ’yan cirani. Ba mu isa mu ja da su ba, su ’yan kasa ne. shi ne jama’a suka taru, suka ce yau za su nuna wa duniya cewa dan cirani a Kalaba yana da tasiri. Wannan ita ce hujjata ta ganin zan iya lashe zabe; na ma fi so a je fagen fama kuri’a ta raba mana gardama,” a cewar Adamu master.
Sakamakon zaben ya yi nuni da cewa, Adamu Muhammad Baba dan cirani ya kayar da Alhaji Garba Sarki Lawal da yawan kuri’u 250, inda shi kuma ya samu kuri’u 68. Bayan da jami’in zabe Honarabul Effiom Effion ya bayar da sakamako ya ce “bisa dama da kuma ikon da hukumar da ta shirya wannan zabe ta ba ni, ga yadda sakamakon kowane dan takara ya samu Francis Asukuo 34; Aishatu Haliru 181; Nkoyo 94; Ndubuidsi 105.
Wadanda aka zaba za su shafe shekara hudu suna rike da mukamin wakilan da za su rika yi zaben duk wani dan takara mukamin ’yan majalisun tarayya da kuma majalisar jihar, har zuwa ma na gwamna. Da aka kammala fadar sakamakon zabe, wakilinmu ya tuntubi Alhaji Amadu Sarki Lawal kakakin dan takarar da aka lika da kasa, kan gamsuwarsu da sakamakon, sai ya ce “ba mu gamsu ba, domin ai ba zabe aka yi ba, wadanda ba su cancanta ba aka tsayar takara, an kori jama’ar mu da suka zo kada mana kuri’a. Ina fa aka yi zabe, anyi son rai.”
Shi kuwa wanda ya lashe zaben da gagarumin rinjaye ya gode wa Allah da kuma jama’ar da suka shafe tsawon wunin ranar da aka yi zaben, domin su ga sun cimma burinsu, inda ya hori sauran abokan takara su mayar da wuka kube, su zo a hada karfi da karfe, domin jam’iyyar PDP a Kuros Riba da kasa baki daya ta yi nasara.