Yadda dan dako ya zama babban lauya
Babban Lauyan Najeriya Yunus Ustaz Usman, dan kabilar Igala ne daga Jihar Kogi, shi ne na biyar a jerin Manyan Lauyoyin Najeriya daga yankin Arewa. Ya zauna a karkashin Babban Lauyan Najeriya na farko daga Arewa, Alhaji Abdullahi Ibrahim da kuma tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Lawal Uwais. A wannan hira, ya yi […]

Babban Lauyan Najeriya Yunus Ustaz Usman, dan kabilar Igala ne daga Jihar Kogi, shi ne na biyar a jerin Manyan Lauyoyin Najeriya daga yankin Arewa. Ya zauna a karkashin Babban Lauyan Najeriya na farko daga Arewa, Alhaji Abdullahi Ibrahim da kuma tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Lawal Uwais. A wannan hira, ya yi wa Aminiya bayanin rayuwarsa da yadda ya yi gwagwarmaya, har ya kai matsayin babban lauyan Najeriya (SAN). Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Mene ne tarihinka?
An haife ni shekaru 57 da suka wuce, a gona da tsakar rana. Iyayena matalauta ne. Na yi dako da leburancin ginin kasa tare da kawuna a kauyenmu, na yi itace ina sayarwa a kwauyenmu da ke Igeme a kasar Igala, don in biya kudin makaranta ko in sayi kayan makaranta. Bayan na kammala sakandare sai na yi karatu a Kwalejin horar da ma’aikata ta tarayya (FTC) da ke Malali Kaduna, inda na koyi buga keken rubutu, daga nan sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ina karatun difloma na samu sakamako mai darajar “A”. Amma Shugaban tsangayar Shari’a, Alhaji Baba Shani ya ki yarda in tsallake zuwa digiri, inda ya ce tunda na fara difloma sai na kammala, sannan zan fara digiri. Sai ya zamo mini alheri, don ya sa na fahimci Shari’ar Musulunci, sannan na karanci Shari’ar Bature.
Bayan na kammala jami’a sai kawuna, wanda kuma shi ne babban lauyan Najeriya na farko a yankin Arewa, Alhaji Abdullahi Ibrahim ya hada ni da amininsa, wanda a lokacin yana shari’a a kotun koli da ke Ikko, Mai Shari’a Muhammad Lawal Uwais, wanda ya sauya mini rayuwa matuka, don ya ba ni masaukin bakinsa na zauna. Da gulob din lantarkin dakina ya mutu, ya zo dakina ya hau kujera da kansa ya canza mini. Abin ya ba ni mamaki matuka. Akwai ranar da na dawo daga fati (gidan rawa) da karfe uku na dare, ashe yana karatu kuma ya ga shigowata, sai ya dauko abinci daga kicin da kansa ya kawo mini. Har ila yau, akwai ranar da na fito zan tafi makarantar horar da lauyoyi, ashe ya ga fitowa ta, sai na ji an ce, “Yunusa ina kwana”. Uwais mutum ne mai karamci matuka.
Na bude ofishina ne a watan Nuwamba 1989. Sannan daya daga cikin shari’un da suka sa na shahara ita ce wacce na yi tsakanin Ila Alkamawa da Bello, wadanda makwabta ne, daya dan Izala ne, dayan kuma dan darika. daya ya so ya sayar da gidansa, inda dayan ya ce lallai sai an sayar masa. Da na je kotu sai na ce ai babu tilastawa a cikin addini, don Malikiyya muke bi. Haka ya sa na ci shari’ar, inda kotu ta yarda kowa na iya sayar da gidansa ba tare da ya sayar wa makwabcinsa ba.
Aminiya: Yayin da Saminu Turaki da Adamu Alieru da Aliyu Shinkafi da Isa Yuguda da Ministan Abuja Bala Muhammad suka bar ANPP suka shiga PDP, PDP ta yi ta murna, amma da PDP ta yi asarar sanatoci yanzu sai ta ce ba a yi mata daidai ba?
Ai su ANPP ba su je kotu don hana fitar ba. Akwai shari’ar da aka zartar a watan Oktaba na karar da bangaren Baraje ta shigar, inda kotu to ce babu baraka a PDP. Har yanzu babu wanda ya daukaka kara, har lokacin daukaka karar ya wuce, don watanni shida ne. Amma sai batanci ake yi wa alkalin a shafukan jaridu.
Aminiya: Ko Shugaba Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a zabe mai zuwa?
Yana iya tsayawa takara, domin sashi na 135 da na 137 ya ce, “Idan ka taba takara ka ci zabe har sau biyu ba za ka kara tsayawa takara ba.” Jonathan ya taba takara sau daya ne kacal. Shekaru biyun da yake mataimakin marigayi Umaru Yar’adua wannan ba shi aka zaba ba. Mutane na cewa ko ni dan PDP ne. Ni lauya ne, don ina kare mutane a kotu daga kowace jam’iyya. Babu wata jam’iyyar da ta burge ni da zan shige ta a yanzu.
Aminiya: Me ya sa ake taron kasa bayan ga majalisar kasa?
Na fadi a kasida cewa, in dai har majalisar dokoki na kasa na nan, ba za a yi mata kishiya ba. Taron bai wuce matsayin kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa ba, don ya mika wa majalisar dokoki ta kasa da burin zama doka. Shugaban na iya yarda da shawarwarin ko kuma ya jefa a kwandon shara. Kuma ba lallai ba ne majalisar ta yi aiki da kudurin da aka aika mata.
Aminiya: Shin akwai tsarin jin ra’ayin jama’a a kundin tsarin mulkin 1999?
A’a, babu wannan tsarin sam-sam.
Aminiya: Me ya sa Mai sharia Idris Kutigi ya karbi jagorancin taron?
Ai taro ne na ba da shawara ga shugaban kasa, don haka a matsayinsa na masanin shari’a, zai yi aikin da ya dace.
Aminiya: Me ya sa Najeriya ba ta daukaka karar da kotun duniya ta yanke ba dangane da kwace yankin Bakassi?
Na sha fadi cewa bai dace ba Najeriya, a karkashin Olusegun Obasanjo, ta ba da Bakassi ga kasar Kamaru. Domin Ingila da ta yi kyauta da yankin ba ta yi daidai ba, domin wannan yankin ba mallakinta ba ne. Matsalata ga shugabannin Najeriya ita ce girman kai, don ba sa jin shawara. Mutanen Bakassi ba za su taba yafe wa Obasanjo ba, don ya jefa su a cikin wahala.
Aminiya: Shin me ya sa wadanda suka saci miliyoyin kudi sai a yi shekaru ba a gama shari’arsu ba, amma wanda ya yi yankan aljihu ake kammala shari’arsa a cikin mako guda?
Akwai matsaloli da yawa. Don ana neman shaidu da dama kafin a gamsar da mai shari’a, ko kuma ya yi watsi da shari’ar. Amma ina bakin ciki da masu shigar da kara maimakon su karbi kudin da aka sata ta hanyar yankan aljihu a mayar wa mai shi, sai a kai mai sanen gidan yari, wanda yana haddasa cinkoso a gidajen yarin kasar nan.