Yadda dan jaridar Faransa ya yi kutse cikin masu ‘jihadi’

Wani Musulmi dan jarida da ya lakaba wa kansa sunan Sa’id Ramzi ya samu nasarar kutsawa cikin masu ‘jihadi’ a karkashin kungiyar ISIS, inda ya rika daukar hotunan bidiyonsu a boye lokacin da suke tsara kai hare-hare da sunan kungiyar kafin a kama su.Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa Ramzi ya tsara wani […]

Yadda dan jaridar Faransa ya yi kutse cikin masu ‘jihadi’
Yadda dan jaridar Faransa ya yi kutse cikin masu ‘jihadi’

Wani Musulmi dan jarida da ya lakaba wa kansa sunan Sa’id Ramzi ya samu nasarar kutsawa cikin masu ‘jihadi’ a karkashin kungiyar ISIS, inda ya rika daukar hotunan bidiyonsu a boye lokacin da suke tsara kai hare-hare da sunan kungiyar kafin a kama su.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa Ramzi ya tsara wani rahoton musamman mai suna “Sojojin Allah” inda ya kawo yadda matasa masu ‘jihadi’ suke gudanar da ayyukansu kuma an nuna fim din da ya shirya kan hakan a ranar Litinin da ta gabata a Faransa.
Ramzi wanda ya ce kusan sa’anni suke da ‘masu kisan’ da suka kai harin 13 ga Nuwamba da ya hallaka mutum 130 a Faransa ya shaida wa AFP cewa, “Burina in gano mene ne tunaninsu. Kuma daya daga cikin manyan darussan da na koya ban ga wani Musulunci a cikin ayyukansu ba. Kuma ba su da wata niyya na inganta duniya. Abin da kawai suke fama da shi shi ne matasa ne masu asara da damuwa da kunar bakin wake da kuma yadda ake saurin juya tunaninsu.”
“Sun yi rashin sa’ar an haife su a lokacin da ISIS ta bayyana. Abin bakin ciki ne, su matasa ne da suke neman wani abu kuma shi suka samu,” inji shi.
Ramzi ya ce mataki na farko na haduwa su mai sauki ne ya yi haka ta hanyar bibiya da tattaunawa da masu da’awar jihadi a shafin Facebook. Daga nan sai ya gana da wanda suka gabatar da shi a matsayin ‘Amir’ din wasu matasa wadanda wasu an haife su Musulmi da wadanda suka tuba. Ya ce wannan ya gudana ne a wani wuri a Chateauroud, wani gari da ke tsakiyar yammacin Faransa.
Ya ce ‘Amir’ din wani matashin Bafaranshe ne dan asalin Turkiyya mai suna Oussama, kuma  a ganawarsu ta farko ya yi kokarin shaida masa cewa an san shi da Abu Hamza, kuma Aljanna tana jiransa (dan jaridar) idan ya yi kunar bakin wake.
Ya ce shaida masa yana murmushi cewa: “Wannan hanya c eta Aljanna. dan uwa zo mu tafi Aljanna, matanmu suna jiranmu a can tare da mala’iku a matsayin masu yi mana hidima. Za ka samu mazauni da kayan karau na lu’u-lu’u da murjani.”
Ya ce a lokacin da wani mai suna Abu Suleiman ya dawo daga Rakka hedkwatar ISIS a Syria ya bukacin dan jaridar ya hadu da shi a wata tashar jiragen kasa, amma da ya je bai same shi ba, sai wata mace sanye da nikabi ta mika masa wata wasika wadda ta kunshi tsarin yadda za a kai hari a wani kulob din dare a yi ta ‘harbi har mutuwa,’ kuma a jira jami’an tsaro sannan a tayar da bama-bamai. Sai dai kafin lokacin jami’an tsaro sun kama galibin ’ya’yan kungiyar kuma daya daga cikinsu da ya tsere sai ya aiko masa da sakon “Ka cika mutum.” Kuma “A nan ne na kawo karshen kutsen da na yi musu.”

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi