Yadda dan Kasuwa Usman Sarki ya bayar da gudunmuwar kujerun makaranta 125 a Katsina

An baiwa daliban karamar makarantar sakandire ta Je-ka ka dawo da ke Kofar Yandaka da ke cikin babban birnin Jihar gudunmuwar kujerun zama masu hade da tebura guda dari da ashirin da biyar (125) ga azuzuwa biyar da ke cikin makarantar. Dokta Muhammadu Usman Sarki, ne ya shaida haka a madadin shi Alhaji Usman Sarki, […]

Yadda dan Kasuwa Usman Sarki ya bayar da gudunmuwar kujerun makaranta 125 a Katsina

An baiwa daliban karamar makarantar sakandire ta Je-ka ka dawo da ke Kofar Yandaka da ke cikin babban birnin Jihar gudunmuwar kujerun zama masu hade da tebura guda dari da ashirin da biyar (125) ga azuzuwa biyar da ke cikin makarantar.

Dokta Muhammadu Usman Sarki, ne ya shaida haka a madadin shi Alhaji Usman Sarki, da zuri’arsa a wajen bikin sanya sunaye ga wasu sassa na makarantar da ake cewa, “House” a turance wanda aka yi a jiya Alhamis a harabar makarantar da ke bisa hanyar zuwa Batsari.

Dattijon dan kasuwar Alhaji Usman Sarki, na daga cikin mutane uku da aka sanya sunayensu a sassan makarantar domin tunawa da shi akan irin gudunmuwar da yake bayarwa domin ciyar da ilmi gaba a cikin Jihar wanda ya hada da na addini da na boko wanda wannan makaranta na daga cikin wadanda suke amfana da ita, kamar yadda Shugaban makarantar Malam Ibrahim Abubakar ya shaidawa jama’ar da suka gaiyato domin shaida wannan bikin.

“Alhaji Usman Sarki, mutun ne wanda yasan darajar ilmi ba wai ga yaransa kawai ba har zuwa ga sauran jama’a in aka duba da irin hidimomin da yake yi da dukiyarsa ta wannan fuska. Makaranta tayi nazari sosai ta yadda zata rika tunawa da wannan bawan Allah shi yasa muka yanke hukunci sanya sunansa ga wannan sashe wanda ya kunshi azuzuwa domin nuna gamsuwa da irin kulawar da yake bamu”.

Har ila yau, a can baya, shi ne mutum na farko da ya gina makarantar sakandire mai bene ta Islamiya mai hade da masallaci mai suna AL-ILHAM da ke Kofar Guga, makarantar na koyar da fannonin biyu, wato, na addini da na zamani ya kuma mikawa al’umar garin Katsina da ke wayenta kyauta domin ilmantar da yara.

Kazalika, ya sake gina wata makarantar ta biyu a tsohuwar kasuwa acikin garin na Katsina. Sauran wadanda aka sanya sunayen su sun hada da Hajiya Zainab Dari tsohuwar Kwamishinar harkokin mata a jahar da kuma Farfesa Mardiya Sanusi Rafindadi.