Yadda dan Najeriya ya bata wa Real Madrid ruwa a La Liga
Chukwueze ya maimaita irin tarihin da Diego Forlan ya kafa a watan Mayun 2006.
Dan wasan Najeriya, Samuel Chukwueze da ke taka leda a Villarreal ya taimaka wa kungiyar wajen doke Real Madrid da ci 3-2 a gasar La Liga.
An buga wasan ne ranar Asabar a gidan Madrid wato Santiago Bernabeu.
- Zulum ya kaddamar da fara gina gadar sama ta biyu a Borno
- Messi ya zarce Ronaldo yawan cin kwallaye a tarihi
Tun da farko dan wasan Villareal Pau Torres ya yi kuskuren cin gida a minti 16 da fara wasa.
Amma a minti na 39 Chukwueze ya danna cikin gidan Real Madrid ya zura musu kwallo.
A minti na 48, Real Madrid ta sake zura kwallo a ragar Villarreal ta hannun Vinicius Junior.
Sai kuma a minti na 71 lokacin da Jose Luis Morales ya zura kwallo a ragar Madrid, lamarin da ya mayar da wasan 2-2.
Karawar ta ci gaba a haka har lokacin da Chukwueze ya harba kwallo a ragar Madrid a minti na 80, lamarin da ya bai wa Villarreal nasara a gidan Madrid.
Da wannan rawar da ya taka, Samuel Chukwueze ya zama dan wasan Villarreal na biyu da ya ci kwallaye biyu a gasar La Liga a gidan Real Madrid wato Santiago Bernabeu, bayan Diego Forlan ya kafa irin tarihin a watan Mayun 2006.
Wannan sakamakon dai ya kara saka Madrid cikin rashin tabbas a kokarinta na sake kare kambun Gasar La Liga a bana.
Babbar abokiyar hamayyarta, Barcelona tana ta daya a teburi da maki 71, yayin da Real Madrid ke bin ta da maki 56.
Ita kuwa Villarreal tana ta biyar a teburin da maki 47.