Yadda dan sanda makaho yake gudanar da aikinsa
Pan Young wani dan sanda ne da ke fama da lalurar makanta. Makahon wanda yake aiki da rundunar ’yan sandan kasar China, ya rasa idanunsa ne bayan ya yi fama da ciwon Glaucoma a shekarar 2002, kamar yadda kafar yada labaran kasar wato People’s Daily ta bayyana. Pan wanda ya cika shekara 43 da haihuwa […]
Pan Young wani dan sanda ne da ke fama da lalurar makanta. Makahon wanda yake aiki da rundunar ’yan sandan kasar China, ya rasa idanunsa ne bayan ya yi fama da ciwon Glaucoma a shekarar 2002, kamar yadda kafar yada labaran kasar wato People’s Daily ta bayyana.
Pan wanda ya cika shekara 43 da haihuwa a bana, yana aiki ne a wata tashar jiragen kasa da ke kauyen Ci Chong, inda kuma yake kula da wasu kauyuka 13 da layin dogon, mai tsawon Kilomita 38, ya ratsa ta cikinsu.
Kuma bana shekara 10 ke nan, ba tare da samun wani korafin aikata babban laifi ba daga yankin da ke karkashin kulawarsa. Ana ganin dai wannan nasarar ba ta rasa nasaba da agajin da yake samu daga bangaren mai dakinsa, mai suna Tao Hongying, wadda ya aura a shekarar 2004.
Tao mai shekara 46 da haihuwa, tana aiki ne da wani kamfani da ke aikin samar da tsaro a tashar jirgin kasan. Hakan ya sa suke jerawa da mai gidan nata duk lokacin da zai fita sintiri a kullum.
Da aka tambaye shi dangane da yadda yake gudanar da aikinsa, Makahon ya ce: “Na yi amannar cewa babban amfanin rayuwar dan Adam shi ne, mutum ya yi wa kasarsa hidima a duk halin da ya samu kanta. Ba na iya ganin jiragen a yanzu, amma ina iya jin kukansu a kodayaushe.”