Yadda dan shekara 110 ke zaman kadaici a Saudiyya

Wani dattijo dan shekara 110 a kasar Saudiyya, mai suna Abdul Aziz bin Abdullah Ahmad Saeed da ake yi wa lakabi da Abu Zaki yana zaune shi kadai a gidan gonarsa da ke Al-Ahsa, inda yake cin gashin kansa, ba tare da wani mai taimaka masa ba. Wannan tsoho ya yi tukin mota na tsawon […]

Yadda dan shekara 110 ke zaman kadaici a Saudiyya
Yadda dan shekara 110 ke zaman kadaici a Saudiyya

Wani dattijo dan shekara 110 a kasar Saudiyya, mai suna Abdul Aziz bin Abdullah Ahmad Saeed da ake yi wa lakabi da Abu Zaki yana zaune shi kadai a gidan gonarsa da ke Al-Ahsa, inda yake cin gashin kansa, ba tare da wani mai taimaka masa ba.

Wannan tsoho ya yi tukin mota na tsawon shekara 62, ba tare da ya taba yin hadari ba; ya kuma daina tukin ne saboda dundumi ya kama idanunsa kwanan nan. Duk da tsufa da ya kama Abu zaki, har yanzu yana cin gashin kansa, inda yake dafa abincinsa da kansa, ta hanyar amfani da kayan miyar ganyayyakin da ya noma da hannunsa. Kuma ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya saboda yana cin naman gada da korayen ganyayyaki.
Mafi yawan mutane sun dauka cewa, tsofaffin da shekarunsu suka kai 90 suna da tarina bokai da ’yan uwa. Sai dai abin takaici shi ne, Abdul Aziz bin Abdullah Ahmad Saeed, wanda aka fi sani da Abu Zaki, mutum ne da ke zaune cikin kadaici daidai lokacin da ya cika shekara 110. Abu Zaki yana zaune ne a gonarsa da ke Al-Ahsa tsawon shekara 25, sai dai a wasu lokutan matansa da ’ya’yansa kan ziyarce shi.
a lokacin da yake ganiyar kuruciyarsa, wannan dattijo ya yi aikace-aikace da dama, wadanda suka hada da kula da dawakai da kanikanci da kamfanin hakar mai na Aramco da kidan badujar sojan kan iyaka.
Da yake tuna irin wahalhalun rayuwa da ya sha, Abu Zaki ya tuna aikin tuki da ya yin a tsawon shekara 29, ya kuma yi nesa da iyalansa, kuma yakan hau rakumi daga Al-Ahsa zuwa katif.
Da aka tuntube shi kan batun al’adun aure a da, ya ce ya bai wa matarsa sadakin Riyal 80 da akuya babba, kuma al’adun da ba a kashe kudi masu yawa, kamar yadda ake yi a bukukuwan auren wannan zamanin.
“Idan talaka na son aure, kuma ba shi da kudi ko gida, mutane ne ke tara masa kudin da ake bukata,” inji shi.
Wannan tsohon manomi ya rasa ’ya’yansa 15, sannan ya sha yin aikin hajji da umra, ineda a da yake zuwa Makka a kan rakumi, daga baya ya samu tsofaffin motoci. Sai dai ya ce bai taba fita daga masarautar Saudiyya ba, kuma ba shi wata matsala ta rashin lafiya.
Wani bincike da aka gudanar kan masu nisan shekaru da suka zarta 90 cikin koshin lafiya, an gano cewa, suna da dimbin Bitamin A da E damfare a jikinsu, al’amarin da aka alakanta da koshin lafiya da nisan shekarunsu.