Yadda dan shekara 12 ya zama Wakilin Masarauta a Nassarawa
Dagacin Tudun Wada da ke karkashin Masarautar Karshi a Karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nassarawa, Alhaji Abubakar Abdullahi Bako, ya nada yaro mai shekara 12 a matsayin Wakilin Madaki a masarautar bayan amincewa da hakan da ’yan majalisarsa suka yi. Wanda aka nada mai suna Fahad Abdullahi Bodejo dan Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal […]
Dagacin Tudun Wada da ke karkashin Masarautar Karshi a Karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nassarawa, Alhaji Abubakar Abdullahi Bako, ya nada yaro mai shekara 12 a matsayin Wakilin Madaki a masarautar bayan amincewa da hakan da ’yan majalisarsa suka yi.
Wanda aka nada mai suna Fahad Abdullahi Bodejo dan Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Kasa ne, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo wanda shi kansa ke rike da sarautar Sarkin Fulanin masarautar.
Da yake jawabi a yayin bikin nadin wanda ya gudana a ranar Juma’ar da ta gabata a fadar Dagacin, Dagacin na Tudun Wada ya ce, ya bai wa yaron sarautar ce bisa la’akari da cancantarsa kasancewar ya gaji sarautar daga bangaren mahaifiyarsa, sannan ya nuna godiya a kan ayyukan ci gaba da mahaifinsa ya kawo ga al’ummar Gwandarawan Tudun Wada da suka hada da gina masana’anta da makarantar marayu da kasuwa, inda ya ce hakan ya samar da ayyukan yi ga jama’arsa. Sai ya hori sauran masu hannu da shuni da ke garin su yi koyi da abin da ya yi.
A jawabin da ya yi, mahaifin yaron, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo wanda ya tabo tarihin dangantakarsa da masarautar, ya bayyana al’ummar yankin a matsayin masu son zaman lafiya da sauran jama’a. Ya ce mahaifiyar dansa Fahad ta fito ne daga gidan marigayi Sarkin Karshi Muhammadu Bako sannan shi kansa ya aurar da kanwarsa ga iyalan gidan don kyautata zamantakewa da kuma karfafa zumunci a tsakaninsu.
“Saboda haka ina horon Fulani da ke da zama a wannan gari ku auri ’ya’yan kabilar Gwandara matukar suna da kyan hali,” inji shi.
A jawabin godiya, Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Kasa, Alhaji Sani Juli, ya yi fatan ci gaban zaman lafiya a yankin da kuma kasa baki daya. “Al’ummar Fulani makiyaya da manoma suna bukatar juna a kan sana’o’insu,” inji shi. Sai ya bukaci su rika kai zukata nesa a duk lokacin da aka samu rashin jituwa ta hanyar kai korafi a gaban shugabanni ko kuma hukuma maimakon daukar mataki na kai-tsaye.