Yadda dan shekara 7 ya kubuta daga hannun masu garkuwa a Katsina

A yammacin ranar Talatar da ta gabata ce rundunar ’yan sandan Jihar Katsina bisa jagorancin Kwamishina Sanusi Buba ta gabatar wa manema labarai wadansu mutane da take zargi da satar wani yaro dan shekara 7 mai suna Abdurrahman Sama’ila da ke garin Runka a Karamar Hukumar Safana a jihar. Kakakin Rundunar SP Gambo Isa ya ce, […]

Yadda dan shekara 7 ya kubuta daga hannun masu garkuwa a Katsina

A yammacin ranar Talatar da ta gabata ce rundunar ’yan sandan Jihar Katsina bisa jagorancin Kwamishina Sanusi Buba ta gabatar wa manema labarai wadansu mutane da take zargi da satar wani yaro dan shekara 7 mai suna Abdurrahman Sama’ila da ke garin Runka a Karamar Hukumar Safana a jihar.

Kakakin Rundunar SP Gambo Isa ya ce, rundunar ta yi nasarar kama Jazuli Ayuba da Abubakar Aminu da Jibrin Sa’idu dukkansu mazauna kauyen Kadanya da Haruna Sale da ke cikin garin Runka tare da hadin gwiwar wadanda suka tuba kuma suka yi alkawalin bayar da tasu gudunmawar don kawo karshen ta’addancin da ake yi.

Kakakin ya ce wannan kamu ya biyo bayan sako yaron da matsaran suka yi kimanin wata da ya wuce, bayan sun karbi kudin fansa Naira dubu 25.

Da yake karin haske kan yadda suka saci yaron, Abubakar Aminu ya ce Haruna ne ya zo ya same shi ya ce su dauke yaron za a samu kudi “Mun zo mun amshi bindiga wajen Jazuli bayan na fada maaa abin da za mu yi. Bayan mun dauko yaron na samu Jibrin Sa’idu na shaida masa cewa yaro na hannu. Shi ya ba mu wayarsa don kiran mahaifin yaron amma sai lambar ta ki shiga. Sai na je na tuntubi wani mai suna Kabiru don in samu lambar Sama’ila bayan na shaida wa Kabiru abin da ake ciki. Ya ba ni lambar amma ya ce kada in nuna wajensa na same ta,” inji shi.

Abubakar ya ce, sun ci gaba da magana da mahaifin yaron inda suka nemi ya biya su Naira miliyan biyu, inda karshe suka amshi Naira dubu 25, “Mun kai yaron can cikin dajin a wani kangon gidan wani Bafulatani.

Abubakar ya ce sun yanke shawarar karbar Naira dubu 25 ne bayan sanarwar da Gwamna Masari ya bayar cewa duk wadanda suke tsare da wadansu don karbar kudin fansa su sake su a cikin kwana biyu ba tare da wani sharadi ba ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Mahaifiyar yaron mai suna Binta ta ce ta ga mutane kawai sun shigo cikin gidan wadanda kuma babu wanda ta sani daga cikinsu, sun kuma nufi inda yaron yake.

“Sun tayar da shi daga barci suka ce ya je ya sanyo takalminsa. Da na tamabaye su ko lafiya? Sai suka ce wai raka su zai yi ba wani abu ba. Bayan na yi salati na ce, yanzu tafiya za ku yi da shi? Sai wani daga cikinsu ya mare ni bayan na rike yaron na ce, ba zai je ko’ina ba. Ina ji ina gani suka tafi da shi da karfi,” inji ta.

Malam Bashir Jafaru abokin mahaifin Abdurrahman ya ce, “Washegarin da abin ya faru, na shigo cikin garin sai na ji ana labarin cewa an dauke wani yaro dan gidan Sama’ila Mai Dankali. Bayan na tuntube shi ya tabbatar min, an yi magana ta waya har an daidaita, sai yake nuna mini cewa ba ya da wanda zai je ya kai kudin. In taimaka in je na kuma yarda bayan ya shaida mini sun ce wanda zai je ya sanya bakaken kaya tunda da dare ne za a je. Bayan na je sai suka zo suka same ni suka karbi kudin suka kirga, bayan sun ga sun cika, sai suka ce in koma wajen babur dina in tsaya. Na tsaya jim kadan sai suka kawo yaron na dauko shi muka dawo gida.”

Kakakin Rundunar ’Yan sanda SP Gambo Isa ya ce da zarar sun gama bincike za su gabatar da su a kotu.