Yadda dangantaka tsakanin Ali da Zango ta sukurkuce bayan shekara 14

Masu iya magana sukan ce kaddara ta riga fata musamman ma idan wani abu marar dadi ya faru, tabbas haka ne domin a makon jiya ne wutar rikici ta tashi tsakanin jarumi Adam Zango da Rahama Sadau, rikicin da ya kawo salwantar kyakkyawar dangantaka ta tsawon shekara 14 tsakanin fitaccen jarumi Ali Nuhu da kuma […]

Yadda dangantaka tsakanin Ali da Zango ta sukurkuce bayan shekara 14
Yadda dangantaka tsakanin Ali da Zango ta sukurkuce bayan shekara 14

Masu iya magana sukan ce kaddara ta riga fata musamman ma idan wani abu marar dadi ya faru, tabbas haka ne domin a makon jiya ne wutar rikici ta tashi tsakanin jarumi Adam Zango da Rahama Sadau, rikicin da ya kawo salwantar kyakkyawar dangantaka ta tsawon shekara 14 tsakanin fitaccen jarumi Ali Nuhu da kuma Adam Zango din.

Zango ya bayyana cewa ya yanke alakar da ke tsakaninsa da Ali Nuhu cikin wata hira da ya yi da Aminiya a ranar Asabar. Ya ce ba zai yarda ya ci gaba da alaka da maigidansa ba, saboda ba zai yarda da tafiyar da babu gaskiya a cikinta ba.
Wutar rikicin ta barke ne a makon jiya bayan Rahma ta shiga turakarta ta Istagram ta gasa wa Zango bakaken maganganu saboda ya cire ta a sabon fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta’, wanda tuni aka fara daukarsa. Duk da cewa daga baya jarumar ta ba jarumin hakuri amma wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, kasancewar wani dan gani kashe nin Zango mai suna Ali Artwork ya rama wa ubangidansa zagin da aka yi masa, inda ya yi wa Ali Nuhu tatas. Hakan ya sanya yaran Ali Nuhu wadanda suka hada da Garzali Miko da Shamsu dan’iya da sauransu suka kai karar Ali Artwork, aka hada su da ’yan sanda don a kama Ali Artwork, amma ba su same shi ba, a nan aka kama iyayensa. Daga baya ya kai kansa bayan mahaifiyarsa ta yi barazanar tsine masa. An ci gaba da tafka rikici daga baya dai aka sasanta.
Kwatsam sai Zango ya bayyana ya yanke duk wata alaka tsakaninsa da Ali Nuhu.
Ya ce: “Yau rana ce da zan fadi abin da al’umma ba su sani ba, domin suna yi mini kallon ni yaron Ali Nuhu ne. Wannan kalma mai suna yaro a wurin Ali ni ne na dauka na dora masa, na kuma ce shi ubangidana ne. A shekara 14 da nake fim a industiri, sunana ya yadu a duniya, ni nake yi wa Yakubu Muhammad da Abubakar Sani da Sadi Sidi Sharifai da Mudassir kassim da Adam Kirfi da Adamu Nagudu da sauransu kida. Sunana ya shiga duniya.”
Ya ce a wancan lokaci ya bukaci furodusoshi su sanya shi a fim amma suka ki, har sai da ya tara kudi ya yi wa kansa fim mai suna ‘Surfani’, daga nan furodusoshi irin su Bauni da Ali Nuhu da Najjashi SB Jakara suka fahimci yana da hazaka za su iya sa shi a fina-finansu.
“A wannan lokaci ne Najjashi ya yi mini fim mai suna ‘Misali’, Bauni ya yi mini ‘Dukiya’, Ali Nuhu kuma ya yi mini ‘Zabari’, saboda haka a wancan lokacin sai na dauki wadannan mutane a matsayin iyayen gidana, amma sai na fifita Ali a kansu, saboda a wancan lokacin shi ne ya yi mini fim din da na fi suna. Wannan dalilin ya sa na dauki suna na ba shi na matsayin mai gidana, ba wai don wani abu ba. Don haka ina so duniya ta sani cewa ni na yi wa kaina komai a masana’antar fim kafin wani ya taimake ni.” Inji Zango.
Ya bayyana cewa ya kasance mai yi wa Ali nuhu biyayya, sama da shekara goma sha biyu, “A yanzu Allah Ya kai ni wani matsayi irin nasa (Ali). Duk inda na je za a ce ga Zango ga Ali Nuhu, amma hatta in tafiya za mu yi ni nake daukar jakar Ali Nuhu in rike. Amma duk da haka yaran da ke zagaye da shi babu wanda ba ya cin mutuncina, ya yi mini rainin da ya ga dama. Na yi wa Ali Nuhu korafi babu adadi, ya yi musu fada amma kuma babu wanda ya gyara hakan.
“Ni kuma na rantse da Allah a cikin kannena da mu ke uwa daya uba daya da yara da ke karkashina babu wanda ya isa ya zagi Ali Nuhu ya zauna lafiya tare da ni, su sun san wannan. Don haka ni ban ga dalilin ni ina girmama shi, yarana na girmama shi, amma shi kuma ba zai kasance yaransa su girmama ni ba, saboda haka babu wani amfani mu ci gaba da tafiya mu na munafuntar junanmu. Amma daga rana mai kamar ta yau ni da Ali Nuhu sunanmu jarumai a industiri, amma dangantakar da suka sani tsakani na da shi ni na yanke ta.” Inji shi.
Batun ko shi ya tura Ali Artwork ya zagi Ali Nuhu sai ya ce “Wallahil Azim! Billahil lazi la’ilaha illa huwa ban sa Ali artwork ya zagi Ali Nuhu ba. Abin da na sani kawai shi ne Ali Artwork yaro ne mai biyayya, wanda komai zai iya yi idan aka ci mutuncina, abin da ya daure kai shi ne babu wani babba a industiri da ya ce wa Rahama kanzil sakamakon abin da ta yi mini, wannan abin ya harzuka shi ya ga tun da ba a yi magana ba, to ubangidansa ya zama mutumin banza ke nan, hakan ya sa ya yi magana a kan batun.”
Jarumin ya karyata batun ya cire jarumar a fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta’ ne don ta ki amince wa tayin soyayyar da ya yi mata, inda ya ce jarumar ta kitsa karya don neman wata biyan bukata ta kashin kanta.
Ba zan ce komai kan batun da ya shafe ni da Zango a kasuwa ba- Ali Nuhu
Sai dai bayan Aminiya ta tuntubi jarumi Ali Nuhu ko akwai wani martanin da zai mayar sai dangane da abubuwan da Zango ya yi ikrari sai ya ce ba zai ce komai kan batun abin da ya shafe shi da Zango a kasuwa ba.
Ya ce: “Batun abin da ya shafe ni da Zango ba zan rika yin sa a kasuwa ba. Bai kamata mu rika yada maganganu a waje ba. Idan su Zango sun shiga kafafen yada labarai sun yi maganganu, to ni ba zan iya haka ba. Don haka Bashir mu bar wannan magana.”
Ba Ali Nuhu ne ya sa na yi wa Adam Zango tatas ba- Rahama Sadau
Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa bacin rai da biye wa zuciya ne suka sanya ta yi wa Adam Zango tatas a shafinta na Istagram ba wai kamar yadda ake yada wa cewa Ali Nuhu ya sa ta ba.
Ta ce: “Na kadu sosai da na ji ana cewa wai Ali Nuhu ne ya sa na aikata abin da na yi wa Adam Zango, wannan ba gaskiya ba ne. Kuskure dai na aikata, shi ya sa ma daga baya na koma na ba shi hakuri, wanda kuma Ali Nuhu ne ya sanya na yi hakan, amma abin mamaki sai a rika cewa shi ne ya sanya na aikata hakan.”
Ta bayyana ta yi nadamarta kan abin da ya faru har dangantaka tsakanin Ali da Zango ta sukurkuce.
Dangantaka tsakanin jaruman ta dade da yin tsami
Wata majiya da ke kusa da Ali Nuhu da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana dangataka tsakanin jaruman ta dade da yin tsami, inda Ali Nuhu ya ki cewa komai ne saboda zurfin ciki da kuma iliminsa.
“Na tabbata Ali Nuhu ya ki cewa komai ne saboda zurfin ciki da kuma iliminsa, amma na tabbata shi ma ya yanke alaka tsakaninsa da Adam Zango din. Sau da yawa Ali kan kira Zango a waya amma ya ki dauka, yakan yawaita korafi a kan hakan. Akwai lokacin da bayan ya kira shi ya ki dauka ne sai ya kira Falalu dorayi shi kuma ya kira Zango, inda nan take ya dauka, a nan ma yaransa sun yi ta shiga da fice wajen bayyana masa cewa shi sarki ne, kuma zaki ne dole a bi shi. Zango ya yanke hukunci ba tare da ya yi tunani ba, sannan yaran da suke gindinsa ma sun taka muhimmiyar rawa wajen zuga shi har ya yanke alaka tsakaninsa da Ali.” Inji majiyar.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa