Yadda Dangote ya tuka mota babu jami’an tsaro don yin ta’aziyya
Attajiri mafi kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya tuka motarsa da kansa inda ya je gaisuwar ta’aziyya ba tare da rakiyar jami’in tsaro ba. Wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan zumunta wanda shugaban kamfanin jaridar Ovation, Cif ya Dele Momodu ya sanya a shafinsa, ya nuna yadda Alhaji Dangote ya tuko […]
Attajiri mafi kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote ya tuka motarsa da kansa inda ya je gaisuwar ta’aziyya ba tare da rakiyar jami’in tsaro ba.
Wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan zumunta wanda shugaban kamfanin jaridar Ovation, Cif ya Dele Momodu ya sanya a shafinsa, ya nuna yadda Alhaji Dangote ya tuko kansa a mota shi kadai da rana, domin ta’aziyyar rusuwar tsohuwar Sarauniyar Kyau, Ibidun Ighodalo.
Bidiyon ya nuno Dangote da kansa yana faka motar da ya tuko ya bude kofa zai sauko bayan isarsa gidan Shugaban Cocin Tiriniti da ke Ikoyi a Legas, Fasto Itua Ighodalo, wanda shi ne mijin mai rasuwar, domin yi masa ta’aziyya.
- An binne sarauniyar kyau Ighodalo
- Tsohuwar Sarauniyar Kyau ta rasu
- Matatar Dangote za ta samar da rarar Dala biliyan 2.5 a fannin takin zamani
Mutanen da suka tari attajirin sun cika da mamakin ganin Dangote ya fito daga motar ba tare da direba ko dogarin da ke tsaron lafiyarsa ba.
Dangote ya yi basaja har ya isa gidan gaisuwan shi kadai a motarsa kirar G-Wagon mai ruwan toka.
A ganinku me ya sa Dangote fita ba tare da jami’an tsaro ba?
Dangote drove himself to Pastor Ituah's residence pic.twitter.com/sDYISP3Mgi
— #Dangbele (@MellodiOfficial) June 16, 2020