Yadda ‘dattawa’ ke goya wa matasa baya suna ta’asa a Jos
Wasu dattawa a Jos ke zuwa suna karbo ’yan daba da jami’an tsaro suka kama
Jama’a na zargin wadansu dattawa da daure wa ’yan Sara-Sukar gindi a garin Jos na Jihar Filato inda suke zuwa suna amso ’yan Sara-Sukar daga hannun hukuma a duk lokacin da saka kama su.
Hakan na faruwa ne yayin da matasan ke addabar mutanen birnin, tare da jefa rayukansu a mawuyacin hali ta hanyar tsare mutane suna raunata su da yi musu kwacen wayoyi da sauransu.
- 2023: Jonathan na nan daram a PDP —Saraki
- Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa zamanin mulkin Jonathan ya shiga APC
Hakan ya sa ala tilas mutanen birnin Jos suka samar da kungiyoyin ’yan sintiri don su taimaka wajen tabbatar tsaro tare da kama wadanda ake zargi da aikata ta’asa suna mika su ga ’yan sanda.
Sai dai yadda wasa dattawan ke zuwa suna karbo bata-garin daga hannun hukuma ya dade yana mayar da hannun agogo baya tare da ci wa mutanen garin da a baya ya fice wurin zaman lafiya tuwo a kwarya.
Sun fara kai hari ga ’yan sintiri
Aminiya ta samu labarin cewa hakan ya karfafa wa ’yan Sara-Sukar gwiwa inda suka fara kai hari kan ’yan sitirin suna illata su don huce fushi.
Kwamandan Kungiyar ’Yan sintiri ta Neighborhood reshen Nasarawa, Jos Alhaji Aminu Musa na daya daga cikin wadanda matasan suka illata.
Ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar 26 ga Disamban 2020, an samu hargitsi a tsakanin ’yan Sara-Sukar da sojoji a Filin Bal, inda DPO din Nasarawa ya kira shi, kan su tura ’yan sintiri wurin.
Ya ce sun isa da misalin karfe 6:45 na safe, kuma bayan ’yan sanda sun tafi, wadansu daga cikin yaran sama da 50 da suka buya suka kawo musu hari da adduna da barandami alhali ba su fi mutum shida ba.
Ya ce tilas ’yan bangar suka gudu, “Nan suka same ni, suka sassare ni, aka kai ni Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), inda na yi mako biyu ina jinya kafin in dawo gida, in ci gaba da jinyar.
“Mutane da dama sun dauka ba zan rayu ba, saboda raunukan da suka yi min,” inji shi.
Alhaji Aminu ya ce ba wannan ne na farko ba, sun sha fuskantar irin wadannan hare-hare daga matasan.
Ya ce akwai wani dan kungiyarsu, mai suna Mamman da tsagerun yaran suka kashe a shekarar 2018.
“A lokacin a Unguwar Dutse-Uku, wadannan matasa sun yi yunkurin kashe wani dan banga, wajen daba masa wuka sai suka daba wa dan uwansu.
“Amma sai suka juya magana suka ce, ’yan banga ne suka kashe dan Sara-Sukar.
“Suka zo suka kona ofishinmu na ’Yan Shanu, suka zo gidana suka rushe gabansa; Suka je Filin Bal suka kona mana ofishi, sannan suka tafi babban ofishinmu na Majema suka kakkarya kujerun wurin,” inji shi.
Shugaban ya ce iyaye da dama ba sa taimaka musu wajen gyaran tarbiyyar yaran, inda banda wasu ma da tsine musu suna ce musu yaran Fir’auna.
Sai ya yi kira ga iyaye su hada kai a gyara yaran, idan ba haka ba za su iya hana mutane zama a gidajensu.
Wani dan Sintiri na Neighborhood da ke Unguwar Rikkos, mai suna Mustapha Muhammad da ’yan Sara-Sukar suka karya wa hannu lokacin da suka je unguwar yin abin da suke kira ‘Shara,’ ya ce mako uku da suka gabata a an gaya musu cewa ’yan daba za su zo ‘Shara’ a unguwarsu.
Ya ce a tsakanin Magariba da Isha’i aka kira shi, cewa ga yaran sun shigo unguwar, inda suka gaggauta zuwa suka iske yaran sun fi 100 dauke da adduna.
“Sai yaran suka juya, ashe sun rabu uku ne, wadansu suka bullo ta wani gefe, mu uku da aka ware don tsare wata hanya, sai suka sanya mu a tsakiya.
“Sai muka ji suna cewa a kashe mu, suna kawo mana sara da adduna da sanduna, garin tarewa ne hannuna ya karye.
“Biyu daga cikinmu da suka iya sanda ne suka kora su, aka dauke ni zuwa asibiti,” inji shi.
Ya ce idan ’Yan Shara suka zo unguwa ko dabba ba sa bari, haka idan suka samu shago sukan wawushe kayansa su tafi.
Suna kwace wayoyin mutanen da suka samu, idan mutum bai gudu ba kuma su daba masa wuka ko adda.
Laifin iyaye ne –COJOYA
Shugaban Kungiyar Matasa ta Bunkasa Jos da Kewaye (COJOYA), Barista Buhari Ibrahim Na-Shehu, ya shaida wa Aminiya cewa abin da ke faruwar, yawancin iyaye ne suka yi sakaci da tarbiyyar ’ya’yansu.
Ya ce akwai bukatar gwamnati da al’ummar gari su hada kai don ceto yaran.
“Harkar Sara-Suka harka ce mai muni da matasa da dattawa da hukuma da kowa zai kawo gudunmawa don magance ta a nan Jos.
“A matsayinmu na matasa idan ana son magance matsalar, muna bayar da shawarar a canja tunanin matasan ta hanyar zama da su a wayar musu da kai kan illolin abubuwan da suke yi,” inji shi.
Matsalar ta addabi jama’a –Lauya
Wani lauya mai zaman kansa, kuma daya da cikin shugabannin al’ummar Jos, Barista Muhammad Lawal Ishak, ya ce matsalar Sara-Suka a Jos, matsala ce da ta addabi jama’a, wadda ta faro lokacin rikice-rikicen kabilanci da addini a shekarun baya.
Ya ce rikice-rikicen sun sanya matasa da dama sun dauki ta’asa ko rashin bin doka a matsayin daidai.
Ya ce a lokacin Gwamnatin Jang, akwai rashin fahimta tsakaninta da al’ummar Jos, wannan ya sa duk wani abu da gwamnatin ta yi, ana yi masa kallon don a kuntata wa al’ummar Jos ne. Don haka abin ya zamo ba a son bin doka da oda.
“Misali lokacin da Gwamnatin Jang ta hana acaba da dama al’ummar Jos ba su yarda da dokar ba.
“Saboda ana ganin kamar an fito da ita ce don a hana matasanmu sana’ar da suke samun abinci,” inji shi.
Barista Lawal Ishak ya ce a lokacin an samu sabani a tsakanin ’yan sanda da matasa har ta kai ga aka harbe wadansu matasa.
“Hakan ya kai ga dan sanda bai isa ya sanya kaki ya yi yawo a unguwanninmu ba.
“Wannan ya sa ’yan sanda jin tsoron shigowa cikin gari su yi aiki. Hakan ne ya kara wa matasan karfin gwiwar yin abin da suka ga dama,” inji shi.
Ya ce yanzu abin ya yi muni, ya kai a wasu unguwanni idan dare ya yi babu wanda zai iya shiga, domin matasan suna tare mutane su kwace musu wayoyi, wadansu na kai wa junansu hari.
Barista Ishak ya ce sun dauki matakan dakile matsalar ta hanyar amfani da kungiyoyi a unguwanni inda suke wayar da kan matasan illar abin da suke yi.
Kuma suna taimakawa wajen sama wa matasan ayyukan yi da samar musu gurbin karatu a makarantu.
Sai ya yi kira ga gwamnati ta samar wa matasa ayyukan yi don magance wadannan matsaloli.
Kuma masu hali su ba da gudunmawa ta hanyar kafa kananan masana’antu da za su rika daukar matasan a aiki.
‘Yawanci su suke haddasa rikicin addini’
Babban Shugaban Kungiyar ’Yan sintiri ta Neighborhood a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, kuma Kwamadanta a Mazabar Ibrahim Katsina, Malam Nasiru Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa sun fara gudanar da ayyukansu ne lokacin da rikice-rikicen addini da kabilanci suka ki ci, suka ki cinyewa a Jos.
Ya ce sun gano bata-gari masu aikata miyagun ayyukan ne suke jawo rikice-rikicen.
“Wadannan batagari, suna hada baki a tsakanin Musulmi da Kirista, inda wanda ke bangaren Musulmi, zai dauki hayar mai babur ya gaya masa wata unguwa da Kirista suka fi rinjaye, idan ya je sai su hadu da abokansa Kiristoci a buge shi su dauke babur din.
“Ko sace-sace ne za ka ga tare suke yi. Idan suka aikata laifi a bangaren Musulmi, sai su koma bangaren Kiristoci su buya, idan kuma suka aikata laifi a bangaren Kiristoci sai su taho bangaren Musulmi su buya a wajen abokansu. Abubuwn da suka yi ta faruwa ke nan kafin a gane su.”
Ya ce da suka hadu Musulmi da Kiristoci a shekarar 2011, suka fara gudanar da aiki karkashin kungiyar sai aka fara samun saukin lamarin.
Kwamandan ya ce matsalolin da suka fi fuskanta su ne ba a taimaka musu, domin komai na ayyukansu su suke yi da kudinsu.
“Mutane a unguwa suna kwance a gidajensu, babu wanda ke taimakawa. Haka babu wani taimako da gwamnati ke ba mu.
“Sannan iyaye ba sa son a fadi laifin ’ya’yansu, akwai yara da dama da mun kai su wajen ’yan sanda, bayan sun yi laifi, kafin mu dawo gida sun riga mu dawowa.
“Wadannan yara sun fi amfani da lokutan Maulidi da Takutaha da Karamar Sallah wajen aika-aika.
“Suna zuwa wajen da makamai da kayan shaye-shaye, kafin ka ce haka sun fara fada a tsakanin unguwa da unguwa har abin ya shafi wanda bai ji ba, bai gani ba,” inji shi.
Daya daga cikin dattawan Jos, kuma Shugaban Kamfanin Kega Motors, Alhaji Yahaya Muhammd Kega, ya ce abubuwan da suke sa yaran aikata ta’asar su ne shaye-shaye da rashin karatu da sakacin iyaye.
“Ya kamata kowace unguwa a ce suna da dattawa masu kula da abubuwan da ke faruwa.
“A unguwarmu mu mun ja kunnen masu sayar da kwayoyi kan su bar wannan kasuwanci.
“Kuma muna kula da su, duk wanda muka kama dole ya bar mana unguwa.
“Mun kori irin wadannan mutane da yawa, yanzu mun samu saukin matsalar,” inji shi.
Abin da ya sa muke Sara-Suka
Wadansu daga cikin ’yan Sara-Sukar da wakilinmu ya zanta da su, sun ce rashin tallafi daga gwamnati da sauran al’umma ke sa su haka, sun ce an bar su suna zaman banza, babu sana’a babu karatu.
“Wadansunmu iyayensu sun rasu lokacin rikice-rikicen baya.
“Mun taso marayu, babu masu kula da mu, babu wanda zai taimaka mu yi karatu ko sana’a, saboda haka ba yadda muka iya, sai dai mu shiga shaye-shaye, don mu manta da damuwar da muke ciki,” inji su.
Abin ya gagare mu –Iyaye
Iyayen yara da dama da wakilinmu ya tuntuba kan zargin daure wa ’ya’yansu gindi suna ta’asa, sun musanta hakan.
Sun ce suna iyakar kokarinsu kan lamarin, amma abin ya gagare su, don haka ya kamata hukuma, ta yi abin da ya kamata.
Shugaban Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce suna kama ragamar mulki suka zauna suka dubi me ya kamata su yi kan wannan matsala.
“Sai muka fito da wani salo na dakile matsalar, inda muka tattaro yaran muka zauna da su.
“A zaman sun ce babu wata gwamnati da taba zaunawa da su ta ji koke-kokensu, don haka sun ji dadin hakan kuma sun yi alkawarin ba za su sake wannan abu ba,” inji shi.
Alhaji Shehu Bala ya ce sakamakon zaman sun dakile kashi 85 cikin 100 na matsalar.
Don haka batun Sara-Suka a Jos a yanzu sai dai jefi-jefi, sabanin baya da ake samun matsalar a kowace unguwa.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa garin Jos fadar Jihar Filato, gari ne da ya yi suna wajen zaman lafiya inda mutane suke zuwa yawon bude ido daga ko’ina a duniya.
Amma a shekarar 2001, sai garin ya fara fuskantar rikice-rikicen addini da kabilanci da suka yi sanadin asarar dubban rayuka da dukiyoyi na biliyoyin Naira.
Bayyanar Sara-Suka a Jos
Wadannan rikice-rikice sun jawo dubban matasa sun kasa ci gaba da karatu tare da rasa aikin yi, kuma hakan ya jawo suka fantsama ga aikata miyagun ayyuka.
Rikice-rikicen sun jawo rarraba wuraren zama a tsakanin Musulmi da Kirista, wanda hakan ya tado da wata sabuwar kura inda a wasu unguwannin Jos, jami’an tsaro ba su iya shiga don tabbatar da doka da oda, ko kama wadanda ake zargi da karya doka.