Yadda dattijo mara lafiya, mai shekara 85 ya kada kuri’a
Wani dattijo mai shekara 85 da ke kwance a wani asibiti ya yi zaben Shugaban kasar makon jiya bayan tilasta wa wadanda ke jinyarsa su taimaka masa yin hakan. Dattijon mai suna Dokta Adebisi Sebanjo ya kada kuri’arsa ne a wata mazaba da ke unguwar Apapa da ke Jihar Legas. Likitan wanda shi ne Daraktan […]
Wani dattijo mai shekara 85 da ke kwance a wani asibiti ya yi zaben Shugaban kasar makon jiya bayan tilasta wa wadanda ke jinyarsa su taimaka masa yin hakan.
Dattijon mai suna Dokta Adebisi Sebanjo ya kada kuri’arsa ne a wata mazaba da ke unguwar Apapa da ke Jihar Legas. Likitan wanda shi ne Daraktan Asibitin Julisam Hospital, ya samu taimakon wasu ma’aikatan jinya biyu mata wadanda suka tallafa masa zuwa rumfar zaben.
A lokacin da aka nemi ganawa da shi, wadanda suka rako shi sun bayyana cewa ba shi da karfin yin magana.
Dokta Adebisi mahaifi ne ga Babban Mai bai wa Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola Shawara kan Magance Talauci, Idowu Sebanjo.