Yadda dillalai ke zagon ƙasa ga shirin tallafin kayan noma

An kama shugaban kungiyar manoma kan zargin badaƙalar kayan nona da gwamnatin ta samar wa manoma a farashi mai rahusa a Jihar Jigawa

Yadda dillalai ke zagon ƙasa ga shirin tallafin kayan noma

Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa Reshen Karamar Hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa ta shiga hannu, kan badaƙalar kayan noman da Gwamnatin Tarayya ta ba wa manoma a farashi mai rahusa.

An kama shi ne tare da wasu dillalai da jami’an gwamnati a ƙananan hukumomin Kiyawa da Kafin Hausa, kan zargin karkatar da kayan noman da gwamnati ta zaftare rabin farashinsa ga manoma.

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Mahadi, ya bayyana takaici kan yadda ’yan kasuwa ke haɗa baki da jami’an gwamnati wajen karkatar da kayan zuwa kasuwa da kuma tsawwala wa manoma farashi.

Da yake bayyana cewa za su fuskanci fushin doka ya bayyana takaici bisa yadda almundahanar ta dabaibaye shirin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa noma da tallafa wa manoma da kayan noma a jihar.

A yayin da gwamnan yake rangadi a cibiyoyin rabon kayan noma a jihar ne ya bankaɗo yadda dillalai da jim’an gwmanati suke zagon ƙasa ga shirin.

Gwamnan ya ce, “Dillalai na zagon ƙasa ga wannan shiri, wanda hakan ke kawo wa manoma matsala wajen ci gaba da noma su. Ba za mu lamunci hakan ba,” in ji gwamnan.

Ya bayyana cewa “gwmanati ta sanya N159,187 a matsayin kuɗin kayan noman, wanda ta rage rabin kuɗinsa ga manoma

“Amma mun samu bayanai cewa ’yan kasuwa na ƙara musu N5,000 zuwa N10,000, wanda ƙarin nauyi ne ga manoma.

“Wannan zagon ƙasa ne ga ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa harkar noma da manoma. Don haka za mu tabbatar an ƙwato duk haramtattun kuɗaɗen da aka karɓa a hannun manoma, a mayar musu,” a cewar Gwamna Namadi.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja