Yadda direbobin tasi suke harkokinsu a Kamaru

Manyan birane a kasar Kamaru kamar Yaounde da Douala na fama da karancin wuraren daukar fasinjoji motocin tasi. Bisa ka’ida dai motocin tasi da suke aikin jigilar jama’a daga wannan unguwar zuwa wancan mutane hudu ne yakamata su dauka bayan shi matukin motar. Sai dai kuma abin da yake faruwa shi ne maimakon a dauki […]

Yadda direbobin tasi suke harkokinsu a Kamaru
Yadda direbobin tasi suke harkokinsu a Kamaru

Manyan birane a kasar Kamaru kamar Yaounde da Douala na fama da karancin wuraren daukar fasinjoji motocin tasi.
Bisa ka’ida dai motocin tasi da suke aikin jigilar jama’a daga wannan unguwar zuwa wancan mutane hudu ne yakamata su dauka bayan shi matukin motar.
Sai dai kuma abin da yake faruwa shi ne maimakon a dauki fasinja guda a gabar mota, guda biyu ake dauka ba tare da la’akarin kauri, ko sirintakar mutum ba.
Kodayake, direbobin sun saba da haka, su ma fasinjojin a wani lokaci kamar da safe lokacin tafiya wurin aiki ko kuma makaranta, hakan ma da yamma lokacin fitowa makaranta da tashi daga aiki, su da kansu  sukan bukaci a yi hakan domin su samu isa inda da suka nufa cikin lokaci.
Wannan ya samo asali ne daga halayyar wasu fasinjoji ta rashin son biyar kudin mota kamar yadda ka’ida ta shumfida. A yanzu haka dai,  tafiya mai nisan kilomita 11 daga inda mutum ya shiga tasi zai biya CFA 250 kwatankwacin Naira 83 zuwa 85.
Kodayake, idan fasinja ya ga cewa yana hanzari, zai iya kara wa direban kudi domin ya dauke shi. Hakan zai iya kaiwa CFA 300 zuwa 500 wato Naira 100 zuwa 165. Idan kuma “Drop” ko shata ne kudin CFA 1,500 ne wato Naira 500 zuwa sama bisa ga yarjejeniyar da bangarorin biyu za su yi tare da yin la’akari da nisar tafiyar da kyawun hanyar da kuma ko yawan kayan da tasi din za ta dauka. Sai dai kuma abin da yake faruwa shi ne da farko akasarin mutane na lura har idan inda za su tafi yana kusa ne suna yi wa direban tasi tayin CFA 100 kwatankwacin Naira 33 zuwa 35.
Shi kuma direba daga na shi bangaren har idan kuma ya ga cewa zai kona manshi tare da ya samu riba komai kankantarta, yana amincewa ya dauki fasinja da ya yi mishi wannan tayi.
Yadda kuma tsari yake a nan Kamaru babu tashoshi na tsayiwar su motoci masu yawo a cikin gari. Zagaya wa kawai suke yi suna neman fasinjoji.